Wace rawa jakadun Najeriya a ƙasashen waje za su iya takawa?

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Tun bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar tura dakarunsa zuwa Najeriya domin yaƙar ƴa'ta'adda da ya ce suna kashe Kiristoci, ƙwararru ke ta nanata muhimmancin naɗa jakadun Najeriya a ƙasashen waje.

Fiye da shekaru biyu kenan, Najeriya ba ta da jekadu a ƙasashen ƙetare, wani abin da masana ke ganin ya mayar da ƙasar baya ta fuskar hulɗarta da ƙasashen wajen.

Tun watan Satumban 2023 Najeriya ta kira jekadunta daga ƙasashe da dama, bayan rantsar da shugaba Bola Ahmed a watan Mayu, kuma har yanzu gwamnatinsa ba ta naɗa sabbi ba.

Sai dai kuma a watan Afrilun 2024 gwamnatin Tinubu ta naɗa wasu jami'an diflomasiyya 12 a ƙasashe 14 waɗanda ake kira "chargés d'affaires".

Masana na cewa jakadu a ƙasashen waje na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen daƙile zargin kisan Kiristanci tun kafin al'amarin ya kai ga yadda yake a yanzu.

Illar rashin jakadan Najeriya a Amurka

Masana harkokin diflomasiyya sun ce rashin jakadan Najeriya a Amurka na ɗaya daga cikin dalilan da suka haifar ƙarfafar zargin yi wa Kiristoci "kisan gilla".

Dakta Muhammad Haroon, masanin alaƙar ƙasa da ƙasa da diflomasiyya kuma malami a kwalejin fasaha da ke Kaduna ya ce da a ce akwai jakadan Najeriya a Amurka to da al'amuran ba su zama haka ba.

"Ita farfaganda wato tallata manufa wani abu ne mai muhimmancin gaske. Ka ga amma tun da babu jakada, to ta yaya za a san me ƙasarka take yi."

Rawar da Jakadu ke takawa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jakada, mukami ne mai muhimmaci a ƙasa domin wakili ne kan duk abin da ya shafi lamurran ƙasar a wata ƙasa, domin yana magana ne da yawun ƙasar da yake wakilta da kuma shugaban ƙasa.

Jakada kan taka muhimmiyar rawa musamman wajen janyo ra'ayin masu zuba jari tare da bayar da shawarwari kan fannonin da za su amfani ƙasa.

Sannan jakada ido ne na ƙasa wanda ke kare manufofi da buƙatunta a ƙasashen ƙetare tare da zama babban jigo ga sauran hulɗoɗin ƙasa da sauran hukumomi na duniya.

Rashin jakada, zai sa ƙasa ta rasa dukkanin waɗannan damarmakin tare da kuma rage ƙimarta da tasirinta a harakokin duniya.

Sai dai ba a san yadda ƙasashen duniya suke kallon Najeriya ba, kasancewar ta shafe fiye da shekaru babu jekadunta a ƙasashen na ƙetare, musamman ƙasar da ke dogaro da masu zuba jari na ƙasashen waje da kuma tallafi.

Tsohon jakadan Najeriya Ambasada Suleiman Dahiru, wanda ya yi aiki a ƙasashe da dama ya ce rashin jakadun, babban giɓi ne ga ƙasar musamman ga hulɗoɗinta a ƙasashen ƙetare.

"Ba zaɓi ba ne kuma bai dace ba a ce Najeriya ba ta da jakadu a ƙasashen waje. jami'an diflomasiyya da ta tura ba su da ƙarfin da za su yi gogayya da gwamnatoci, musamman shugabannin ƙasashe," in ji shi.

Me ya janyo tsaikon naɗa jakadun Najeriya?

Daga cikin dalilan da gwamnati ta bayar na rashin naɗa jakadun Najeriyar a ƙasashen wajen sun haɗa da rashin kuɗi a lalitar gwamnati da ƙasar ta ce tana fama da shi, kamar yadda wata majiya daga ma'aikatar kasashen waje ta Najeriya ta shaida wa BBC.

Sai dai ambasada Dahiru ya ce batun rashin kuɗi ba dalili ba ne na rashin naɗa jakadun, la'akari da irin kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa a wasu hidimominta.

Toshon jakadan na Najeriya a Sudan ta Kudu ya alaƙanta tsaikon da yadda aka siyasantar da al'amuran ƙasa.

''Ina ganin abin da ke kawo jinkirin a ganina an sanya siyasa, saboda ana debo 'yan siyasa a cusa a aikin diflomasiya alhalin ba su da kwarewa a wannan fannin, dan haka gwamnati ta yi kokarin ganin Najeriya ta samu wakilci a kasashen da ba ta da jakadu.''

Sai dai bayanai da rahotanni da ke fitowa daga fadar shugaban Najeriyar na nuna cewa a yanzu shugaban ƙasar yana ta ƙoƙarin haɗa sunayen mutanen da za a aika a matsayin jakadun ƙasar a ƙasashen wajen.