FA Cup: Abin da ya kamata ku sani kan wasan Brighton da United

Brighton da Manchester United za su kece raini a karawar daf da karshe a FA Cup ranar Lahadi a Wembley.

United ta kawo wannan matakin bayan da ta ci Fulham a zagayen quarter finals ranar 19 ga watan Maris, yayin da Brighton ta ci Grimsby Town 5-0 a ranar.

United mai FA Cup 12 an fitar da ita daga Europa League ranar Alhamis, bayan da Sevilla ta doke ta 3-0, jimilla 5-2 gida da waje da suka kara.

Brighton na fatan kai wa wasan karshe a FA Cup a karon farko tun bayan 1983 - wadda ta yi rashin nasara a hannun United.

Ita dai Brighton na taka rawar gani a bana, wadda take ta takwas a teburin Premier League, mai kwantan wasa, wadda ke fatan samun gurbin buga gasar zakarun Turai a badi.

A cikin watan Agusta farko-farkon fara Premier League, Brighton ta doke United 2-1 a Old Trafford.

Pascal Gross ne ya fara cin kwallo a minti na 30, sannan ya kara na biyu minti tara tsakani, United ta zare daya bayan da Alexis Mac Allister ya ci gida.

De Zerbi, ya tsinci dami a kala a matakin kociyan Brighton, bayan da ya maye gurbin Graham Potter, wanda Chelsea ta dauka daga baya ta sallame shi.

United ta kwan da sanin dadin daukar kofi musamman a Wembley, wadda a cikin watan Fabrairu ta lasshe Carabao Cup, bayan doke Newcastle United.

United wadda ta yi ban kwana da Europa League za ta yi kokarin lashe kofi na biyu a bana wato FA Cup da kammala Premier cikin 'yan hudun farko - hakan gagarumar ci gaba aka samu a kungiyar a kakar nan.

Bayan da United ta kwaso kwallo 7-0 a Liverpool ranar 5 ga watan Maris, kungiyar Old Traffod ta ci Real Betis a Europa da doke Brentford 1-0 a Premier.

Koda yake United ta yi rashin nasara a hannun Newcastle United a St James Park a Premier League, wadanda suka tashi a karawar farko 0-0 a Old Trafford.

Karin labarai kan Brighton da Manchester United

'Yan wasan Brighton da ke jinya sun hada da mai tsaron baya Joel Veltman da mai buga bangaren gaba, Evan Ferguson.

Marcus Rashford zai iya buga wa United fafatawar, wanda ya shiga wasa canji a karawa da Sevilla a Europa League a Sifaniya.

Bruno Fernandes zai iya buga wasan, wanda ya yi hutun hukuncin dakatarwa.