Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Telegram: 'Dandalin da miyagu ke yadda suka ga dama'
- Marubuci, Joe Tidy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan intanet
- Lokacin karatu: Minti 6
Kimanin wata tara da suka gabata a lokacin da nake wani bincike, kwatsam sai na tsinci kaina a wani zauren dandalin Telegram mai mambobi da yawa wanda ake fataucin miyagun ƙwayoyi.
Sai kuma aka saka ni a wani zauren da ke koyar da kutse da kuma wanda yake mayar da hankali kan hanyoyin satar katin banki.
Daga baya ne na fahimci ashe yanayin tsarin da nake ciki na Telegram ɗina ne ya ba da damar a riƙa saka ni a cikin zaurukan ba tare da na sani ba. Amma duk da haka sai na bar tsarin a haka domin ganin abubuwan da suke faruwa.
A cikin wasu ƴan watanni, sai da na tsinci kaina a cikin zauruka 82 daban-daban.
Daga baya sai na canja tsarin domin hana shigar da ni zaurukan, amma har yanzu kullum ina shiga Telegram ɗin, nakan samu dubban saƙonni daga gomman zauruka na miyagun ayyuka.
Kama shugaban Telegram da aka yi a Faransa ya haifar da muhawara a kan tsarin kula da bayanan masu amfani da dandalin.
An tuhumi Pavel Durov da zargin bayar da dama ana gudanar da miyagun ayyuka a a dandalin, ciki har da fataucin miyagun ƙwayoyi da zamba da yaɗa hotunan batsa domin dandalin ya samu ƙarbuwa.
Babu shakka ana gudanar da wasu ayyukan na assha a wasu kafofin na sadarwa, amma binciken da na yi na gane wa idona abubuwan da jami'an tsaro suka daɗe suna bayyanawa a shekaru da dama.
Ga wasu abubuwa da na gano a cikin zaurukan da aka saka ni a ciki.
Duka hotunan nan a cikin zaurukan aka saka su, amma mun canja sunan zaurukan domin gudun tallata su.
Wannan ne ya sa na daina mamakin ba yadda masanin kimiyyar kariyar intanet Patrick Gray ya daɗe yana bayyana Telegram a matsayin "dandalin da masu miyagun harƙalla ke yadda suka so."
Da yake bayyana kamen Mista Durov, Mista Gray ya bayyana a shirinsa na rediyon intanet wato podcast mai suna Risky Business cewa dandalin Telagram ya daɗe da zama dandali da masu aikata miyagun ayyuka ke yadda suka so.
"Muna magana ne a kan cin zarafin yara da safarar miyagun ƙwayoyi da wasu miyagun ayyuka da ba a yin komai a kai," in ji shi.
Masu aikata miyagun ayyuka suna son amfani da irin wannan dandalin ne saboda ɓoye bayanansu, kasancewar gano wanda yake amfani da wani suna ko shafi na da wahalar gaske.
Masu bincike a kamfanin tsaron intanet na Intel471 ya ce, "kafin zuwan Telegram, ana gudanar da irin waɗannan harƙallar ne a intanet da aka tsara da wasu ɓoyayyun bayanai," amma ga masu son aikata miyagun ayyuka ƙanana waɗanda ba su da ƙwarewa sosai, "Telegram ya zama waje mafi sauƙi a gare su."
Masu kuste na Qilin, waɗanda suka yi wa asibitocin NHS kutse a farkon wannan bazarar, sun yaɗa sakamakon gwajin jinin mutane da suka sace a zaurensu na Telegram kafin daga bisani suka saka kafarsu ta intanet da ke ɓoye bayanan masu amfani da ita.
Wasu daga cikin zaurukan dandalin Telegram da ake gudanar da miyagun ayyuka da aka saka ni akwai su a Snapchat sannan kuma za a iya samun dilolin ƙwayoyi a Instagram ma.
Amma dilolin ƙwayoyi na tallata shafukansu na Telegram a waɗancan manhajoji domin jan mutane zuwa zaurukansu.
A watan Janairu, ƴansandan jihar Latvia sun kafa sashe na musamman domin bibiyar manhajojin da suke tallata ƙwayoyi, sannan jami'an sun bayyana sunan Telegram a rahotonsu.
