Gwagwarmayar da Somalia take don fatattakar mayakan al-Shabab

A wani naɗi da ta yi, sabuwar gwamnatin Somalia ta naɗa tsohon ɗan ƙungiyar al-Shabab, wanda ya taɓa faɗa da hukumomi, a matsayin ɗaya daga cikin majalisar ministocin ƙasar amma mummunan harin da aka kai kan wani otal tunatarwa ce kan gagarumin aikin da ke gaban wadanda ke kan mulki.

Lokacin da sabon Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya karɓi mulki a watan Mayu, ya bayyana muhimmin abin da zai kawo ƙarshen ta'addancin da aka shafe shekara 15 ana yi.

Watanni uku bayan nan, al-Shabab ta kai wani hari kan otal da ke kusa da fadar shugaban ƙasa a Mogadishu, babban birnin ƙasar.

Sun yi wa wajen ƙawanya tsawon sa'a 30. Jami'ai sun ce fiye da mutum 20 ne suka mutu a harinda aka kai Hayat, wasu 117 kuma suka jikkata.

Ƙasa da wata ɗaya kafin nan ne ƙungiyar ta kutsa Ethiopia. Ya yi kamar ƴan ƙungiyar ba sa martaba sabon shugaban.

Jami'an diflomasiyya na ƙasashen waje sun ce an shafe watanni 18 ana tsara harin da ya hada da mayaƙa 1,200.

Kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Amurka da Afirka a lokacin, Janar Stephen Townsend, ya ce mayaƙan sun nausa cikin Ethiopia - taku 150.

Wani dalili da yasa kungiyar ta zafafa kai hare-hare shi ne saboda karuwar rikice-rikice a Habasha bayan wasu shekaru na zaman lafiya da ci gaba.

Jim kadan bayan barkewar yaƙin basasa a yankin Tigray da ke arewacin Ethiopia a watan Nuwamban 2020, wani mamban al-Shabab ya yi mani kira.

"Mun ajiye maƙaman mu, muna kuma kallon yadda Habasha ke wargaza kanta da kanta,'' in ji mamban na al-Shabab. ''Lokacin cin galaba a kan abokan gabanmu ya kusa zuwa.''

Habasha na ɗaya daga cikin ƙasashe a yankin da ta tura dakaru zuwa Somaliya don marawa gwamnati baya.

Wannan shi ne karo na biyu da shugaba Mohamud yake kan mulki.

Lokacin da na tattauna da shi jim kadan bayan fara wa'adin mulkinsa na farko a 2012, ya ce zai ci galabar mayakan cikin shekara biyu.

Sai dai, shekara goma bayan nan, mayakan na ci gaba da kara karfi.

Shugaban wata hukumar gudanar da bincike da kuma samar da tsaro a Mogadishu mai suna Hiraal Security think-tank, Mohamed Mubarak, ya ce ''mayakan na al-Shabab na da karfi da kuma manyan makamai masu sarrafa kansu ba kamar yadda aka sansu a 2012 ba''.

Al-Shabab dai ta kafa wata gwamnati tasu ta daban, inda kuma suke iko da manyan yankuna.

Kungiyar na sakawa mutane da ke yankunan da take iko biyan kudin haraji.

Yawancin mazauna Mogadishu, sun fi son amfani da tsarin shari'a na al-Shabab, wadda suke ganin yafi musu saboda babu zargin rashawa kamar yadda yake a wajen kotunan Habasha.

Kungiyar na ci gaba da kai hare-hare a lokacin da take so, inda take harba makamai kan majalisar ƙasar da kuma zuwa cikin filin jirgin saman kasa da kasa inda ofisoshin jakadanci da na Majalisar Dinkin Duniya da kuma dakarun kasar waje suke.

Hare-haren da al-Shabab ke kai wa zuwa manyan wurare ne ma yasa ake kwatanta ta da kungiyar al-Qaeda.

Shugaba Mohamud ya bayyana cewa ba za a iya cin galabar al-Shabab ta hanyar karfin soji kaɗai ba.

A ranar 2 ga watan Augusta, gwamnatin kasar ta dauki aniyar kawo ɗaya daga ciki tsoffin abokan gabarta a matsayin wani sabon yunkuri na kawo karshen rikicin.

Ina Mogadishu a lokacin, cikin mota da wasu abokanai makale cikin cunkoson ababen hawa.

Babu wanda ya damu ko kadan kan fitar da mu daga motar da binciken mutane da ababen hawa da kuma jakukkuna.

Lokacin da muka tsaya jira a kusa da wani inuwar da muka samu, mun shiga wani irin yanayi, idanuwan mu sun koma kan wayoyin mu, inda muke kallon jawabin mai magana da yawun firaminista kan naɗa sabuwar majalisar ministoci.

Sunan da muke jiran mu ji shi ne na wani mamban al-Shabab wanda ke cikin wadanda suka kafa kungiyar da kuma ya samu horo a Afghanistan.

