Da wuya a samu maganin cutar kansa a nan kusa – Bincike

Asalin hoton, FRANCIS CRICK INSTITUTE
Wani gagarumin nazari da aka gudanar ya nuna yadda kusan daga yanzu, har abada, cutar kansa za ta ci gaba da rikiɗa domin ci gaba da ɓarna a jikin ɗan adam, in ji masana kimiyya.
Sakamakon nazarin da aka gudanar ta hanyar bibiyar cutukan kansa na tsawon shekara tara, ya bai wa masu bincike mamaki da tsoro kan irin jan aikin da ke gabansu.
A ƙarshe sun yi ittifakin cewa kamata ya yi a mayar da hankali kan hanyoyin kare kai daga cutyar, ganin cewa da wuya a iya samo maganin cutar a nan kusa.
Cibiyar Bincike kan cutar kansa da ke Birtaniya ta ce gano cutar da wuri na da matuƙar muhimmanci.
Nazarin ya samar da bayani mafi zurfi game da yadda kansa ta samo asali da kuma abin da ke haifar da ita.
Cutar kansa takan rikiɗe a tsawon lokaci – saboda tana da siffofi da dama.
Ƙwayoyin cutar kan sauya su munana, ta yadda za su iya bijire wa garkuwar jiki kuma su yaɗu a sassan jiki.
Tsiron kansa kan fara ne daga ƙwayar halitta ɗaya wanda ya lalace, wanda daga baya yakan ƙunshi miliyoyin ƙwayoyin halitta da suke rikiɗewa.













