Su wane ne shugabannin Boko Haram da ISWAP a yanzu?

Lokacin karatu: Minti 5

A ƴan kwanakin nan sojojin Najeriya sun bayyana samun nasara a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a jihar Borno.

Ko a ranar Lahadi, sojojin sun bayyana kisan Abu Khalid, “mutum na biyu mafi girman muƙami a Boko Haram a yankin dajin Sambisa,” a cewar sanarwar da sojojin suka fitar.

Sanarwar ta ce sun samu nasarar kashe Abu Khalid, da wasu mayaƙansa 10 a wani samame cikin dare da suka kai maɓoyar mayaƙan.

Kisan nasa na zuwa ne kwana daya bayan sojoji sun kawar da wani gawurtacen kwamandan Boko Haram, da ake kira Julaibib a yankin Gujba.

Ƙungiyar Boko Haram dai ta kwashe shekaru tana ƙaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Tun bayan fara rikicin na Boko Haram a shekarar 2009, shugabannin ƙungiyar da suka fi kaurin suna su ne Muhammad Yusuf da ya assa ta, sai kuma Abubakar Shekau wanda ya karbi jagoranci jagorancin ƙungiyar, kafin ɓallewar tsagin ISWAP ƙarƙashin jagorancin Abu Mus’ab Al-Barnawi.

Sai dai tun bayan kisan shekau a 2021, Boko Haram da ISWAP sun ci gaba da gudanar da ayyukansu a ware, ƙarƙashin jagorancin sabbin shugabanni, wadanda a mafi yawan lokuta ba kowa ne ya san su ba.

To ko su wane ne shugabannin ƙungiyoyin biyu a halin yanzu?

Dokta Audu Bulama Bukarti mai bincike ne kan ayyukan ƙungiyoyin masu dauke da makamai a yankin Sahel ya yi wa BBC bayani game da wasu daga cikin fitattun jagororin ƙungiyar Boko Haram.

Jagororin Boko Haram

Boko Haram ita ce babbar ƙungiyar da ta fara tayar da kayar baya a arewa maso gabashin Najeriya, inda daga baya ta dare zuwa gida biyu - wadda tun asali Muhamamdu Yusuf ya assasa.

Bayan kisan da aka yi wa Yusuf, sai Abubakar Shekau ya karɓi ragamar ƙungiyar, inda ya jagorance ta kuma ya yi suna fiye da Muhammad Yusuf.

Bayan mutuwarsa akwai waɗanda suka ja ragamar ƙungiyar, kamar haka:

Bakura Doro - Shugaba

Asalin sunansa shi ne Ibrahim Muhammadu ɗan asalin garin Doron Baga da ke arewacin jihar Borno, kuma ana yi masa alkunya da Abu Humaimah ko Abu Humaimata.

Bulama Bukarti ya ce Bakura Doro matashi ne wanda ya karbi shugabancin kungiyar yayin da shekarunsa ba su fi 30 da wani abu ba, kuma yanzu haka Bakura Doro shi ne shugaban ƙungiyar Boko Haram ɓangaren Abubakar Shekau.

''Kuma ya zama shugaban ƙungiyar ne tun lokacin da aka kashe Abubakar Shekau a 2021'', in ji shi.

Mai bincike kan ƙungiyar ya ce Bakura Doro ya shiga Boko Haram ne tun lokacin da ƙungiyar ta kafu, kuma da shi aka yi duka yaƙe-yaƙen ƙungiyar.

''Ya kasance makusanci kuma na hannun daman tsohon shugaban ƙungiyar Abubakar Shekau, lamarin da ya sa ma bayan mutuwar Shekau ya ƙi yin mubaya'a ga ƙungiyar ISIS duk kuwa da mabiyan Shekau da dama sun yi hakan'', a cewar Bukarti.

Ya ƙara da cewa Bakura Doro na zaune ne a wani yanki na tafkin Chadi

Abu Isa

Abu Isa shi ne mutum na biyu mafi girman muƙami a Boko Haram bayan Bakura Doro, a cewar Dokta Bulama Bukarti.

Masanin tsaron ya ce babu wasu bayanai da ke nuna cikakken asalin sunansa.

Sai dai Dokta Bukarti ya ce alamu na nuna cewa Abu na tare da Bakura Doro a cikin yankin Tafkin Chadi.

Aliyu Ngulde

Barista Bukarti ya ce wani mutum mai girman muƙami yanzu haka a ƙungiyar Boko Haram shi ne Aliyu Ngulde, wanda ke kula da ayyukan ƙungiyar a yankin Gwoza.