Jijitar ta koma ta gaskiya.

An sanar da sunan tsohon mataimaki kuma mai magana da yawun ƙungiyar al-Shabab, Mukhtar Robow a cikin sabuwar majalisar ta ministoci, inda aka naɗa shi ministan harkokin addini.

Yayin da wasu suka firgita da matakin, amma yawancin 'yan Somaliya sun yi na'am da shigar gwamnati na mutumin da ya kasance yana cikin jerin 'yan ta'adda da Amurka ke nema ruwa a jallo da tayin bada tukwuicin dala miliyan 5 ga duk wanda ya kamo shi.

Sun hada da ɗan majalisar dokoki da kuma tsohon wakilin BBC, Moalimuu, wanda ake son kamawa saboda kai hare-hare biyar da al-Shabab ta yi.

Wani harin kunar bakin-wake a farkon shekarar nan, ya sanya shi neman tsira da rayuwar shi.

"Ina farin cikin naɗin mista Robow," a cewar mista Mohamed.

"A matsayinsa na tsohon shugaban kungiyar masu ikirarin jihadi , zai taimaka wajen yaƙi da al-Shabab.

Zai yi aiki da al'ummomin addini don kalubalantar ayyukan masu tsatsaurar ra'ayi wajen ganin an janyo hankalin mayaƙan cewa hanyar da suka bi ba tafarkin addinin Islama ba ce.

"Mista Robow ya rabu da kungiyar al-Shabab a 2013.

Ya fito bainar jama'a ya kalubalanci kungiyar, inda har ma ta kai ya bayar da taimakon jini ga mutanen da wai harin bam ya rutsa da su a Mogadishu a watan Oktoban 2017, wanda kuma ya hallaka mutum kusan 600.

An tsare shi a watan Disamban 2018 da kuma ajiye shi a wani gida har sai bayan da aka sanar da sunansa cikin sabuwar majalisar ministoci. Ya ce ya samu kirar waya lokacin da yake tsare.

Wani masanin harkar tsaro, mista Mubarak, ya kwatanta naɗin mista Robow da cewa hakan ''tunani ne mai kyau ta ɓangaren yaƙi da ta'addanci''.

''Yana da karfin gaske, musamman ta fuskar aƙida, saboda zai bayar da gagarumin gudummawa wajen yaƙi da al-Shabab.

A matsayinsa na wanda suka kafa kungiyar al-Shabab, ya san ciki da wajen kungiyar. Ya kuma san yadda suke tunani da kai hare-hare.''

Wasu sun mayar da martani mara kyau ga naɗin mista Robow cikin gwamnati, inda suke ganin naɗin a matsayin alama ce ta rashin hukunta masu laifi da suka janyo faɗa ta gwamman shekaru a Somaliya.

Kafafen sada zumunta sun cika da suka kan naɗin.

Yawancin tsokaci da ake kan shafin Twitter ya kasance mai zafi: ''Idan Somaliya wajen aiki ne na al'umma, da an hukunta mista Robow a gaban jama'a.''

''Naɗin wannan makashi na nufin abu ɗaya cewa: al-Shabab ta gama kutsawa cikin gwamnatin Somaliya.''

Al-Shabab ta yi imanin cewa amincewa da tsohon shugabanta a cikin gwamnati babban laifi ne, wanda ya cancanci hukunci.

A cikin wani sakon murya na minti 10, mai magana da yawun al-Shabab, Ali Dheere, ya ce ''Robow mai ridda ne, wanda kuma jininsa ya halasta.''

Shugaba Mohamud ya yi imanin cewa naɗin mista Robow harda da sabon shirin soji, zai iya karya lagon al-Shabab wajen sanya ta shiga tattaunawar sulhu.

''Hakan duka ya dogara ne ga bukatar siyasa,'' a cewar mista Mubarak.''

''Karshen al-Shabab zai zo ne idan kungiyar tarayyar Afirka ta AU da sauran dakarun ƙasashen waje da na yankuna da dukka mayaƙa suka haɗa kai wajen aiki tare.

Idan ba haka aka yi ba, kungiyar ba za ta shiga tattaunawar sulhu ba.''

Mista Robow da ya kasance mayaƙi kafin a naɗa shi muƙamin minista, a yanzu yana maganar samun zaman lafiya da kuma afuwa.

Ya ce zai yi aiki da malaman addinin Islama don janyo hankalin mutane domin barin al-shabab ta hanyar sanar da su cewa addinin musulunci bai yadda da abin da kungiyar ke yi ba.

Sai dai, ba a san ko kasadar da gwamnatin ta ɗauka ko kwalliya za ta biya kuɗin sabulu ba, ko kuma hakan zai karawa al-Shabab karfi wajen kara kai hare-haren da ba su saba kai wa ba.