Yaɗa hotunan batsa na ƙananan yara
Mahukunta Telegram sun ce dandalin na "tsarin gudanar da dandalin ya yi daidai da ake tafiyar da tsare-tsaren gudanar da ɓangaren kafofin sadarwa," amma ko a makon nan mun ga wasu abubuwa da suka nuna akasin haka.
A ranar Laraba, BBC ta gano cewa dandalin Telegram ba ya amsa buƙatun ƴansanda na sauke wasu abubuwa da ba su dace ba.
Rashin yin abin da ya dace wajen kiyaye yaɗa hotunan cin zarafin ƙananan yara na cikin tuhumar da Faransa ta gabatar a kan mai dandalin.
"Daga cikin tuhumar da ake masa akwai rashin tsarin samar da daidaito da bayar da haɗin kai musamman wajen yaƙi da cin zarafin ƙananan yara," in ji Jean-Michel Bernigaud, Sakatare Janar na hukumar kare haƙƙin yara ta Faransa.
Mahukunta dandalin na Talegram sun bayyana wa BBC cewa suna bibiyar ayyuka marasa kyau, ciki har cin zarafin ƙananan yara a dandalin. Sannan sun ce ko a watan Agusta kaɗai sun ɗauki mataki a kan wasu zauruka guda 45,000 da ba su bayyana sunansu ba.
Rashin ba ƴansanda haɗin kai
Samar da daidaito ba shi kaɗai ba ne matsalar dandalin. Yadda dandalin ke kunnen uwar shegu ga buƙatar ƴansanda na cire wasu abubuwa da ba su dace ba, tare da miƙa bayanan masu aikata laifin na cikin sukar da ake musu.
Brian Fishman, ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa manhajar Cinder ya ce, "Dandalin Telegram ya kasance wani maɓoyar ƴan isis na gomman shekaru. Dandalin na bayar da damar yaɗa hotuna da bidiyon cin zarafin yara, sannan sun ƙi yin komai a kan buƙatar jami'an tsaro na dakatar da aikata irin waɗannan abubuwa na tsawon lokaci."
Telegram na ba da dama ga masu amfani da dandalin su shiga tsarin "Secret Chat" wato zantawa ta sirri wanda ko masu Telegram ɗin ba za su iya ganin me ake tattunawa ba.
Amma sai mutum ya shiga tsarin da kansa ne zai iya amfani da shi, sannan kuma yawancin waɗannan ayyukan da ake magana a kai - ciki har da zaurukan fataucin miyagun ƙwayoyi da aka saka ni a ciki - ba za a iya shigar da shi tsarin sirri ba saboda dukkan zauruka babu damar shigar da su tsarin zantawar sirri.
Wannan na nufin dandalin Telegram zai iya tantacewa tare da miƙa dukkan bayanan da ƴansanda ke buƙata, amma ba sa yi.
"Dukkan tattaunawa da ake yi a dandalin Telegram ko a zauruka mallakin waɗanda suke yi ne, ba za mu amince da buƙatar miƙa su ga kowa ba," kamar yadda yake a rubuce a dokokin manhajar.
A watan Yuni, Pavel Durov ya bayyana wa ɗanjarida Tucker Carlson cewa ya ɗauki "injiyoyi kusan 30" domin kula da manhajar.
Ƴancin faɗin albarkacin baki
Duk da irin sukar da dandalin Telegram ke sha, wasu na ganin akwai matsala a kamen da aka yi wa Mista Durov.
Ƙungiyar kare haƙƙin amfani da intanet ta Access Now ta ce tana bibiyar abin da ke wakana.
A wata sanarwa, ƙungiyar ta ce ta daɗe tana sukar dandalin Telegram ɗin ita ma.
Sai dai ta ce "tsare ma'aikacin wani dandalin da mutane suke amfani da shi wajen cika ƴancin da suke da shi na faɗin albarkacin bakinsu ba tare da tauye haƙƙin wasu ba, zai iya zama an wuce makaɗi da rawa wajen tantancewa, sannan zai tauye haƙƙin wasu."
Elon Musk, mai manhajar X ya soki kama Mista Durov, sannan ya bayyana hakan ya danna ƴancin mutane na faɗin albarkacin bakinsu, sannan ya yi kira da a gaggauta sakin mai manhajar ta Telegram.