Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda na dawo gida na tarar da gawar ƴaƴana uku a cikin firji'
"Na bar yara na uku a gida na je coci, da na dawo gida, gawarsu na tarar".
Wannan shi ne labarin Madam Chikazor Ogachukwu Ejezie da ta rasa 'ya'yanta uku a rana daya a yankin Nnewi da ke Anambra.
A labarinta ta bar yaranta uku a gida, ta je jarabawa a yankin Ihiala da ke jihar, amma a lokacin da ta dawo, ba ta tarar da kowa ba a gidan, sannan kofar gidanta a buɗe.
Ɗanta namiji da ke cikinsu bai haura shekara uku ba, yayin da yaranta mata akwai mai shekara bakwai da kuma shekara tara.
A labarin da ta bayar ta saki jiki tana hira da tunanin sun fita wasa za su dawo, amma har yamma shiru babu alamarsu, a nan ne tsoro ya kamata ta kuma ankare.
"Na tuntubi matar abokin mijina da 'ya'yanta suke zuwa coci tare da 'ya'yana, amma sai ta shaida min cewa a wannan ranar 'ya'yanta ba su fita ba. Sai na tambaye ta ko yarana na gidanta, amma sai ta amsa da cewa ba sa gidan," a cewarta.
Ta kara da cewa "ɗaya daga cikin makwaftanta sun shaida mata cewa sun ga wasu matasa biyu sun fito daga gidan a wannan rana, kuma sun ga ɗaya daga cikin yarana mata sun fito sun je shago sun yi siyayya, sannan suka koma gida.
'Yadda muka gano gawawwakin yaran'
Daga nan ne suka soma bincike da neman yara ta ko'ina. Daga baya dai suka tsinci gawawwakin yara a cikin firizar gidansu.
Mahaifin yaran, Samuel Ejezie ya fada wa BBC cewa matarsa ta je jarrabawa a Ihaiala, bayan ta koma gida da rana sai ta iske yaran ba sa gida.
Ya ce a ka'ida "idan mamansu ta dawo gida yaran na fitowa su rungume ta, amma a wannan ranar yaran ba su fito domin tarar mamansu ba, kuma ga takalmansu a gidan."
Ya ce daga su sai mahaifiyar mai gidan da suke haya ke rayuwa a gidan, amma a wannan ranar matar ba ta gidan.
"Sauran mutanen da ke rayuwa a gidan masu kula da jarirai ne, kuma ina da tabbacin ba su da hannu a wannan lamarin kuma ba ni da matsala da su," a cewarsa.
Har yanzu an gagara fahimtar yadda wannan yara suka shiga cikin firiza ko wanda ya sa su a firiza, saboda babu wanda ya bada shaidar ganin wani abu.
'Yansanda a Anambra sun tabbatar da labarin, sannan sun ce suna bincike.
Irin wadannan korafe-korafe na mutuwar yara na karuwa a baya-bayanan.
Ko a makonnin baya an rinƙa samun rahotanni na mutuwar wasu yara 'yan gida daya a cikin wata mota da aka ajiye a yankin Nise da ke Anambra.