Yadda shazumami suka gallabi wasu ƙauyukan Indiya

Ɗaruruwan mutane da ke rayuwa a wasu ƙauyuka bakwai a jihar Tamil Nadu a kudancin Indiya, sun ce suna cikin wani hali bayan gallaba musu da shazumami suka yi.

Sun ce shazumamin, sun far wa dabbobinsu da kuma shuka da suka yi, wanda ya sanya hanyar samun abincinsu cikin haɗari.

A cewar ƙungiyar kula da halittu ta duniya, shazumami na cikin halittun da suka fi mamaya a duniya.

Ba sa cizo, amma suna watsa wasu sinadarai da kan yi illa.

Ana kiran dangin halittun da Anopolepsis gracilipes a kimiyyance – sannan ana iya samun su a yankuna masu tsananin zafi.

Suna kuma tafiya a warwatse, inda hakan ke zama abin damuwa a wasu lokutan.

Masana sun ce waɗannan shazumami na ƙaruwa cikin lokaci ƙanƙani, sannan za su iya haifar da babbar barazana ga muhalli.

Yawancin sassan Australiya sun ruwaito mamayar da shazumamin suka musu.

Dr Pronoy Baidya, wani likitan dabbobi da ya gudanar da bincike kan dangin shazumami, ya ce halittu ne masu yawa.

"Ba su da wani abinci da suka dogara da shi. Sukan ci komai da komai," a cewarsa.

Ya ƙara da cewa suna kuma kashe wasu halittu kamar zuma domin su ci. 

Ƙauyukan jihar Tamil Nadu da shazumamin suka shafa na wani yanki mai cike da tsaunuka na dajin Karanthamalai da ke lardin Dindigul.

Yawancin mutanen wajen manoma ne da kuma makiyaya.

"Duk lokacin da muka yi ƙoƙarin zuwa dajin, shazumamin kan hau kanmu, inda hakan ke sanya mu samu raunuka a jiki.

Ba ma kuma iya ɗiban ruwa mu sha saboda sun cika kogunan wurin. Ba mu san me za mu yi ba," a cewar Selvam, wani manomi mai shekara 55.

Mutanen ƙauyen sun faɗa wa sashen BBC Tamil cewa, sun ga irin shazumamin a cikin dajin a shekarun da suka gabata.

Amma wannan ne karon farko da suka fito masu yawa a ƙauyukan, inda hakan ya jefa rayuwar mutane cikin garari.

Makiyayan da suke rayuwa kusa da dajin, sun ce sun bar matsugunansu saboda mamayar shazumamin.

"Tun bayan lokacin da shazumamun suka mamayi gidana, na bar gidan na dawo wannan ƙauye.

Mun kasa shawo kansu, saboda suna da yawa kuma sai ƙaruwa suke yi," a cewar Nagammal, wani wanda shazumamin suka far wa awakinsa.

Wani jami’in gandun daji a yankin, Prabhu, ya faɗa wa sashen BBC Tamil cewa ya bai wa jami’ai umurnin ‘gudanar da cikakken bincike da kuma gabatar da rahoto’".

"Ba zan iya cewa komai ba har sai na samu sakamakon binciken," a cewar Prabhu.

Wani likitan dabbobi na gwamnati, Dr Singamuthu, ya shaida wa sashen BBC Tamil cewa ‘shazumamun ba irin wadanda aka saba gani ba ne".

"Ba mu san me ya sa suka yi mamaya ba. Ba mu kuma san yadda za mu shawo kansu ba.

Haƙiƙanin gaskiya ba za mu iya cewa wannan shi ne matsalar da mutane da kuma dabbobi ke fuskanta ba," a cewarsa.

Ya ƙara da cewa an buƙaci ƙauyawa a yankin da ka da su kai dabbobinsu kiwo zuwa dajin.

Sai dai, ƙauyawan sun yi zargin cewa dabbobinsu har ma da macizai da kuma zomaye sun mutu sakamakon far musu da shazumamin suka yi.

Dr Baidya, ya ce nau’ukan sinadarai da daruruwan shazumami ke watsawa, sun shafi idanun dabbobi, amma ya kara da cewa ‘ba a dai san ko idanun dabbobin suka nufa ba’"

A bangaren ‘yan adam kuwa, ya ce sinadaran za su iya jawo musu cututtuka amma ba masu barazanar kisa ba.

Masana sun damu cewa watsuwar wadannan shazumami, zai iya shafar halittun yankin.

A lokacin da shazumamin suka fara mamaye tsibirin Chritsmas na Australiya, sun daidaita wasu halittu a yankin ta hanyar far musu da kuma toshe wuraren da suke samun abinci, a cewar Dr Baidya.

Sun kuma kashe miliyoyin kaguwa a tsibirin ta hanyar far musu.

Wani masanin ƙwari, Dr Priyadarshan Dharmarajan, ya ce shazumamin suna cudanya da wasu nau’ukan kwari da ke yin illa ga shuka.

"Suna samun abinci ne kan wasu ƙwari, da ke barnata shuka," a cewarsa.

Dr Dharmarajan ya ce matsalar ta munana a yanzu saboda karuwar yanayin zafi.

"A lokacin da yanayin zafi na muhalli ya karu, suna ƙaruwa, wand hakan ke sa su cin abinci da yawa.

Wannan zai iya zama dalili," a cewarsa, inda ya ƙara da cewa ba za a iya tabbatar da hakan ba sai an yi bincike.

"Ya kamata mu samu Karin bayanai dangane da yanayi a yankunan da shazumamin suka mamaye kafin mu san mataki na gaba.’’