Ƙungiyar JNIM na barazanar durƙusar da Mali, ina Nijar da Burkina Faso?

Shugaban mulkin soja na ƙasar Mali Assimi Goita

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban mulkin soja na ƙasar Mali Assimi Goita
    • Marubuci, Isidore Kouwonou
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
    • Aiko rahoto daga, Dakar
  • Lokacin karatu: Minti 8

Ƙaracin man fetur na ƙara tsananta a Bamako da kewaye.

Masu lura da lamurran yau da kullum na ƙara nuna damuwa kan hare-haren da Jama'at Nusrat al-Islam wal Muslimin (JNIM), mai alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda, ƙarƙashin jagorancin Iya Ag Ghaly ke kai wa a kusa da babban birnin na ƙasar Mali.

Sace wasu ƴan kasuwa ƴan asalin ƙasar Masar a birnin Bamako, da kai hari kan ayarin tankokin dakon man fetur a wurin mai nisan kilomita 50 daga garin Kati, kusa da babban birnin ƙasar na daga cikin ta'asa ta baya-bayan nan da ke tayar da hankalin ƙasar a kwanakin nan.

Amurka ta sanar cewa "Artabun da ake yi tsakanin gwamnatin Mali da ƴan ta'adda na ƙara ƙamarin rashin tabbas a cikin ƙasar," inda Amurkar ta buƙaci ƴan ƙasarta da ke Mali "su fice daga ƙasar nan take."

Wannan ne karon farko da Amurka ta bayar da irin wannan gagaɗi bayan da masu ikirarin jihadi ke toshe hanyoyin shigar da man fetur, lamarin da ya durkusar da ayyukan tattalin arziƙi da jefa rayuwar yau da kullum ta al'umma cikin garari a tsawon fiye da mako biyu.

Wannan lamari ya tursasa wa gwamnati rufe makarantu, manya da ƙanana.

Gidan mai da cunkoson mutane a Mali.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Al'ummar Mali na fama da matsanancin ƙarancin man fetur, wani abu da ke ƙara taɓarɓarar da yanayin tattalin arziƙi da na tsaro a ƙasar

Ministan Ilimi na Mali, Dr Amadou Sy Savane ya ce toshe hanyoyin shigar da man fetur zuwa yankunan ƙasar da ƙungiyar JNIM ta yi ya kawo cikas ga zirga-zirgar malamai da ɗalibai a ƙasar.

Al'umma na shan ukuba sanadiyyar ƙarancin man fetur da kuma matsin da hakan ke haifarwa ga tattalin arziƙi da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar, musamman a Bamako da garuruwan da ke makwaftaka waɗanda mayaƙan JNIM ke ƙoƙarin katsewa daga sauran yankuna.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da alama mazauna birnin Bamako ba sa hangen ƙarshen lamarin a nan kusa. A ƙarshen makon da ya gabata, wakilin BBC ya ga yadda ake samun dogayen layuka a sauran gidajen mai ƴan ƙalilan da suka rage suna sayar da man fetur ɗin. Wasu sun kwashe kwana da kwanaki a kan layi domin samun man fetur da bai taka kara ya karya ba.

"Al'amarin ya buwaye mu baki ɗaya," in ji wani mazaunin birnin Bamako. Ya bayyana cewa ya jingine babur ɗinsa fiye da tsawon mako ɗaya kuma a saboda haka hanyar kuɗaɗen shigarsa ta rufe ruf.

"A jiya ne kawai wani ya taimaka min da rabin galan din fetur, da shi na yi amfani na yi wasu ƴan abubuwa."

Wani matuƙin mota ya bayyana yanda ya kwashe sama da kwana ɗaya a kan layin mai, inda aka sayar masa da ɗan abin da bai taka kara ya karya ba. "Muna shan wahala wajen tafiyar da rayuwarmu. Abin ya tsananta. Dole sai ka kwashe kwana uku kana bin layi kafin ka samu man fetur lita biyu, idan kuma ya ƙare haka za ka dawo ka kwashe wasu kwanakin a kan layi."

"Kamfanoni da dama sun buƙaci ma'aikatansu su zauna gida saboda ƙarancin man fetur," kamar yadda wani mutumin ya shaida mana, ya ce waɗanda suka yi dace su ne waɗanda aka ce su yi aiki a gida. "Wasu da dama ba su samu wannan gatan ba."

Herve Wendyam Lankounde, mai sharhi kuma masani a Cibiyar bincike kan zaman lafiya da tsaro da ci gaba a Afirka da ke da mazauni a ƙasar Netherlands, ya ce ƙungiyar JNIM ta "yanke shawarar kai farmaki kan hanyar samun kudin shiga na al'ummar ƙasar Mali ne domin da zaran aka samu ƙarancin man fetur, farashin komai zai tashi.

