Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me tsarin mulki ya ce kan bai wa mataimakin shugaban Najeriya riƙon ƙwarya?
'Yan Najeriya musamman ƴan siyasa da ƴan gwagwarmaya na ci gaba da cecekuce kan tafiye-tafiyen da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke yi zuwa ƙasashen waje ba tare da bai wa mataimakainsa riƙon ƙwaryar gudanar da harkokin gwamnati ba.
A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasar ya tafi "ziyarar aiki" ta mako biyu zuwa ƙasar Faransa, kamar yadda fadarsa ta bayyana cikin sanarwar tafiyar.
Sanarwar ta ce shugaban zai yi amfani ziyarar ne wajen nazarin yadda gwamnatinsa ta kasance a daidai lolacin da take dab da cika rabin wa'adi.
Fadar shugaban ƙasar ta ce Tinubu zai ci gaba da jagorantar al'amuran gwamnatinsa a yayin da yake birnin na Paris.
Ko a shekarar da ta gabata ma shugaban ƙasar ya tafi hutu ba tare da bayar da riƙon ƙwarya ga mataimakin nasa ba.
Wannan ne dalilin da ya sa wasu ƴan ƙasar ke sukar shugaban kan rashin bayar da riƙon ƙwaryar ƙasar ga mataimakinsa, suna masu kafa hujja da tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari - wanda ya sha bai wa mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo riƙon ƙwarya a lokuta da daban-daban idan zai tafi hutu.
Kan haka ne BBC ta tuntuɓi masna kundin tsarin mulkin ƙasar don jin me dokokin ƙasar suka tanadar kan bayar da riƙon ƙwarya ga mataimakin shugaban ƙasa a Najeriya.
Abin da kundin tsarin mulki ya tanada
Barrista Audu Bulama Bukarti, lauya masanin kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce sashe na 145, ƙaramin sashe na (i) na kundin tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadin cewa a duk lokacin da shugaban ƙasar zai yi tafiya, ko ba shi da lafiya ko yana cikin wani yanayin da ba zai iya shugabanci ba, to lallai ya rubuta wa majalisar dokokin ƙasar takarda domin ta amince ya miƙa wa mataimakinsa ragamar shugabancin ƙasar a matsayin riƙo.
Bukarti ya ce sashen ya kuma tanadi cewa da zarar shugabannin majalisun dokokin ƙasar biyu sun karɓi wasiƙar shugaban ƙasar, to shikenan mataimakin shugaban ƙasa ya zama shugaban riƙon ƙwarya.
''Kuma zai ci gaba da jan ragamar mulkin ƙasar har sai lokacin da shugaban ƙasar ya rubuta wa majalisun wata wasiƙar ta sanar da su dawowarsa, domin ci gaba da mulkinsa'', in ji Barista Bukarti.
Lauyan ya ƙara da cewa tanadin sashe na 145 na kundin tsarin mulkin Najeriya a yanzu ya bambanta da tanadinsa kafin 2010, ''saboda a baya dama aka bai wa shugaban ƙasa na rubuta takardar, amma a yanzu tilas ne''.
''A baya sashen bai tilasta wa shugaban ƙasa sanar da majalisa idan zai yi tafiya ba, kawai sashen ya ba shi dama ne cewa idan zai yi tafiya, ya kuma rubuta wa majalisa wasiƙa to mataimakain shugaban ƙasa ya zama shugaban riƙo'', a cewar masanin kundin tsarin mulkin.
''To amma sai aka samu mummunar illa 2010, lokacin da tsohon shugaban ƙasar, Marigayi Umaru Musa Yar'Adua ya tafi jinya, ba tare da aike wa majalisar dokokin wasiƙar sanarwa ba, daga ƙarshe kuma jinyar ta yi tsawo, ƙasa ta rikice saboda bai sanar da majalisar dokoki ba''.
''Anan ne aka samu rikicewar kundin tsarin mulki da dokoki, saboda babu shugaban ƙasa, ba kuma yadda za a yi mataimaki ya zama shugaban riƙo saboda shugaban ƙasar bai rubuta takardar da a wancan lokacin dama aka ba shi'', a cewar lauyan.