''Shi ke jagorantar ayyukan ƙungiyar a yankin Gwoza da tsaunukan Mandara'', in ji shi.

Dokta Bukarti ya ce ɓangaren da Ngulde ke jagoranta na mayaƙan Boko Haram shi ke da alhakin kai hare-hare kan sansanonin jami'an tsaro da fararen hula a yankin Mandara da Gwoza.

Alai Kale

Wani mutum da ake gani cikin jagororin ƙungiyar Boko Haram a yanzu shi ne Alai Kale.

Dokta Bukarti ya ce Alai Kale ne jagoran ƙungiyar Boko Haram a yankin da mayaƙan ke kira da Darul Gazwa.

''Shi ke jagorantar mayaƙan ƙungiyar da ke kai hare-hare yankunan Bama da Dikwa da kuma Konduga'', in ji mai bincike kan ayyukan ƙungiyar.

Su wane ne jagororin ISWAP?

A shekarar 2016 ƙungiyar ISWAP ta ɓalle daga Boko Haram, bayan ƙungiyar IS ta kai wa ƙungiyar goron gayyata tare da alƙawarin samun goyon baya.

Wasu daga cikin mayaƙan Boko Haram sun fice daga ciki tare da komawa ISWAP, wadda ke da bambancin aƙida da Boko Haram.

Abu Mus'ab Albarnawi - Shugaba

Cikakken sunansa shi ne Habib Muhammad Yusuf, ɗa ga mutum na farko da ya assasa ƙungiyar Boko Haram.

Dokta Bukarti ya ce Al-Barnawi matashi ne da shekarunsa ba su fi 30 ba, ''saboda lokacin da Boko Haram ta fara ƙaddamar a yaƙi da 2009 bai fi shekara 10 ba''.

Al-Barwani ya zama shugaban ISWAP a 2016 bayan ɓallewar ƙungiyar daga Boko Haram, kuma shi ne mutumin da IS ta yarda da shi tun bayan ɓallewar, a cewar Bukarti.

''Ya kasance cikin mutane na gaba-gaba da suka yi wa Shekau tawaye, lamarin da ya sa ma aka naɗa shi shugaban ISWAP'', in ji mai bincike kan ƙungiyoyin ƴanbindigar.

Sai dai wasu majiyoyi na cewa har yanzu yana nan da ransa bai mutu ba, kamar yadda Bukarti ya bayyana.

Baya ga Barnawi Bukarti ya ce akwai wasu ƙusoshin ƙungiyar da ke taimaka masa gudanar da ita da suka haɗa da Baa lam da aka fi sani da Abba Ghana da Abu Dawun da aka fi sani da Abba Ibrahim da Malam Baƙo da Bako Gorgore da Abu Ibrahim

Ya ƙara da cewa a tsarin jagorancin ISWAP ba mutum guda ne ke jagorantar ba, akwai sassa daban-daban kamar haka:

Kwamitin Shura

Dokta Audu Bulama Bukarti ya ce ƙungiyar ISWAP na da tsarin shugabanci da ya bambanta da na Boko Haram.

''ISWAP kwamitin majalisar Shura take da shi, kuma duk wani babba mai faɗa a ji a ƙungiyar na cikin wannan majalisa, wadda ita ce ƙololuwa a tsarin ƙungiyar''.

''Kuma Al-Barwnawi shi ke jagorantar wannan kwamiti, don haka ka iya cewa shi ne shugaban ISWAP'', kamar yadda Bukatri ya yi ƙarin haske.

Amirul Jaishi

Dokta Bukarti ya ce bayan kwmaitin shura a tsarin shugabancin ISWAP sai Amirul Jaishi, wanda shi ne shugaban mayaƙa.

Wannan shi ke da alhakin shiryawa tare da ƙaddamar da hare-hare a duka wuraren da ƙungiyar za ta kai hari.

Shugabannin larduna

Waɗannan su ne masu muƙamai na uku a tsarin kungiyar ISWAP, kamar yadda Bulama Bukarti ya bayyana.

''Jagororin ƙungiyar ne a yankunan da ƙungiyar ke da rassa kamar Tafkin Chadi da dajin Sambisa da Sahel'', in ji shi.

''Da wuya ƙungiyar ISWAP ta fitar da bayanai game da shugabanninta ko idan ta sauya shugaba, ba ta sanarwa saboda sukan yi ƙoƙarin sirrinta al'amuran ƙungiyar'', in ji Bukarti.

''Ko mu kanmu masu bincike galibi mukan san matsayin mutum a ƙungiyar ne ta hanyar hirarrakin da IS ke yi da su,'' in ji shi.