"An kai hari ne kan hanyar samun kuɗin shiga ta al'umma a fakaice. Kuma hakan ya taɓa ƙarfin gwamnati."

Vue aérienne de la ville de Bamako

Asalin hoton, Reuters

Ko ficewar MINUSMA da dakarun Faransa ya taimaka?

Des soldats maliens montrent le drapeau du groupe djihadiste, JNIM après l'attaque de Radisson Blu à Bamako.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dr. Seidik Abba ya bayyana cewa dakarun ƙasashe ƙeatre na a Mali a shekarar 2015 amma duk da haka ba su iya dakatar da masu iƙirarin jihadi daga kai hari a Mali ba

Mutane da dama sun yi fargabar cewa lamarin tsaro zai iya taɓarɓarewa a Mali, da ma sauran ƙasashen ƙawancen yankin Sahel (AES) bayan ficewar dakarun ƙasashen ƙetare, musamman sojojin Faransa da rundunar Barkhane da Minusma da kuma sauran dakarun ƙasashen Turai.

Wasu masharhanta na da amannar cewa wannan na faruwa ne sanadiyyar taɓarɓarewar tsaro, wanda ya haifar da sake farfaɗowar ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da kuma sake dawowar faɗace-faɗace tsakanin ƙabilu.

Hervé Wendyam Louankande na da yaƙinin cewa ya zuwa wani lokaci ƙungiyar tsaro ta Wagner ce ta cike giɓin da aka samu bayan tafiyar dakarun ƙasashen waje, ko da kuwa ba ta da isassun jami'a kamar rundunar Barkhane ko MINUSMA.

Ficewar dakarun ƙasashen waje ta ƙara ƙarfafa wa masu ikirarin jihadi gwiwa.

"Ina ganin masu iƙirarin jihadi sun lura da cewa waɗanda ke taimaka wa gwamnati wajen yaki da su sun tafi, saboda haka yanzu faɗan ya rage ne tsakaninsu da gwamnati.

"Wannan ya ba su damar ƙaddamar da hare-hare tare da samun sukuni," in ji masanin.

Ya ƙara da cewa hakan ya sa ƙungiyar JNIM ta faɗaɗa hare-harenta, inda ta samar da wasu gungu-gungu na masu kai farmaki waɗanda ke tafiya daga wani wuri zuwa wani a fadin ƙasar ta Mali.

Ƙungiyar na son ta murƙushe sabon salon yaƙi da jirage marasa matuƙa da Mali ke aiwatarwa tare da hadin gwiwar Burkina Faso da Nijar da kuma sabbin ƙawayensu.

"Akwai masanan da ke kwatanta abin da ke faruwa a Mali da wanda ke faruwa a Afghanistan ko wasu ƙasashen da masu ikirarin jihadi ke ayyukansu. Ina ganin cewa a yanzu JNIM na iko da wasu ƙauyuka. Amma tambayar ita ce ko suna da ƙarfin da za su ƙwace iko da Bamako? Ba na tunanin hakan."

A nasa ɓangaren, Dr Seidik Abba ba ya ganin cewa masu jihadin, musamman ma JNIM sun farfaɗo ne sanadiyyar ficewar dakarun ƙasashen ƙetare.

Ya ce akwai wasu abubuwa da ke faruwa a cikin ƙasar waɗanda ke taimaka wa ƙungiyar JNIM wajen ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare.

"Abin shi ne mun kasa sauya dabarunmu. Tun kafin zuwan sojoji da bayan zuwan su, duk abin da muka dogara da shi shi ne amfani da ƙarfin soja wajen yaƙi da matsalar tsaro a Mali."

Ya bayyana cewa rashin aikin yi tsakanin matasa da rashin daidaito a tsakanin al'umma da kuma rashin kasancewar gwamnati a wasu yankunan ƙasar sun kasance abubuwan da masu iƙirarin jihadi ke cin gajiyarsu wajen ƙara ƙarfi.

"Saboda rashin magance waɗannan matsaloli ne ya sanya muka tsinci kanmu a wani yanayi da ya sanya JNIM take ƙara ƙarfi. Saboda ta samu damar ɗaukar matasa wadanda ke fama da matsin rayuwa."

Shugaban na Cibiyar nazari kan tsaro a yankin Sahel ya jaddada cewa idan ba a sauya salo ba ta hanyar nemo ƙwararan hanyoyi baya ga amfani da ƙarfin soji, to kuwa ƙungiyar JINIM za ta ci gaba da faɗaɗa ayyukanta.

Duk da cewa ya jaddada buƙatar ganin ba a watsar da batun ƙarfafa ɓangaren soji ba, Dr Abba ya bayyana cewa magance matsalolin al'umma na da matukar muhimmanci, kuma hakan zai iya zama tushen samo masalaha game da matsalar tsaro da ake fuskanta a yankin Sahel.