Barista Bukarti ya ce amma a 2010 sai aka yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima, aka tanadi cewa duk lokacin da shugaban ƙasa zai yi tafiya to 'tilas' ne ya rubuta wannan wasiƙa.
''A gyaran da aka yi aka yi amfani da kalmar Turanci ta ''Shall'', wadda a tsarin doka take nufin 'Tilas', indai ba wani yanayi ba ne ko ita dokar kanta ta nuna cewa ba dolen ba ce'', in ji shi.
Don haka ne lauyan ya ce a yanzu abin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada shi ne a duk lokacin da shugaban ƙasar zai yi tafiya irin wadda ya yi yanzu to tilas ne ya rubuta wa majalisar domin sanar da ita tare da bai wa mataimaki riƙon ƙwarya.
''Kuma abin da shugaba Tinubu yake yi a yanzu biris ne da tanadin kundin tsarin mulki, ko kuma bai lura da wannan sashe ba, kuma mun ga illar hakan a baya lokacin Marigayi Umaru Musa Yar'Adua'', in ji shi.
Me doka ta ce idan shugaban ƙasa bai bayar da riƙo ba?
Barista Bukarti ya ce kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi yadda za a yi idan shugaban ƙasar bai sanar da majalisar dokokin ƙasar ba.
''Sashe na 145 ƙaramin kashi (ii) ya yi tanadin cewa idan shugaban kasa ya ƙi ko ya kasa sanar da majalisa batun tafiyarsa ta hanyar aike mata da wasiƙa cikin kwana 21 da tafiyarsa, to majalisa ta zauna ta ayyana mataimakin shugaban ƙasa a matsayin shugaban ƙasa na riƙon ƙwarya'', a cewar Bukarti.
''Majalisar za ta iya yin hakan ne idan ta samu ƙaramin rinjaye (Simple majority) a majalisun ƙasar biyu''.
Ya ƙara da cewa mataimakin zai ci gaba da riƙon ƙwarya har zuwa lokacin da shugaban ƙasar zai dawo.
''Amma abin da ya sa aka samu sammatsi shi ne watakila saboda Shugaba Tinubu bai taɓa kwana 21 a wajen Najeriya ba, tunda ya zama shugaban ƙasa, amma da zai yi hakan doka ta bai wa majalisa damar tabbatar da mataimakinsa a matsayin shugaban riƙo.'' in ji shi.
Akwai 'ziyarar aiki' a kundin tsarin mulkin Najeriya?
Sai dai wani abu da magoya bayan shugaban ƙasar ke cewa shi ne tafiyar tasa ta aiki ce, kamar yadda fadarsa ta bayyana a lokacin sanarwar tafiyar.
To Amma Barista Bukarti ya ce a kundin tsarin mulkin Najeriya na yanzu babu wannan tanadin na 'ziyarar aiki', indai ba tarukan shugabanin ƙasashe ko ƙungiyoyin duniya ba.
''A baya sashen ya bai wa shugaban ƙasa dama ne idan zai iya aikin daga waje, misali ta waya ko da zoom da sauransu to babu matsala'', in ji masanin kundin tsarin mulkin.
Sai dai ya ce a gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya, a yanzu babu wannan tanadin, indai ya bar Najeriya to lallai ya bayar da dama wa shugaban riƙo.
''Inda a ce taron shugabannin ƙasashe ya tafi na kwana biyu ko uku, ko taron Majalisar Dinkin Duniya, ko ta Common Wealth da sauransu to wannan ziyarar aiki ne''.
''Amma yanzu da ya tafi Faransa ganawa zai yi da shugaban Faransa?, ko kuma yana da wata fada a Faransa''?
Ya ce kawai fadar shugaban ƙasar na amfani da kalmar 'ziyarar aiki' ne maimakon 'hutu' domin kauce wa tanadin kundin tsarin mulki.
''Amma kuma a doka ana duba asali ne ba wai sunan da aka kira abu ba, tun da dai ba taro ya tafi ba, kuma ba shi da fada a Faransa, to ai hutu ne'', in ji shi.