Kalamai 6 da ba su dace ma'aurata su faɗa wa juna ba idan suna gardama
- Marubuci, Alicia Hernández
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
- Lokacin karatu: Minti 4
Mutane da dama kan yi amfani da wani salo na nuna wa abokin hulɗarsu cewa akwai matsala a tunaninsu. Sai dai akasari sukan yi hakan ne domi neman wani abu a wurin ɗaya ɓangaren.
"Ɗabi'a ce ta ɗan'adam, duk da cewa akwai lokutan da muke aikatawa ba tare da mun san muna aikata su ba," a cewar Cortney S. Warren, wata masaniyar halayyar ɗan'adam a Jami'ar Harvard.
Matsalar wannan salon ita ce mutum ba shi iya sanin lokacin da wani zai yi amfani da shi a kan sa ba shi ma.
To ta yaya mutum zai kiyaye kada ya faɗa irin wannan tarkon?
Ɗaya daga cikin manyan hanyoyi shi ne idan wani ya ce maka wani abu da zai sa ka ji rashin natsuwa, "ko kuma kamar dai kana dakushe kanka da kanka," in ji Warren.
Masaniyar ita ce marubuciyar litafin Letting Go of Your Ex: Skills to Heal the Pain of a Breakup and Overcome Love Addiction.

Asalin hoton, Cortesia
Ta bayar da shawarar cewa mutum ya ɗan dakata duk loakcin da wani ya faɗa masa wata kalma "mai guba" da za ta sa ya ji rashin daɗi.
Warren ta taƙaita wannan salon cikin matakai uku: ankarewa, da nazari, da ɗaukar mataki.
Ta ce hikimar yinhakan ita ce mtum ya san kansa domin gina ƙwarin gwiwar da zai iya mayar da amsa ga duk wanda ya nemi ya sace masa gwiwa.
Ta bayyana abubuwa shida:
1. 'Kai mahaucki ne / Ba ka da juriya'
A cewar masaniyar, duk mutumin da ya faɗi waɗannan yana nufin ɗayan ba shi da fahimtar abubuwa.
Duka waɗannan kalaman ba su taimakawa a lokacin da mutum biyu, musamman ma'aurata, ke gardama da juna tun da mai faɗinsu yana kore duk wata suka ne daga ɓangarensa.
Bugu da ƙari, idan ka faɗa wa mtum cewa yana wuce kima a tunaninsa hakan na nufin ba ka damu da tunaninsa ba, in ji Warren.
Amsar da za a iya bayarwa a irin wannan yanayi ita ce:
"Kana tunanin ina wuce kima a tunanina, to abin da nake ji kenan yanzu. Abin da na yi imani da shi kenan, kuma abin da nake gani kenan."
"Ba zan yi musu kan abin da nake ji ba. Zan saurare ka amma ina fatan za ka mutunta halin da nake ciki yanzu."
Masaniyar ta ce mutum zai iya ɗaukar hutu daga tattaunawar har zuwa lokacin da zukata za su ɗan kwanta.
Za ku iya cewa: "Zan je na ɗan nimfasa minti ɗaya kafin na ci gaba da magana."
2. 'Wasa nake yi'
Wannan kalamin da ka iya zama mai cutarwa, na zuwa ne bayan abokin sa'i'nsa ya mayar wa mutum martani mai zafi, kamar yadda Warren ta bayyana.
Wani zubin mutane kan aikata abin da bai dace amma sai su basar su nuna kamar wasa suke yi duk da cewa da gaske suke yi.
Amasar da mutum zai iya bayarwa a nan ita ce: "Kai a tunaninka wasa ne, ni ba wasa ba ne a wajena kuma ta ɓata min rai."

Asalin hoton, Getty Images
3. 'Kai ka jawo na aikata haka / laifinka ne'
Mutane masu dabara na son su dinga ɗauke laifi daga kansu saboda wani abu da suka aikata ba daidai ba.
Za su iya faɗin abubuwa kamar "na yi maka masifa ne saboda ka yi kuskure yau". Ko kuma "ka dawo gida latti shi ya sa na yi maka faɗa".
Amma masaniyar ta bayyana ƙarara cewa: "Ba za ka taɓa zama mai laifi ba saboda abin da wani ya aikata."
Haka wasu abokan zaman kan yi amfani da dabarar wajen zargin abokansu da saka su aikata komai duk loakcin da suka yi ba daidai ba.
Amsoshin da za a iya bayarwa a irin wannan yanayi su ne:
"Halayenka na nuna irin tunaninka, ba nawa ba."
"Ko da na aikata wani abu da bai yi maka daɗi, martanin da ka mayar zaɓinka ne, ba nawa ba."
4. 'Idan kana so na za ka iya yin haka, / bari na yi kawai'
A cewar Warren, akasarin masu neman agajinta kan irin wannan matsala masoya ne, waɗanda idan suna gardama ɗaya ke ɗora musu nauyin yin komai da komai.
"Wani lokacin mutane kan yi amfani da irin wannan dabara wajen neman abubuwa da yawa game da saduwa waɗanda suka san abokan zamansu ba su so kawai don matsa musu sauya tunani," in ji ta.
A cewarta, irin wannan salon na jawo wanda aka faɗa wa ya ji kamar ya aikata laifi, da kuma cewa yana da taurin kai.
Shawarar da ake bayarwa a irin wannan yanayi ita ce mutum ya yi ƙoƙari ya gano abubuwan da tabbas ba ya son su kuma ya riƙe wuta a kansu.
Abubuwan da za a bayar d amsa da su sun ƙunshi:
"Dalilin da ya sa ba zan yi ba ba shi da wata alaƙa da son da nake yi maka. Ina ƙin yi ne saboda halina kenan kuma a haka nake so na rayu."
"Ba na jin daɗin yin hakan. Kana iya cewa saboda ba na so ka ne, amma dai ni ba na son yi."

Asalin hoton, Getty Images
5. 'Kowa ya yarda da ni ban da ke/kai...'
Wasu mutanen kan yi amfani da maganar cewa kowa yana amincewa da tunaninsu amma ban da mata ko mazajensu kawai saboda su nuna abin da suke faɗa ne daidai.
Suna kuma son su nuna cewa mutumin da suke faɗa wa maganar, halayensa na da tsauri.
A cewar Warren, irin waɗannan mutanen na ƙasƙantar da abokan zaman nasu ne ta hanyar neman agajin wani.
Ana iya ba su amsa da cewa:
"Na fi so ka yi magana a kan kanka, ba wai ka yi magana da yawun wasu ba."
6. 'Kai/ke ce babbar matsalar...'
Wannan salo ne na yunƙurin sauya maudu'in da ake magana a kai, da zimmar kawar da batun da ake magana.
Warren ta ce mutum ya yi bakin ƙoƙarinsa wajen ci gaba da tattauna batun saboda burin abokin gardamarsu shi ne sauya batun.
Ana iya ba su amsa da cewa:
"Ka san ina son mu tattauna a kan komai, amma matsalar da nake fuskanta yanzu wannan ce."
"Wannan magana ce ta daban, wadda zan so mu tattauna a nan gaba idan kana so. Amma yanzu wani abu daban muke magana."











