Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama mutumin da ya kara motarsa a ƙofar shiga hanyar Fadar Gwamnatin Birtaniya
Rundunar ƴan sanda a Birtaniya ta cafke wani mutum bayan da wata mota ta bugi ƙofar shiga hanyar Fadar Gwamnatin Birtaniya - Downing Street.
Rundunar ta ce an kama shi ne saboda zargin yin ɓarna da kuma tuƙin ganganci.
Zuwa yanzu dai babu rahoto kan wani da ya jikkata kuma ana ci gaba da bincike, in ji ƴan sanda.
Tuni dai ƴan sanda suka rufe Whitehall - babbar hanyar da ke bi ta Downing Street.
Lamarin ya faru ne da ƙarfe 4:20 na yammacin Alhamis, kamar yadda ƴan sanda suka ce.
Ana iya ganin motar mai launin azurfa a wajen baƙaƙen ƙofofin ƙarfen ta wurin hanyar shiga Fadar inda Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak da iyalinsa ke zaune.
Firaminista Sunak yana cikin Fadar ta Downing Street a lokacin da lamarin ya faru.