Kada ya ciji wani yaro sanadiyyar ambaliyar ruwa

...

Asalin hoton, Getty Images

Kada ya ciji wani yaro a daidai lokacin da ake ƙoƙarin kwashe mutane daga yankin arewacin Australiya wanda ambaliyar ruwa ta mamaye.

Kadan ya ciji yaron ne ɗan shekara 17 a bayan ƙafarsa daidai lokacin da yake ficewa daga yankin, kamar yadda wani shaida ya bayyana wa gidan rediyon ABC.

BBC ta gano cewa an kai yaron zuwa asibiti domin samun kulawa.

Dama dai an gayyaci dakarun Australiya su taimaka wajen ceto mutane a yankuna da ambaliyar ruwa ta shafa.

Mamakon ruwan sama da aka rinƙa tafkawa ne ya haifar da ambaliyar.

Gwamnan yankin, Chansey Paech ya ce mutane 700 ne, cikin su har da marasa lafiya 35 aka ɗauke su ta jirgin sama zuwa garin Kalkarindji, mai nisan kilomita 770, bayan da rafin Victoria ya ɓalle.

Ya wallafa a shafinsa na tuwita cewar “dakarun Australia sun ba mu gudumawar manyan jiragen sama guda uku domin aikin kwashe waɗanda ambaliyar ta rutsa da su zuwa garin Katherine,”

Mai magana da yawun gwamnan ta ce ambaliyar ta ƙara jefa al’umma cikin haɗarin hari daga kadoji.

Ta shaida wa BBC cewar “da zarar rafin ya ɓalle za ka ga kada a ko ina.”

Hukumomi sun ce za a ajiye waɗanda aka kwashe daga gidajensu ne a wani sansani da aka yi amfani da shi domin kwantar da masu cutar korona, inda a wurin yara za su iya halartar makaranta.

An dai ayyana dokar ta ɓaci a ƙauyuka huɗu cikin wannan mako bayan da rafin Victoria ya cika ya batse sannan ya yi amai.