Yaushe Tinubu zai nada jakadun Najeriya a kasashen waje?

Shugaba Tinubu

Asalin hoton, @PBATMediaCentre

Lokacin karatu: Minti 4

Yadda Najeriya ta shafe watanni ba ta da jakadu a ƙasashen waje ya fara jan hankalin ƴan kasar har ma da masana diflomasiyya.

Fiye da shekara kenan, Najeriya ba ta da jekadu a ƙasashen ƙetare, wani abin da masana ke ganin ya mayar da ƙasar baya ta fuskar hulɗarta da ƙasashen waje.

Tun Satumban bara Najeriya ta kira jekadunta daga ƙasashe da dama, bayan rantsar da shugaba Bola Ahmed a watan Mayu, kuma har yanzu gwamnatinsa ba ta naɗa sabbi ba.

Duk da cewa gwamnatin Najeriya ba ta bayyana dalilin tsaikun nada sabbin jakadun ba amma a baya gwamnatin ta danganta lamarin da rashin isassun kuɗi.

A watan Afrilu gwamnatin Tinubu ta naɗa wasu jami'an diflomasiyya 12 a ƙasashe 14 waɗanda ake kira "chargés d’affaires"

Aikinsu ya ƙunshi gudanarwa da tafiyar da harakokin ofisoshin jakadancin Najeriya, amma kuma ba su da ƙarfin iko ta yin hulɗa ta ƙasashen waje kamar jakada.

Babu tabbas ko an yi tanadin kan sabbin jakadun na Najeriya a ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi.

Masu sharhi da masana diflomasiyya na ganin rashin jakadun a ƙasashen waje zai yi wa Najeriya illa a ɓangarori da dama.

Wannan dai ba sabon abu ba ne a gwamnatin APC, domin ko zamanin gwamnatin Buhari an shafe watanni kafin naɗa jakadun ƙasashen waje.

Me masana ke cewa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tsohon jakadan Najeriya Ambasada Suleiman Dahiru, wanda ya yi aiki a ƙasashe da dama ya ce rashin jakadun, babban giɓi ne ga ƙasar musamman ga hulɗoɗinta a ƙasashen ƙetare.

"Ba zaɓi ba ne kuma bai dace ba a ce Najeriya ba ta da jakadu a ƙasashen waje. jami'an diflomasiyya da ta tura ba su da ƙarfin da za su yi gogayya da gwamnatoci, musamman shugabannin ƙasashe," in ji shi.

Akwai fannoni da dama kamar ɓangaren cinikayya da buƙatu na tsaro da Najeriya ke tattaunawa da ƙasashen waje, kuma rashin wakili zai iya kawo tarnaƙi ga samun nasarar abin da ƙasar ke buƙata.

Gwamnati ta sanya hannu kan yarjeniyoyi a ƙasashen waje, kuma wasu na ganin akwai bukatar wakilan Najeriya a ƙasashe da za su bibiya domin tabbatar da nasararsu.

Ambasada Dahiru na ganin kasancewar gwamnatin Najeriya ta siyasa ce ba ta soja ba, bai kamata a ce an shafe wannan tsawon lokacin ƙasar ba ta da jakadu a ƙasashen waje ba.

Masanin diflomasiyar na ganin ya kamata gwamnati ta yi la’akari da yadda wasu ƙasashe ke gaggauta turo jekadansu a Najeriya da zarar sun sauya wani.

“Yana da wahala ka ga an yi mako ɗaya ko biyu, ba a turo sabon jakada ba bayan sauya tsoho,”

"Amma yanzu a ce a Najeriya an shafe fiye da shekara babu jakadu, kamar ta toshe wasu hanyoyi ne na hulɗa tsakaninta da ƴan ƙasashen ƙetare."

Amasada Dahiru ya bayar da misali da gwamnatin soji ta marigayi Sani Abacha da ta ƙi naɗa jakadun ƙasashen waje saboda faɗan da take yi da su musamman ƙasashen yammaci.

“Bai kamata kuma wannan gwamnatin da take ta siyasa ba a ce ba ta da jakadu a ƙasashen waje.”

"A matsayina wanda ya yi aikin diflomasiyya na shekaru da dama ban ji dadin a ce Najeriya ba ta da jekadu ba a ƙasashen waje.

Amasaba ya ce batun rashin kudi ba dalili ba ne na rashin nada jakadun, la’akari da irin kudaden da gwamnati ke kashewa a wasu hidimominta

“Ni yadda na sani, da zarar an cire jakada nan-take ake nada wani. A ce an shafe shekara guda wannan ba daidai ba ne” in ji shi.

Masanin ya ce kuskure ne a ce, wasu ƙasashe sun turo da jakadunsu a Najeriya amma kuma ƙasar ba ta da nata wakili a nasu ƙasashen.

Wannan babbar illa ce ga jami’an diflomasiyya, saboda wasunsu sun kusan yin ritaya, kuma akwai tsarin cewa duk wanda shekara ɗaya ta rage masa ya yi ritaya, ba za a naɗa shi ambasada ba.

Muhimmancin jakadun kasashen waje

Jakada, mukami ne mai muhimmaci a ƙasa domin wakili ne kan duk abin da ya shafi lamurran ƙasar a wata ƙasa, domin yana magana ne da yawun ƙasar da yake wakilta da kuma shugaban ƙasa.

Jakada kan taka muhimmiyar rawa musamman wajen janyo ra’ayin masu zuba jari tare da bayar da shawarwari kan fannonin da za su amfani ƙasa.

Sannan jakada ido ne na ƙasa wanda ke kare manufofi da buƙatunta a ƙasashen ƙetare tare da zama babban jigo ga sauran hulɗoɗin ƙasa da sauran hukumomi na duniya.

Rashin jakada, zai sa ƙasa ta rasa dukkanin waɗannan damarmakin tare da kuma rage ƙimarta da tasirinta a harakokin duniya.

Sai dai ba a san yadda ƙasashen duniya suke kallon Najeriya ba, kasancewar ta shafe fiye da shekara babu jekadunta a ƙasashen na ƙetare, musamman ƙasar da ke dogaro da masu zuba jari na ƙasashen waje da kuma tallafi.