Ƙauyen da ya zama na marayu zalla bayan mummunan harin Rasha a Ukraine

- Marubuci, By Zhanna Bezpiatchuk in Hroza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Ukrainian
Matashi Dima ya rasa iyaye da kakanninsa biyu sakamakon wani harin makami mai linzami da aka kai ƙauyensu na Hroza a arewa maso gabashin Ukraine.
"Na kasa fahimtar abin baki ɗaya," kamar yadda matashin mai shekara 16 ya shida wa BBC. "Yanzu ni ke kula da gidanmu," a cewarsa, ya ƙara cewa: "Na fi tausaya wa ƙaramar ƙanwarmu.
Kafin abin ya faru, ba ta so na rungume ta, amma a yanzu da kanta take rungume ni saboda babu wanda za ta runguma a gidanmu in ba ni ba."
A ranar 5 ga watan Oktoban 2023, wani harin makami mai linzami ya fada kan wani kantin shan shayi a Hroza inda ya kashe mutum 59.
Aƙalla mutum guda na kowane gida a ƙauyen ya halarci jana'izar wani mutum da ake kira Andriy Kozyr, wanda ya shiga rundunar sojin Ukraine a matsayin ɗan sa kai.
An kashe kashi ɗaya bisa biyar na al'ummar ƙauyen, galibin mutanen da suka mutu iyaye ne, a don haka yanzu an san Hroza a matsayin ƙauyen da ya cika da marayu.
Harin shi ne mafi muni ga farar hular Ukraine tun da Rasha ta ƙaddamar da mamaya a ƙasar shekara biyu da suka gabata.
Rasha ba ta taɓa fitowa ta yi tsokaci kan harin ba, amma sojojinta sun ce sun kai hare-hare kan yankunan sojoji a yankin, a cewar kafafen yaɗa labaran Rasha.
Ukraine ta ce babu sansanin sojoji a kusa da ƙauyen, kuma wani rahoto da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar ya tabbatar da hakan inda ya ce "Babu wata alama ta sojoji ko wasu halastattun wuraren sojoji na doka."

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dima ya taso kamar kowa kafin yaƙin inda yake zaune tare da mahaifansa, ya shaƙata tare da abokai, akasari a kan wayarsa, wani lokacin ya yi hira da ƙannensa.
A wata maƙabarta da ke wajen ƙauyensa, Dima ya ƙura ido kan furannin da suka lulluɓe sabbin kaburburan da aka haƙo na iyaye da kakanninsa.
Har yanzu ba a yi musu shaida ba amma an sa katako mai alamar kuross tare da hotunan fuskokinsu cikin murmushi.
Akwai masu ziyara kaɗan a nan. Ƙauyen Dima da ke yankin Kharkiv a Ukraine yana kusa da iyakar Rasha kuma ana ƙazamin faɗa a kewayen garin Kupyansk mai nisan kilomita 30.
Furanni masu launin tutar Ukraine sun bayyana inda ƙarar fashe-fashe daga nesa ke katse shirun da wurin ya yi.
Cikin ɗimuwa da jimami, Dima da ƙannensa sun koma wurin iyayan mahaifiyarsu domin samun kulawa.
"Harin ya kashe mutane da dama. Nan da nan ƙauyen ya zama kufai,"
Kakan Dima mai shekara 62 Valeriy ya yi bayani cewa "Ba za a taɓa manta raɗaɗin ba.
Mun samu akwatin gawa huɗu a gidan. Zuciyata ta fahimci abin da ya faru, amma har yanzu zuciyata ta kasa fahimta."
Ya nuna min hoto na ƙarshe da aka ɗauka na ƴarsa Olga da mijinta Anatoliy. "Sun nuna min ƙauna sosai," Valeriy ke tunawa: "Gida ne mai kyau."

