Wadanne matakai kungiyar G7 take dauka a kan yakin Ukraine?

An yi taron ƙasashen G7 na bana ne a Jamus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi taron ƙasashen G7 na bana ne a Jamus

Shugabannin kungiyar G7 ta kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya, suna gudanar da taro a Jamus domin yanke shawara kan karin matakan da za su dauka a kan Rasha sakamakon hare-haren da take kai wa Ukraine.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi jawabi a wurin taro na G7 ta hanyar bidiyo, inda ya yi kira da su bai wa kasarsa shi karin makamai sannan ya ce yana so a kawo karshen yakin daga yanzu zuwa karshen shekara "kafin hunturu ya iso".

Mece ce G7?

Tutocin kasashen G7

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kungiyar ta G7 ta kunshi kasashen da suka hada da Canada, da Faransa, da Jamus da Italiya da Birtaniya da Amurka da kuma Japan.

Ana kiran G7 da suna "Kungiyar Kasashe Bakwai".

Kungiya ce ta kasashen da suke kiran kansu "mafiya ci gaba" a fannin tattalin arziki, wadda ta mamaye harkokin cinikayya da tsarin kasuwancin kasashen duniya.

Kungiyar ta G7 ta kunshi kasashen da suka hada da Canada, da Faransa, da Jamus da Italiya da Birtaniya da Amurka da kuma Japan.

Ministoci da jami'ai daga kasashen kungiyar ta G7 sukan yi taro, su samar da matsaya kan batutuwa daban-daban sannan su wallafa matsayar tasu kan al'amuran da suka shafi kasashen duniya.

A ina ake gudanar da taron kungiyar G7 na shekarar 2022?

Schloss Elmau, a castle retreat in the Bavarian Alps

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A bana an yi taron ne a yankin Bavarian Alps a Jamus

Jamus ce ta karbi ragamar shugabancin kungiyar G7 a watan Janairun 2022, abin da ke nufin ita za ta karbi bakuncin taron kungiyar na kwanaki ukut - wanda ake gudanarwa daga ranar 26 zuwa 28 ga watan Yuni.

Taron shi ne karo na 48 da kungiyar ta G7 take gudanarwa kuma ana yin sa ne a wurin shakatawa na Schloss Elmau da ke yankin Bavarian Alps.

Shin Tarayyar Turai mamba ce ta G7?

Ana yawan ganin shugabanni tara a wurin taron G7 inda suke daukar hoto a matsayin "iyali daya"

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana yawan ganin shugabanni tara a wurin taron G7 inda suke daukar hoto a matsayin "iyali daya"
BBC info graphic

Tarayyar Turai ba mamba ba ce ta kungiyar G7 sai dai tana halartar taron da suke yi.

Tana zuwa taron ne a matsayin bakuwa, kuma shugaban Majalisar Tarayyar Turai da kuma shugaban Hukumar Tarayyar Turai ne suke wakiltarta a wurin taron.

Shi ya sa sau da dama kuke ganin shugabanni tara a cikin hoto a wurin taron kungiyar - wadanda suke bayyana kansu a matsayin "iyali daya".

Me ya sa a baya ake kiranta kungiyar G8?

Rasha ta shiga kungiyar a shekarar 1998, abin da ya sa ta zama kungiyar G8, amma an cire ta daga cikin kungiyar a 2014 saboda mamayar da ta yi wa Crimea.

China ba ta taba zama mamba a kungiyar ba, duk da karfin tattalin arzikinta da kuma kasancewa mafi yawan al'umma a duniya.

Its relatively low level of wealth per person means it's not seen as an advanced economy in the way the G7 members are.

Me kungiyar G7 take yi a kan Ukraine?

Zelensky

Asalin hoton, Nur via Getty Images

A tsakaninsu, tuni kasashen kungiyar G7 suka sanya takunkumi a kan Rasha wanda shi ne mafi girma da aka kakaba kan tattalin arzikinta.

Sun hana kasar gudanar da harkokin cinikayya da tsarin kudi na kasashen duniya, kuma sun hana attajiran kasar taba dukiyoyinsu da ke kasashensu.

Kasashen kungiyar G7 mambobi ne na kungiyar tsaro ta Nato kuma sun bai wa Ukraine makamai da sauran kayan soji.

Wanne mataki kuma kungiyar G7 za ta iya dauka?

Construction workers at Nord Stream 2 site in Lubmin, Germany

Asalin hoton, AFP

Tambaya a nan ita ce shin shugabannin kungiyar G7 sun shirya daukar matakai masu kaushi a kan Rasha wadanda su ma za su shafi tattalin arzikinsu.

Daya daga cikin manyan batutuwa shi ne ko za su daina sayen fetur da gas daga Rasha kwata-kwata.

Amurka ta daina sayen dukkan man fetur da gas daga Rasha, yayin da ita ku,ma Birtaniya take rage yawan makamashin da take saya daga Rasha daki-daki har ta daina saya baki daya daga yanzu zuwa karshen shekara.

Shugabannin Ukraine sun zaku su ga su ma sauran shugabannin kungiyar G7 sun bi sahu.

Sai dai kasashen turai suna sayen kashi daya cikin hudu na fetur dinsu da kuma kashi arba'in cikin dari na gas din da suke amfani da shi daga Rasha, kuma kawo yanzu abin da kawai Tarayyar Turai ta yi shi ne rage sayen kashi biyu cikin uku daga Rasha.

Photo from the G7 summit of the leaders, tweeted by the German government on 9 June 2018

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Daya daga cikin tarukan G7 wanda ya ja hankali - inda a 2018 Shugaba Trump ya yi watsi da sanarwar bayan taron da kasashen kungiyar G7 suka amince da ita, ciki har da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel

A wani sakon tiwita, ma'aikatar wajen Ukraine ta roki mambobin kungiyar G7 su dauki karin matakai, tana kira ga shugabanninta su "dakatar da daukar nauyin yaki na kudi, su daina biyan Rasha idan suka sayi makamashinta.

Daya daga cikin mafita ga kasashen Turai ita ce su kulla yarjejeniya da Amurka domin shigar da gas dinta.

A halin da ake ciki taron na kungiyar G7 yana tattaunawa kan wannan batu.

Shin kungiyar G7 tana karfin iko?

G7 leaders as puppets

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane suna zanga-zanga a Munich a yayin da G7 ke gudanar da taro

Ba za ta iya zartar da wata doka ba saboda kasashen da ke cikinta suna da mabambanta tsarin dimokuradiyya.

Sai dai a baya matakan da ta dauka sun yi tasiri sosai a harkokin duniya. Alal misali, kungiyar G7 ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa gidauniyar kasashen duniya domin yaki da maleriya da cutar Aids a 2002.

Gabanin taron kungiyar G7 na shekarar 2021 a Birtaniya, ministocin kudi na kasashen sun amince su tilasta wa manyan kamfanoni biyan karin haraji.

Kazalika kungiyar ta samar da kudi ga kasashe masu tasowa domin shawo kan matsalar sauyin yanayi.