Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ƴanbindiga suka ƙone fadar Sarki da kashe mutane a Kwara
Al'ummar jihar Kwara a yankin Irepodun na zaman ɗarɗar sakamakon wani mummunan hari da ƴanbindiga suka kai inda suka halaka mutane da dama.
Shugabannin yankin sun ce sama da mutum 30 aka kashe a harin na ranar Talata da yanbindiga suka kai a garin Woro dauke da muggan makamai suna harbi kan mai uwa da wabi.
"An shaida muna cewa an ƙirga gawawwakin mutum 35 zuwa 45 duk da cewa ba mu tabbatar ba," kamar yadda Hon Sa'idu Baba Ahmed, ɗanmajalisar jiha da ke wakiltar yankin a jihar Kwara ya shaida wa BBC.
Ya ce ƴanbindigar sun kuma ƙona shaguna masu yawa, yayin da wasu kuma suka tsere daji da raunuka. Sai dai ya ce ba su iya kai ga tabbatar da ko ƴan bindigar sun tafi da wasu ba.
Hon Sa'idu Baba Ahmed ya ce ƴanbindigar sun ƙone fadar Sarkin Woro kuma har yanzu ba a san inda basaraken yake ba, "duk da cewa lokacin da ƴanbindigar suka kawo harin ba ya cikin fadar yana cikin gari."
"An ƙone fadarsa gabaɗaya har da shagunan da ke kusa da fadar Sarkin," in ji shi
Ya ce jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji da ke yankin sun shiga dajin bayan samun labarin harin amma babu tabbaci ko sun haɗu da ƴanbindigar da suka kawo harin.
Ko a kwanan baya ƴanbindigar sun kai hare-hare a jihar Kwara inda suka kashe mutane a Nuku da ke cikin ƙaramar hukumar Kaiama da ke makwabtaka da Woro.
Ɗanmajalisar ya ce akwai wasiƙa da ƴanbindigar suka rubutuwa sarakunan Nuku da Woro cewa za su kawo hari, matakin da ya sa aka baza sojoji.
"Amma ba su shigo ba a lokacin da aka girke sojoji, sai a ranar Talata suka shigo suka yankin," in ji shi.
Ana tunanin ƴanbindigar sun fito ne daga dajin Borgu a jihar Neja da ke makwabtaka da jihar Kwara.
Gwamnatin jihar Kwara ta fitar da sanarwa tana allawadai da harin, tare da jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe.
Babu dai wata sanarwa daga ɓangaren ƴansanda game da harin.