Asalin hoton, Valeriy Kozyr
Valeriy ya ce Anatoly ya taɓa faɗin da wasa cewa idan ya mutu kafin Olga, za ta ci gaba da rayuwarta ne kuma ta sake aure.
"Amma sai Olga ta ce, 'A a, ya Anatoliy, za mu mutu a rana ɗaya.'
Kamar ta san yadda ajalinsu zai zo," in ji Valeriy, yayin da yake share hawayen da zuba a idonsa.
Valeriy ya bayyana bayan harin na watan Oktoba kamar 'fim ɗin ban tsoro da aka gaggauta yin sa".
Ya yi gaggawar zuwa nemo ƴarsa amma bai kai ga yin haka ba a kan lokaci. Wata mata da ke tare da Olga lokacin da ta mutu ta faɗa masa:
"Kalamanta na ƙarshe: 'Ina son na ci gaba da rayuwa."
Valeriy da matarsa Lubov sun ɗauki riƙon Dima da yayarsa Daryna mai shekara 17 da ƙanwarsa Nastya mai shekara 10.
"Dole jikokina su zauna a wajena, a nan. Ba zan iya barin wannan iyalin ya ɗaiɗaita ba," in ji shi, ya ƙara da cewa ya damu cewa yaran na iya tsintar kansu a gidan marayu.
Duk da cewa Valeriy ya yarda cewa kula da jikokinsa ba abu ne mai sauƙi ba, ya ce suna tare da juna a wannan lokaci.
"Dima yana taimakawa a lambu wajen kula da aladu. Daryna ta koyi girki sannan Nastyna tana da tunani da kirki."

Asalin hoton, Valeriy Kozyr
Yara 14 a ƙauyen sun rasa aƙalla ɗaya cikin mahaifansu a harin, ciki har da takwas da suka rasa duka mahaifansu. A duka irin haka, kakanni da sauran ƴan uwa sun yanke shawarar kula da yaran don kada a tura su gidajen marayu.
Galibin mutane na tunanin abin da ya faru. "Ba zan taɓa mantawa da jana'izar ba lokacin da yaran ke tsaye sun yi shiru cikin kaɗaici suna riƙe da hannun juna," Diana Nosova, da ke zaune a yankin ya faɗa min. "Zuciyata ta karaya."
Bayan harin, wasu marayu sun yanke shawarar zuwa wuri mai tsaro ciki har da Vlad mai shekara 14. Ya koma zama a yammacin Ukraine tare da yaruwar mahaifansa bayan da aka kashe duka mahaifiyarsa da kakansa da ɗan uwan mahaifansa da kuma ɗan ƴaruwarsa mai shekara takwas.
"Na yi kewar su sosai," kamar yadda ya faɗa wa kakarsa Valentyna ta bidiyo. "Nima haka," ta ce.
Valentyna ta yanke shawarar zama a ƙauyen duk da rasa akasarinta danginta a harin, har da mijinta da ƴarta da ɗanta da jikanta.
Ina tattaki da mai shekara 57 a ƙauyen inda ta shafe rayuwarta tana zama. Amma abubuwa sun sauya yanzu.
"Wuri ne mai ban tsoro," ta faɗa min yayin da muke bi ta gaban ginin da ya ruguje inda harin makami ya shafa. "Abu ne mai wahala. Idan ka ji cewa yaranka suna kwance a ƙasa. Ga mutuwarsu ta zo."
"Yayin da lokaci ke wucewa, ina jin raɗaɗi. Ba ni da kowa. Kusan babu wanda ya tsira.
Valentyna ta ce tana samun sauƙi a wurin dabbobinta - karnuka biyu da kyanwarta mai suna Stephan. Ta ce hankalinta ya karkata kan Vlad. Tana son ya samu ilimi mai ƙarko. Tana yawan kiransa ta bidiyo kuma ta biya masa a riƙa koya masa darasin fasaha. Amma abu mafi muhimmanci tana son Vlad ya samu tsaro kuma ta ce ta ji daɗi ba ya yankin Kharkiv.












