Ziyarar Mbappe da masu baje-koli a cikin hotunan Afirka

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kylian Mbappé ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ya ziyarci Ile Djébalé garin mahaifinsa a Jamhuriyar Kamaru
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar ƙarin kuɗin haraji a Kenya
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Litinin ne aka baje koli ƙayatattun tufafin Morocco a wani shagon dinki a Italiya.
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu yara na farin ciki da saukar dusar kankara a birnin Johannesburg na ƙasar Afirka ta Kudu ranar Litinin
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yaran da suka tsere wa rikicin wariyar launin fata a birnin Sfax na ƙasar Tunisiya, suna wasa a sansanin sojoji da ke iyakar Libiya
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Israel Adesanya na Najeriya tare da Dricus du Plessis na Afirka ta Kudu za su fafata a gasar dambe ranar Asabar a ƙasar Amurka
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Tsohon dan dambe Floyd Mayweather tare da Yan Jam`iyyar Zanu-PF a ƙasar Zimbabuwe lokacin yakin neman zaben da za a gudanar a watan Agusta
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum yana watsa ruwa jikinsa saboda tsananin yanayin zafi a Algiers babban birnin Kasar Algeria