'Mahara sun turo wasiƙa kafin kai hari a Kwara'

Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura bataliyar soji zuwa sassan jihar Kwara, bayan mummunan harin da ya yi sanadiyyar kisan gomman mutane a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar.

Shugaba Tinubu a wata sanarwa da kakakinsa Bayo Onanuga ya fitar ranar Laraba da dare ya kuma naɗa kwamandan da zai jagoranci rundunar sojin da za a tura jihar Kwara, wadda za ta gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya da aka yi wa laƙabi da 'Operation Savanna Shield'.

Gwamnatin Najeriya ta ɗauki wannan mataki ne bayan harin da aka kai wa ƙauyen Woro, inda rahotanni ke cewa an tattara gawarwakin mutane 78 da maharan suka kashe.

Hon Sa'idu Baba Ahmed, ɗan majalisar dokokin jihar Kwara ne, kuma ya shaidawa BBC cewa sun yi jana'izar sama da mutane 70 daga cikin waɗanda maharan suka kashe.

Ya ce ''abin da dai na gani, waɗanda muka yi wa sallah, mutum 78 ne amma akwai waɗanda aka ƙone a cikin gidajensu, ba mu san adadin su ba tukun. An hallaka mutum zai kai 170.''

Hon. Baba Ahmed ya kuma ce maharan ''sun wuce da mata 38,'' daga ƙauyukan da suka kai wa hari.

Ya yi bayanin cewa sarkin garin ya shaida masu cewa maƙonni uku da suka wuce an rubuta mashi wasiƙa cewa za su zo su yi wa'azi a wajen, lamarin da ya sa shi kuma sarkin ya bayar da rahoto ga jami'an tsaro.

Ɗan majalisar ya ce daga cikin mutanen da suka yi wa jana'iza a ranar Laraba da yamma, akwai maza 75 da mata uku, sannan akwai wasu mutum bakwai da aka garzaya da su asibiti saboda munanan raunin da suka samu.

A yanzu dai ana sa ran rundunar 'Operation Savanna Shield' da shugaba Tinubu ya tura jihar Kwara ta iya samar da tsaro ga jama'ar yankin da yanzu haka suke cikin fargaba, da kuma kare sauran sassan jihar daga irin wannan mummunan hari.

Masu tsattsauran ra'ayi ne suka kai harin - Gwamnatin Kwara

Hukumomi a jihar Kwara da ke tsakiyar Najeriya sun ce masu tsattsauran ra'ayin addini ne suka kai mummunan harin da ya kashe gomman mutane a jihar, ba ƴanbindiga ba.

Gwamnan jihar, Abdulrahman Abdulrazaq wanda ya tabbatar da matakin shugaba Tinubu na tura bataliyar soji domin samar da tsaro a jihar, a yayin ziyarar da ya kai yankin a ranar Laraba da dare, ya ce an kai wa mutanen hari ne saboda sun ƙi amincewa da wata sabuwar aƙidar musulunci da maharan suka gabatar masu.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a lokacin da ya ke jawabi a fadar sarkin Kaiama, Alhaji Muazu Omar.

‎Ya kuma bayyana harin a matsayin harin ƙare-dangi, wanda ya bai wa jama'ar jihar tabbacin cewa za su yi duk abin da ya dace domin kamo masu hannu a ciki da kuma wanzar da tsaro ga jama'a.

Rahotanni sun ce an jibge sojoji da sauran jami'an tsaro a yankin, inda suke tabbatar da tsaro da kuma bin sahun maharan da suka aikata wannan ɓarna.

Dama dai hukumar agaji ta Red Cross a Najeriya ta ce akwai mutane da dama da ba a gano inda suke ba tun bayan harin, inda ƴanbindiga suka ƙona shaguna da gidaje bayan kashe mutane da kuma garkuwa da wasu.

Yadda aka kai harin

A ranar Talatar da ta gabata ce al'ummar jihar Kwara, musamman na yankin Irepodun suka shiga tashin hankali bayan harin.

Hon Sa'idu Baba Ahmed, ɗanmajalisar jiha da ke wakiltar yankin a jihar Kwara ya shaida wa BBC ya ce ƴanbindigar sun ƙona shaguna masu yawa, yayin da wasu kuma suka tsere daji da raunuka.

Hon Sa'idu Baba Ahmed ya ce ƴanbindigar sun ƙone fadar sarkin garin gabaɗaya har da shagunan da ke kusa da fadar.

Ya ce jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji da ke yankin sun shiga dajin bayan samun labarin harin amma babu tabbaci ko sun haɗu da ƴanbindigar da suka kawo harin.

Ko a kwanan baya ƴanbindigar sun kai hare-hare a jihar Kwara inda suka kashe mutane a Nuku da ke cikin ƙaramar hukumar Kaiama da ke maƙwabtaka da Woro.

Ɗanmajalisar ya ce akwai wasiƙa da ƴanbindigar suka rubutuwa sarakunan Nuku da Woro cewa za su kawo hari, matakin da ya sa aka baza sojoji.

"Amma ba su shigo ba a lokacin da aka girke sojoji, sai a ranar Talata suka shigo suka yankin," in ji shi.

Ana tunanin ƴanbindigar sun fito ne daga dajin Borgu a jihar Neja da ke maƙwabtaka da jihar Kwara.