Yadda mutum zai tsira daga tunanin kashe kansa
A hankali ana samun ƙaruwar mutanen da ke kashe kansu a Najeriya, musamman ma matasa.
Babban Bankin Duniya a 2019 ya ce yawan masu kashe kansu ya ƙaru da kashi 3.5 cikin 100 a ƙasar.
A shekarar 2021 kawai, an samu mutum 50 da suka kashe kansu.
Wasu ƙwararrun ma na cewa ba a faye samun labaran da yawan mutanen da ke kashe kansu ba.
BBC Hausa ta tuntuɓi Dr Dayyaba Shu’aibu, wata likitar lafiyar ƙwaƙwalwa da ta yi bayani kan yadda za a gane idan mutum yana tunanin kashe kansa, da matakan da za a bi a dakatar da hakan.







