Shin matakan CBN kan hauhawar farashi a Najeriya sun yi tasiri?

Asalin hoton, @cenbank
Bisa al'ada ma'aikatu kan yi bitar shekara mai ƙarewa tare da bayyana nasarori da ƙalubalen da aka fuskanta a shekarar tare da kuma bayyana fatan sabuwar shekara da abubuwan da suke son cimmawa.
Kuma kamar sauran hukumomi, Babban Bankin Najeriya CBN yana da irin wannan tsari na yin bitar ayyukansa na shekara da kuma tanadin da aka yi wa sabuwar shekara.
A 2023 CBN ƙarƙashin jagorancin gwamnan bankin Olayemi Cardoso ya bayyana abubuwan da yake son cimmawa a 2024.
Ɗaya daga cikin abubuwan da ya bayyana wa kwamitin kula da bankuna da cibiyoyin kudi da kuma inshora na majalisar dattijan Najeriya shi ne zai yi ƙaƙarin rage hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya zuwa ƙasa da kashi 20% daga yadda yake.
A wancan lokacin Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya NBS ta ce " hauhawar farashin kayayyaki a watan Disambar 2023 ta kai 28.93 daga 28.20 a watan Nuwambar 2023.
"Hauhawar farashin kayan abinci ta kai 33.93 a watan Disamba daga kashi 32.84 a watan Nuwambar 2023," kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na X.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
NBS na fitar da ƙididdiga irin wannan a kowanne wata domin bayyanawa 'yan ƙasa da duniya halin da ake ciki na ci gaba ko akasinsa a ƙasar.
A watan Oktoban da ya gabata, NBS ta ce "hauhawar farashi ta ƙaru zuwa kashi 33.88 daga 32.70 a watan Satumban 2024. Hakan na nufin an samu ƙaruwar hauhawar farashin da kashi 2.64 a Oktoba.
"Hauhawar farashin abinci ta ƙaru da kashi 39.16 a bayaninsu na shekara-shekara" in ji NBS.
Wannan na nuni ƙarara cewa CBN bai cimma burinsa ba na rage hauhawar farashin kayayyaki ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Masana na cewa a yanzu ne ya kamata abubuwa su yi sauki musamman saboda lokacin kakar kayan amfanin gona ake.
Sun ce ya kamata abinci ya sauko amma hakan bai samu ba.
Me majalisa ta ce wa CBN

Asalin hoton, CBN
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A tsari na mulki dole ne CBN a duk ƙarshen shekara ya shaidawa majalisar dattijai alkiblarsa da muradunsa da abubuwan da yake son cimmawa a kowacce shekara.
A gabansu ya yi alƙawura na 2023 waɗanda bai cimma ba, kuma a wannan watan na Disamba zai je ya bayar da bahasin yadda ayyukansa na 2024 suka gudana.
Ƴan majalisar sun ce gwamnan Babban Bankin Olayemi Cardoso ya yi bayanan duk abubuwan da suka cimma, sannan aka buɗe fagen tambayoyi game da yadda shekarar ta gudana.
"A halin da ake ciki yanzu a Najeriya ana fama da ƙaracin garin kuɗaɗe a hannun mutane wani abu da ke ƙara ta'azzara wahalhalun da ake ciki.
"Yan sauran kuɗin da suke yawo a hannun al'umma a fatattake suke," in ji Sanata Babangida Husaini.
Sanatan ya tambayi Cardoso me ya kawo wannan matsala.
"Ya yi mana bayani amma duk matakan da ake ɗauka ba su kai ga nasarar da ake so ba" in ji Sanatan
Sanatan ya ce sun mayar da Gwamnan ya koma ya sake nazari kan manufofinsu na kuɗi domin ba su yi aiki ba.
Ya ce sun ba shi shawarwari da watakila idan ya yi aiki da su a samu sassauci a gaba.
Sanatan ya ce ya yi wa Cardoso bayani irin wuyar da mutane ke ciki ta rashin kuɗaɗe a hannunsu.
"Na ba shi misali da kasuwar Maigatari inda a jihata ne, mutane na fuskantar ciniki kashi biyu, na ɗaya idan kana da garin kuɗi za ka iya samun sauki, sannan wanda zai tura ta intanet farashinsa daban.
"Wannan bai kamata a ce yana faruwa ba a Najeriya," kamar yadda Sanata Babangida Hussaini ya shaida wa BBC
Cardoso cikin bayaninsa ya ce "mun kawo tsari na hukunta duk wani bankin kasuwanci da yake ɓoye garin kuɗaɗen da yake da su amma baya bayarwa".
Sanatan ya ce kai tsaye sun fito sun shaida wa Cardoso "ba mu gamsu da matakan naku ba, idan kuna yi ne domin rage yawan kudin da ke yawo a hannun mutane ku fito fili ku yi wa al'umma bayani".
Samar da tallafi ga manoma
Gwamnan Babban Bankin cikin tambayoyin da ya amsa har da wadda aka yi masa game da rage yawan kuɗin ruwan da bankuna ke karba wanda CBN da kansa kuɗin ruwansa na farawa ne daga kashi 24 zuwa 26.
Wannan ya kai ga tattaunawa kan buƙatar dawo da tsare-tsaren taimakawa manoma da masu ƙananan sana'o'i da bankin ya ke yi a baya.
Cardoso bai boye matsayar bankin ba kan wannan lamari inda ya ce "mun soke waɗannan tsare-tsare ne saboda matsalolin da aka fuskanta cikinsu,".
Sai dai Sanatocin sun ce masa babu yadda za a yi ƙanana da matsagaitan sana'o'i su ci gaba matuƙar ba sa samun tallafi irin na baya.
"Idan an samu matsaloli a baya hakan ba ya nufin a daina shirin baki ɗaya, sai a duba inda aka samu matsala a ɗauki matakan gyara.
"Akwai bankin manoma da na kasuwanci da suke bayar da bashi cikin kuɗin ruwa mai sauki da bai wuce kashi 7, 8 zuwa 9, wanda hakan zai taimakawa manoma" in ji Sanata Babangida Husaini.
Cardoso ya amince da cewa za su je su sake bibiyar manufofin da suka gabatar a 2024 waɗanda a cewar Majalisar Dattijan Najeriya ba su yi wa 'yan ƙasar ba tasiri ba.











