Me ya sa wasu ke yin kiraye-kirayen sauke karamin ministan tsaron Najeriya?

Lokacin karatu: Minti 3

A Najeriya, jama'a na ci gaba da bayyana damuwa game da yawaitar zargin da ake yi wa karamin ministan tsaro na kasar, Bello Matawalle, cewa yana da alaka mai karfi da 'yan bindiga, kuma yana taimaka masu.

Har ma ana ta yi masa matsin lamba a kan ya sauka daga mukaminsa, a gudanar da cikakken bincike kansa don ya wanke kansa.

Sakamakon haka ma wasu lauyoyi masu zaman kansu sun bayyana aniyar shigar da kara kotu, game da zarge-zargen da ake yi wa karamin ministan.

Sai dai ministan ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, da cewa siyasa ce wadda ba yau aka fara ba.

Yanzu haka dai matsin lamba na dada kamari a kan lallai ilalla sai karamin ministan tsaron ya sauka daga mukaminsa, kuma a gudanar da bincike kansa, dangane da zargin da ake ta yi cewa yana da alaka da 'yan bindigan.

Kuma wannan matsin lamba ya kara jawo hankalin jama'a ne, bayan da Musa Muhammad Kamarawa, wani tsohon mataimaki na musamman ga ministan a lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara, ya fitar da wani hoton bidiyo a 'yan kwanakin nan, yana jaddada zarge-zargen da ake yi wa ministan, kan samar da kudi ga 'yan bindiga, da sayo masu motoci da gidaje, da dabbobi da dai sauransu.

Sakamakon haka ne ma wasu lauyoyi masu zaman kansu, su ma suka nemi karamin mnistan ya sauka daga kujerar tasa ko su gurfanar da shi gaban kuliya, a cewar ja-goransu, Barista Hamza Nuhu Dantani a tattaunawarsa da BBC:

''Ya kamata ya yi murabus jami'an tsaro masu nagarta su yi bincike a kansa, kuma idan hakan bai samu ba gaskiya za mu maka shi a kotu.''

Sai dai kuma Ibrahim Dosara, tsohon kwamishinan yada labarai a lokacin da karamin ministan yake gwamnan jihar Zamfara, a martanin da ya mayar a tattaunawa da BBC ya ce wannan zargi ba sabon abu ba ne:

''Magana guda ce dai ake ta yi tun lokacin da yana gwamna lokacin da ya yi sulhu domin irin halin da jihar Zamfara ta shiga ciki. A wannan lokacin ya shiga nemo hanyar da za a bi domin a daina kashe mutane a jihar Zamfara. Kuma aka yi ta fito masa da hanyoyi kala-kala da zagon-kasa.''

Dangane da tarin zarge-zargen Dosara ya kara da cewa: ''Zargi ne na kanzon-kurege wanda ba shi da tushe balle makama.''

Ya kara da cewa magana ce kawai ta siyasa a game da zaben 2027: '' Suna jin tsoron cewa lalle idan yana kan wannan kujera to zai bincike su kuma za su gurfana gaban kuliya a hukunta su,''

Dangane da kiran da ake masa ya sauka daga mukamin a yi bincike kuwa sai tsohon kwamishinan yada labaran na Zamfara ya ce: ''Shi Matawalle ba shi ya nada kansa ba, saboda haka maganar cewar ya sauka a yi bincike ba ta ma taso ba.

Yanzu dai hankalin jama'a ya koma ne ga kallon yadda wannan dakasarama za ta kaya.