Yakin Ukraine: Ba mu ce Rasha ba ta da laifi ba kwata-kwata amma ba mu yi abin kunya ba - Lavrov

    • Marubuci, Daga Steve Rosenberg
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Russia Editor, Moscow

Wannan hira ce tsakanin Editan Sashen Rasha na BBC Steve Rosenberg, da Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov.

Russia foreign minister Sergei Lavrov

Tun bayan da dakarun sojin Rasha suka kutsa Ukraine kusan wata huɗu da suka gabata, an kashe dubban fararen hula tare da lalata gidaje, yayin da miliyoyin ƴan Ukraine suka gudu suka bar gidajensu.

Amma a ranar Alhamis, Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya kalle ni a cikin ido ya gaya min cewa abubuwa fa ba kamar yadda ake faɗa suke ba.

"Ba mu kutsa Ukraine ba," ya ce.

"Mun ƙaddamar da wani aikin soji na musamman ne saboda ba mu da wata hanya ta bayyana wa ƙasashen Yamma cewa son sanya Ukraine a cikin ƙungiyar Nato babban laifi ne."

Tun bayan da Rasha ta kutsa Ukraine ranar 24 ga watan Fabrairu, Mista Lavrov bai yi hira da yawa da kafafen yaɗa labaran ƙasashen Yamma ba.

Ya nanata kalaman fadar gwamnatin Rasha cewa akwai ƴan Nazi a Ukraine. Jami'an Rasha sun sha ikirarin cewa sojojinsu na korar aƙidar Nazi ne a ƙasar.

Mista Lavrov ya jawo ce-ce-ku-ce a baya-bayan nan a lokacin da ya yi ƙoƙarin danganta batun ƴan Nazi da shugaban ƙasar Ukraine, wanda Bayahude ne, inda ya yi kalaman tsokana cewa Adolf Hitler yana da jinin "Yahudawa."

Na ambato masa wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya a kan ƙauyen Yahidne na Ukraine a yankin Chernihiv, inda aka ce sojojin Rasha sun turasa wa "mazauna wajen 360 da suka haɗa da yara 74 da mutum biyar masu lalurar nakasa zama a wani ɗaki na ƙarƙashin ginin wata makaranta tsawon kwana 28.

Babu ban-ɗakuna, babu ruwa... har sai da mutum 10 suka mutu".

Russia's foreign minister Sergei Lavrov (on screen) addresses with a pre-recorded video message at the 49th session of the UN Human Rights Council at the European headquarters of the United Nations in Geneva, Switzerland

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Babu wanda ya damu da saurarar Sergei Lavrov lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban kwamitin kare hakkin ɗan adam na MDD ran 1 ga watan Maris

"Hakan ma yaƙi da ƴan Nazi ne?" Na tambaye shi.

Mista Lavrov ya ce "Babban abin tausayi ne, amma diflomasiyyar ƙasa da ƙasa da suka haɗa da babban jami'in hukumar kare hakkin ɗan adam ta MDD, da sakataren MDD da kuma wakilan MDD na fuskantar matsin lambar ƙasashen Yamma.

"Kuma ana yawan amfani da su wajen yaɗa labaran ƙaryar da ƙasashen Yamma ke ƙirƙira."

"Ba wai Rasha ba ta da laifi ne kwata-kwata ba. Rasha ba kanwar lasa ba ce. Ba ma jin kunyar nuna ko mu su waye.

Mista Lavrov mai shekara 72, ya wakilci Rasha a matsayin ministan harkokin wajenta tsawon shekara 18, amma a yanzu an ƙaƙaba masa takunkuman ƙasashen Yamma shi da ƴarsa.

