Waɗanne ƙalubale ne ke gaban sabon shugaban hukumar zaɓen Najeriya?

Asalin hoton, @inecnigeria
Masana siyasa da masu sharhi kan al'amurran yau da kullum a Najeriya na ganin akwai manyan ƙalubale da ke gaban sabon shugaban hukumar zaben kasar, Inec, Farfesa Joash Amupitan.
A ranar Alhamis ne 23 ga watan Oktoba shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da shi a fadarsa a Abuja.
A wajen bikin rantsar da shi, Shugaba Tinubu ya buƙaci Amuputan ya yi aiki da gaskiya tare da kare tsarin zaɓe da mutuncin zabukan Najeriya da kuma ƙara ƙarfafa hukumar Inec.
Tuni sabon shugaban hukumar zaɓen ya fara aiki a sabon ofishinsa.
Wasu masana a Najeriya na ganin sabon shugaban hukumar zaben zai tunkari gaggan kalubala da suka shafi rikon shi kansa muƙamin da sabbin sauye-sauyen gudanar da ayyukan zabe da dawo da amanar jama'ar kasar game da hukumar da gudanar da zabe mai inganci.
Shugaba Tinubu ya rantsar da shi bayan Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC.
A ranar Talata 7 ga watan Oktoba ne tsohon shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu ya ajiye aikin shugabancin hukumar ta Inec, bayan karewar wa'adinsu biyu na shekaru 10.
Marigayi shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari ne ya naɗa Farfesa Mahmud Yakubu a watan Oktoban 2015 a matsayin shugaban Inec, inda ya kuma sabunta naɗin nasa a shekarar 2020.
Ƙalubalen da Amupitan zai fuskanta
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masana kimiyyar siyasa a Najeriya da suka haɗa da Farfesa Abubakar Kari na Jami'ar Abuja da dakta Ibrahim Baba Sha-tambaya, malami a jami'ar Usmani Ɗanfodio da ke Sokoto da Farfesa Tukur Abdulkadir, malami a sashen kimiyyar siyasa ta jami'ar da ke jihar Katsina sun yi bayani kan manyan ƙalubalen da sabon shugaban INEC zai fuskanta.
Farfesa Abubakar Kari na ganin akwai manyan ƙalubale uku da ke gaban sabon shugaban INEC.
Shugabancin Inec: Ita kanta kujerar shugaban hukumar zabe babban ƙalubale ne a Najeriya saboda ɗimbin aikin da ke gabansa da kuma yadda idon ƴan Najeriya zai koma kansa don ganin irin rawar da zai taka.
"Akwai tsananin ƙishirwar yin zaɓe na Allah da Annabi, wanda a Najeriya abu ne mai wuya - don haka babban ƙalubale ne a gabansa ya ba maraɗa kunya," in ji Farfesa Kari.
Farfaɗo da darajar Inec: Masanin ya ce ƙalubale na biyu shi ne farfaɗo da darajar hukumar zaɓe, saboda a cewarsa ƴan Najeriya sun yanke ƙauna da harakar zaɓe domin suna ganin da wahala a iya yin sahihin zaɓe.
"Babban ƙalubane ne gare shi ya kawar da wannan shakku wanda ya shiga cikin zukatan ƴan Najeriya," a cewar Farfesa Kari.
Sabbin dubaru: Tsohon shugaban hukumar zaɓen Najeriya ya kawo sabbin abubuwa wajen tafiyar da zaɓe musamman amfani da na'urori wadanda ake ganin sun inganta aikin zaɓen a ƙasar.
"Don haka babban ƙalubale ne a gabansa ya ci gaba da kawo sabbin dubaru da wasu hanyoyi na zamani domin magance manya da matsalolin zaɓe," in ji Farfesa Kari.
Sauran masana irinsu Dakta Ibrahim Baba Sha-tambaya da Farfaesa Tukur Abdulkadir su ma sun bayyana irin ƙalubalen da suke ganin ke gaban Farfesa Amupitan.
