Abubuwan da suka kamata ku sani kan kafa ƴansandan jihohi a Najeriya

A baya-bayan nan ne Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da a duba yiwuwar kafa rundunar ƴansandan jihohi a ƙasar a matsayin wani mataki na shawo kan matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
Batun kafa ƴansandan jihohi, ɗaya ne cikin batutuwan da aka tattauna a wata ganawa tsakanin shugaban da gwamnonin jihohin ƙasar 36, inda Tinubu ya buƙaci gwamnonin su fara tsara yadda za a aiwatar da shirin.
Sha'anin tsaro ya taɓarɓare a faɗin ƙasar inda a kowace rana ake tashi da sabon labarin sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa da matsalolin ƴan fashin daji.
Batun samar da ƴansandan jihohi abu ne da ake daɗe ana tattaunawa a kai, lamarin da ya sa aka samu rarrabuwar kai a tsakanin al'ummar ƙasar.
Kuma wannan ne karon farko da hukumomi ke duba yiwuwar kafa rundunar a jihohi.
Wannan ne ya sa za mu duba tunanin masana kan abin da ake nufi da ƴansandan jihohi da kuma tasirinsu wajen magance matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya.
Barista Audu Bulama Bukarti, mai sharhi ne kan al'amuran tsaro kuma a tattaunawarsa da BBC ya ce batun kafa ƴansandan jihohi abu ne da ake yawan taso da shi idan matsalar tsaro ta yi ƙamari.
A cewarsa, "tura ta kai bango" saboda yadda matsalar tsaro ke ƙara ruruwa a faɗin Najeriya.
Sai dai ya ce akwai manyan batutuwa da suka kamata a lura da su game da batun samar da ƴansandan jihohi don kada "garin neman gira a rasa ido." kamar yadda masanin ya ce.
Mene ne aikin ƴansandan jihohi, wace matsala za su magance?
Barista Bukarti ya jefa tambaya kan waɗanne matsaloli ne waɗannan ƴansandan za su magance?
Ya ci gaba da cewa shin za a samar da su ne domin magance matsalar Boko Haram ko ta ƴan fashin daji, ko ta masu garkuwa da mutane?
Barista Bukarti ya ce a fahimtarsa, ba ya ganin akwai abin da ƴansanda ko sojojin tarayya suka kasa da har za a ce a kawo ƴansandan jihohi su magance matsalar.
A bayaninsa, ya ce a maimakon kafa ƴansandan jihohi, kamata ya yi hukumomi su mayar da hankali wajen bai wa ƴansandan da ake da su a ƙasa ƙarin horon da ya dace.
Hukumomin Jiha sun fi na tarayya inganci?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Barista Burkarti ya ce yana mamakin yadda za a dage kan son samar da ƴansandan jihohi a Najeriya, yana mai cewa ai yanzu akwai hukumomin da ake da su a matakin gwamnatin tarayya da na jihohi, amma ya ce babu wata hukuma ta jiha da ta fi ta tarayya inganci.
''Shin makarantun jiha sun fi na gwamnatin tarayya ne, ko kuwa asibitocin jiha sun fi na tarayya inganci ne?'', in ji Bukarti.
Masanain ya buƙaci kowane ɗan ƙasar da ya juya ya kalli wata hukuma da take a matakin jiha da tarayya, ya duba wacce hukumar jiha ce ta fi ta tarayya inganci.
''Don haka bana ganin akwai wani abu da za a ce gwamnatin tarayya ta kasa yinsa, sannan kuma a ce gwamnatin jiha ta yi shi, 'yan sanda tarayya suka kasa, sojojin tarayya suka kasa a ce wai sai na jiha ne za su iya'', in masanin.
Ya yi misali da hukumar zaɓe ta ƙasa wadda a baya take shirya zaɓen ƙananan hukumomi daga baya aka mayar da ita ƙarkashin kulawar jihohi.
Masanin ya yi zargin cewa tun da aka mayar da ta ƙarƙashin jihohi, babu jihar da ta shirya zaɓe sahihi.
Ƙalubalen da ke tattare da samar da ƴansandan jiha
Rashin isassun kuɗi: Barista Bulama Bukarti ya ce babban abin tambaya shi ne ko jihohi suna da isassun kuɗaɗe da kayan aikin da ake nema wajen samar da ƴansandan jihohi da horar da su.
A cewarsa, harkar tsaro lamari ne da ke buƙatar kuɗi, don haka yake ganin ɗorewar tsarin zai iya fuskantar ƙalubale matuƙar aka samar da shi.
Ya ce akwai jihohin da ke fuskantar matsala wajen biyan ma'aikatansu albashi sannan "idan ka kafa ƴansandan jihohi sai an ɗebi dubban sababbin ma'aikata da za su zama ƴansanda, sai an buɗe musu ofisoshi, sai an buɗe musu makarantu,"
"Saboda aikin ɗansanda sai ka yi makarantar horas da ƴansanda sannan sai an kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayo makamai da motoci kuma ba abu ne da za ka yi yau ka ce ka gama gobe ba, abu ne da duk wata sai ka yi." in ji Bukarti.
Rarrabuwar kai: Wani ƙalubalen da Bukarti ya bayyana shi ne yadda ake samun rarrabuwar kai a Najeriya.
"A gwamnatin da ta wuce, akwai jihohin da suka fito suke ta maganganu kamar ma ba su yarda da Najeriya ba." a cewar Bukarti.
Hakan ya sa masanin ke ganin za a iya fuskantar matsala idan aka kafa ƴansandan jihohi aka kuma ba su makamai, akwai wasu gwamnonin da za su iya amfani da su wajen kawo barazana a ƙasar.
Hukumomin da aka taɓa mayarwa ƙarƙashin jihohi: Ya kuma yi bayani kan wasu hukumomi da a baya suke ƙarƙashin gwamnatin tarayya daga bisani aka mayar da su hannun gwamnoni matakin da ya ce bai kawo wani ci gaba ba.
''Tun lokacin da aka mayar da hukumar zaɓen jihohi wace jiha ce ta shirya sahihin zaɓe?
Haka kuma Barista Bukarti ya ce tun da aka mayar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin ƙarƙashin mallakin gwamnatocin jihohi, babu ƙaramar hukumar da ta ƙara jin daɗi.
Mece ce mafita?
Barista Bulama Bukarti ya ce mafita a nan ita ce a ƙara yawan jami'an tsron da ake da su a matakin tarayya, sannan a inganta horon da ake ba su na sanin makamar aiki, ta yadda za su samu damar gudanar da ayyukansu ba tare da wata tangarɗa ba.
"Saboda a manufofin Tinubu lokacin da yake yaƙin neman zaɓe, cewa ya yi zai ƙara yawan su ba cewa ya yi za a bai wa jihohi su yi ba." kamar yadda Barista Bukarti ya ce.
A maimakon kafa ƴansandan jihohi, sannan gwamnatin tarayya ta aiko kuɗi domin a biya su albashi, masanin ya ce kamata ya yi jihohin su haɗu da gwamnatin tarayya wajen kafa asusu mai zaman kansa kan abin da ya shafi tsaro a fadin jihohin ƙasar.