US President Joe Biden (L), Russian President Vladimir Putin (C) and Russian Foreign Minister Sergei Lavrov (R) pose for press prior to the US-Russia summit at the Villa La Grange, in Geneva on June 16, 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shekara ɗaya kenan tun bayan da Mr Lavrov ya gana da Shugaba Biden da Shugaba Putin a wani taro a Geneva

Amurka ta zarge shi da bayar da bayanan ƙarya a kan mamayar Ukraine, da kuma na wanda ya fi taka rawa kan kutsen da Rashar ta yi wa mambar Kwamitin Tsaronta.

Sai kuma na koma kan batun dangantakar Rasha da Birtaniya. Tana cikin jerin ƙasashen da Rasha ta sanya waɗanda za ta daina ƙawance da su, kuma na ce batun a ce dangantaka ta lalace ma ɓata baki ne.

"Ba na jin akwai hanyar da za a iya sauya maganar, saboda ai kowa ya san Firaminista Boris Johnson da Truss sun faɗa ƙarara cewa sai sun yi nasara a kan Rasha, sai sun kai Rasha ƙasa. To ga fili ga doki ai, su je su yi!" in ji Mista Lavrov.

A watan da ya gabata ne Ministan Harkokin Wajen Birtaniya ya ce Shugaba Vladimir Putin na Rasha yana ƙasƙantar da kansa a gaban ƙasashen duniya "don haka dole mu tabbatar ya sha kaye a yaƙin Ukraine."

Da na tambayi Sergei Lavrov yadda yake kallon Birtaniya a yanzu, sai ya ce "tana sarayar da buƙatun ƴan ƙasarta a garin neman cimma burukan siyasa."

Sergei Lavrov (R) accused the BBC of not uncovering the truth of Ukrainian actions in areas held by Russian separatists since 2014
Bayanan hoto, Wannan hira ce tsakanin Editan Sashen Rasha na BBC Steve Rosenberg, da Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov

Na sake tambayarsa kan wasu ƴan Birtaniya biyu da ƴan awaren Rasha suka yanke musu hukuncin kisa a yankin gabashin Ukraine.

Sai ya amsa da cewa "da na nuna wa ƙasashen Yamma hakan, Rasha ce ke da alhakin ƙaddararsu. Ba ruwana da yadda ƙasashen Yamma suke kallo lamarin. Damuwata kawai ita ce matakin dokokin ƙasa da ƙasa kan hakan.

"Kuma dokokin ƙasa da ƙasa sun bayyana cewa ba a kallon sojojin haya a matsayin mayaƙa a lokacin yaƙi."

Ni kuma sai na sake cewa ai mutanen suna aiki ne da rundunar sojin Ukraine ba sojojin haya ba ne, sai Mista Lavrove ya ce kotu ce kawai za ta yanke wannan hukuncin.

Sannan ya zargi BBC da faɗar abin da suka ce yana faruwa ga fararen hula a yankunan da ƴan aware ke iko da su a gabashin Ukraine, "bayan kuma an shafe shekara takwas sojojin Ukraine na ruwan bama-bamai a kan fararen hula."

Na dage cewar cikin shekara shida, BBC ta sha tuntuɓar jagororin ƴan awaren da ke aiki a yankunan don neman izinin su je su ga abin da ke faruwa. Amma ko yaushe sai a hana mu shiga.

Rasha ta zargi Ukraine da aikata kisan ƙare dangi. Haka kuma a 2021, fararen hula takwas aka kashe a yankunan da ke ƙarƙashin ikon ƴan tawaye, kamar yadda masu goyon bayan Rasha suka faɗa, sannan aka kashe bakwai a shekarar 2020.

Duk da dai cewa kisa ba daɗi, a ganina lamarin bai kai girman da za a kira shi kisan ƙare dangi ba.

Na ce idan har kisan ƙare dangi aka yi, do da ƴan awaren da ke Luhansk da Donetsk ba za su damu da shigarmu yankin ba. Amma me ya sa ake hana mu shiga, abin da na tambaya kenan.

Sai Mista Lavrove ya ce "Ni ma ban sani."

Ƙarin bayani daga Paul Kirby.