- Zamanantar da tsarin zaɓe: Dakta Ibrahim Baba Sha-tambaya ya bayyana cewa babban ƙalubale na farko shi ne ganin an kammala aikin zamanantar da tsarin gudanar da zaɓe a Najeriya. "Babban ƙalubale shi ne tabbatar da cewa an kammala tsarin da aka fara na watsa alƙaluman zaɓe ta intanet da kuma tattara sakamakon cikin gaskiya da gaskatawa," in ji Dr. Sha-tambaya.
- Tabbatar da adalci ga jam'iyyu da 'yan siyasa: Sha-tambaya ya ce wannan ƙalubale ne na ganin cewa ya tafiyar da hukumar zaɓen ta ƙasa ta hanyar da zai gamsar da jam'iyyu da kuma manya-manyan ƴan siyasa da masu ruwa da tsaki da ma ƴan Najeriya cewa ya yi adalci. Kuma adalcin shi ne ƴan siyasa su gamsu cewa ya yi musu.
- Gudanar da zaɓe cikin tsari ba tare da tsaiko ba: Wani babban ƙalubale, in ji masanin, shi ne yadda hukumar za ta tabbatar da cewa dukkan abubuwan da ake buƙata wajen zaɓe a shirya su tun kafin lokaci. Ya ce, akwai buƙatar a kai kayan zaɓe da wuri, a horar da ma'aikata da kuma tabbatar da cewa babu wata matsala ta jigilar kayan zaɓe ko rashin kayan aiki a ranar zaɓe.
- Ƙalubalen guje wa zargin goyon bayan jam'iyya ko gwamnati: Sha-tambaya ya ce akawai ƙalubalen tabbatar da cewa shugaban INECc ɗin ya aiwatar da aikinsa ta yadda ba za a zarge shi da yi wa gwamnati aiki ba ko kuma jam'iyya mai mulki saboda a matsayinsa na shugaban hukumar zaɓe bai kamata yana da wata alaƙa da jam'iyyun siyasa ba.
- Ƙalubalen shigar masu iko cikin tsarin shari'ar zaɓe: Farfesa Abdulkadir ya kuma yi nuni da cewa masu mulki kan yi amfani da damar su wajen ƙalubalantar sakamakon zaɓe idan bai yi musu daɗi ba. "Idan sakamakon zaɓe bai yi musu ba, sai su kai ƙara ko su ɗaukaka ƙara don tabbatar da halaccin zaɓe," in ji shi. Wannan, a cewarsa, na daga cikin manyan abubuwan da ke raunana tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya.
Waɗannan in ji masanan su ne wasu daga cikin manyan ƙalubalen da sabon shugaban INEC zai fuskanta waɗanda kuma ya kamata ya mayar da hankali a kansu domin ganin cewa wa'adin mulkinsa bai saɓa wa sauran waɗanda suka riƙe hukumar gabaninsa ba.
Wane ne Farfesa Amupitan?

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
An haifi Farfesa Amupitan ranar 25 ga watan Afrilun 1967 a garin Ayetoro Gbede da ke yankin ƙaramar hukumar Ijumu a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.
Ya yi karatunsa na furamare da sakandire a Kwara, sannan ya halarci Kwalejin Fasaha da ke Ilorin daga 1982 zuwa 1984, sannan ya zarce jami'ar Jos inda ya karanta fannin shari'a daga 1984 zuwa 1987, inda ya zama lauya a 1988.
Ya samu digirinsa na biyu a fannin shari'a a jami'ar Jos a shekarar 1993, sannan ya kammala digirinsa na uku a dai jami'ar a 2007.
Ya fara koyarwa a hukumar wallafa ta jihar Bauchi bayan kammala yi wa ƙasa hidima a shekarun 1988 zuwa 1989.
A yanzu haka shi ne mataimakin shugaban Jami'ar Jos, kuma shugaban hukumar gudanarwar jami'ar Joseph Ayo Babalola da ke jihar Osun.
A yanzu haka Farfesa ne a fannin shari'a a Jami'ar Jos da ke jihar Filatom.
A shekarar 2014 ne ya samu babban muƙamin lauyoyi na SAN