"Ko da mun dawo da dakarun ƙasashen waje, idan ba mu sauya salo ba, ba za mu fita daga wannan matsala ba," in ji shi. Inda ya bayyana cewa hatta lokacin da dakarun ƙasashen waje suke nan ba su hana hare-hare da faɗaɗar ayyukan masu iƙirarin jihadi ba, musamman a yankin tsakiyar ƙasar Mali.

Jarrabawa ga ƙungiyar AES?

Des militants de l'AES brandissent des pancartes, l'une soutenant l'alliance du sahel, l'autre accusant la CEDEAO.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

Masanin ya jaddada cewa abin da ke faruwa a Mali tamkar wata jarrabawa ce ga ƙawancen ƙasashen Sahel (AES) domin gwada ƙarfin haɗin kan da ke tsakaninsu.

Ƙungiyar, wadda ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar, wadanda dukkaninsu ke ƙarkashin mulkin sojoji, kuma wadanda suka fice daga ECOWAS, wajibi ne su nuna cewa ƙungiyar tana da tasiri.

To amma a halin yanzu babu wani tasirin ƙungiyar da aka gani bayan irin hare-haren da ƙungiyar JNIM ke kai wa a ƙasar ta Mali, lamarin da ya kawo ruɗani sosai a ƙasar.

A baya-bayan nan ne ƙungiyar ta sanar da ƙirƙirar dakarun haɗin gwiwa mai sojoji 5,000 domin yaƙi da ayyukan ƙungiyoyin masu ɗaukar makami da kuma ƙarfafa tsaron ƙasashen.

Dakarun sun ƙunshi sojoji daga ƙasashen Mali da Nijar da Burkin Faso, wadanda za su yi aiki ta ƙasa da ta sama, da tattara bayanan sirri, kamar yadda ƙasashen uku suka bayyana.

"An kirƙiri rundunar. Wakilanta sun isa a manyan biranen ƙasashen, kuma ayyukanta na kankama a hankali, in ji masanin.

To amma yanzu ba a san mene ne ke faruwa ba. "Na yi tunanin cewa ƙasashen ƙungiyar AES na son mayar da martani cikin sauri. Abu ne na lokaci, amma tabbas ya kamata a ɗauki mataki cikin hanzari saboda akwai buƙatar hakan.," in ji Dr Abba.

Ya ƙara da cewa: "Yarjejeniyar da ta kafa ƙungiyar AES ta tanadi haɗin gwiwa a fannin soji da tattalin arziƙi. Na yi amannar cewa duk za su so yin hakan."

Shi kuwa Mista Louankade cewa ya yi idan aka yi la'akari da cewa rundunar hadin gwiwar ba ta riga ta kafu yadda ya kamata ba, abu ne mai haɗari ga sauran ƙasashen biyu su tura dakarunsu zuwa Mali bayan kuma su ma suna da nasu matsalolin tsaron da suke fama da su.

Bayanin Dr Sadik ya nuna cewa ana shirya kai ɗauki daga ƙasashen AES, ko da kuwa akwai tafiyar hawainiya game da shirin.

Ya ce Nijar ta yanke shawarar tallafa wa Mali da kimanin tankokin man fetur 100. Sai dai ba a san yadda wadannan tankoki za su iya isa cikin ƙasar ta Mali ba.

Ta yaya za a dakatar da JNIM?

Une foule de personnes dans une station d'essence en train d'attendre.

Asalin hoton, Reuters

Ba kasashen AES kawai ba, yankin gaba daya ya dauki wannan barazana ta masu ikirarin jihadi a matsayin abin damuwa. Saboda haka akwai bukatar ganin an hada karfi domin shawo kan matsalar.

Domin a cewar Dr Sedik Abba, rushewar kasar Mali zai yi mummunan tasiri ga kasashe irin Senegal da Guinea da kuma Ivory Coast, wadanda ba sa cikin kungiyar AES amma suna cikin ECOWAS.

”Yana da muhimmanci a hada karfi a yankin. Yana da kyau a koma kan teburin shawara tsakanin AES da ECOWAS, musamman a kan abubuwa da za su amfani kowa, kamar batun tsaro.

A nasa ra’ayin, nuna goyon baya ba yana nufin sai an tura sojoji zuwa Mali ba, amma kasashen ECOWAS za su iya taimakawa ta hanyar tallafi na tattalin arziki.

Hervé Wendyam Louankande, masani a Cibiyar kwararru masu bincike kan zaman lafiya da ci gaban Afirka, da ke Netherlands ya nuna cewa kasashen uku da kansu suka yanke shawarar ficewa daga ECOWAS.

To amma bai kamata kungiyar ta bari kasashen su rushe ba sanadiyyar ayyukan kungiyoyin masu ikirarin jihadi. Zaman lafiyar yankin baki daya na cikin barazana.