Me kalaman Tinubu ke nufi da ya ce babu mai juya shi?

    • Marubuci, Buhari Muhammad Fagge
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai rahoto
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Alhamis Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya fito ya kawar da duk wani shakku da jita-jita da ake yaɗawa cewa akwai wasu tsirarun jama’a masu ƙarfin faɗa a ji da ke juya shi da ake kira "Cabal" a turance.

Tinubu ya yi waɗannan kalaman ne a ƙoƙarin mayar da martani ga wasu ‘yan Najeriya da ke cewa wani gungun mutane ne ke shirya masa irin manufofin tattalin arziƙin da gwamnatinsa ke ta ɓullo da su a yanzu haka.

"Ba ni da wasu "Cabal". Babu wanda ya ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓe na. Da kuɗina da na sha wuyar rayuwata na nemi zaɓe. Da aka kai wata gaɓa, wasu sun yi ta yunƙurin daƙile ni; an rufe mani asusun bankina. Amma Allah ya ce sai na yi, ni ne zan zama shugaban Najeriya. Babu abin da ya rage mini sai bin hanyar da Allah ya nemi na bi." In ji shugaba Tinubu.

Me kalaman Tinubu ke nufi a siyasance?

Dr Abubakar Kari masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jami'ar Abuja ya ce yana yi wa kalaman na shugaba Tinubu kallo ne "a siyasance kalaman Tinubu na nufin shi jagora ne tsayayye da babu wanda yake yi masa jagoranci a rafiyarsa".

"Idan har shugaba ya yi wa kansa komai tun daga lokacin yaƙin neman zaɓe zuwa nasararsa kamar yadda Tinubu ya faɗa, to wa ake tsammanin zai juya shi ko kuma ya faɗa masa ya ji" kamar yadda Kari ya yi ƙarin haske.

Daga ƙarshe Dr Abubakar Kari ya ce "abin da yake fara sanya shugaba dogaro ga wasu shi ne rauni, na gaza bayar da abin da ake tsammani daga gare shi, ko na shugabanci ko kuma na dogaro da kai".

Me ya bambanta Tinubu da sauran shugabannin baya?

Babu abin da ya banbanta shugaba Tinubu da sauran shugabanni idan ana magana kan mutanen da suke da tasiri a gwamnatinsa.

A cewar Dakta Kari ko "wanne shugaba ba ya rasa mashawarta masu faɗa masa ya ji, don haka Tinubu bai banbanta da sauran shugabannin siyasa ba ko kuma a soji".

Ba wai shugabannin ƙasashen Afrika ba ko na nahiyar Turai ma suna da "Cabal" sai dai tasiri da irin gudunmuwar da suke bayarwa ne yake banbanta irin nasu da namu."

Kuma ai babu wanda zai ce ba shi da amini ko wanda ya yarda da shi to su ake kira "Cabal", in ji Dakta Kari.

Su wane ne masu ƙarfin faɗa a ji (Cabal)?

Masu ƙarfin faɗa a ji ko kuma "Cabal" wasu tsirarun mutane ne da suke da ƙarfin fada a ji ga shugaban da yake jagoranci da kuma madafun iko.

"Cabal" za su iya zama ma su alaƙa ta ƙud-da-ƙud da shugaba don haka sukan iya zama abokai ko 'yan uwa ko iyalai ko ƙwararru ko abokan aikinsu na baya ko kuma iyayen gidan shugaban, kamar yadda Dakta Kari ya bayyana.

Dakta Kari ya ce su Cabal "Mutane ne da ke da dangantaka ga shugaban ko ta aiki ko ta jini ko ta kasuwanci da dai sauransu.

"Suna iya canzawa da kuma juya ra'ayin mai mulki a kowanne lokaci ko kuma kan duk wata manufa ga gwamnatinsa".

Ba wajibi ba ne mambobin "Cabal" su zama ƙwararru, a kan samu amma a mafi yawan lokuta ba sa zama ƙwararru in ji Daktan.

A cewarsa kowa zai iya zama "Cabal" babu wani ma'auni da za a ce sai wani ya cika su zai zama.

Zai yiwu shugaba ya yi mulki ba tare da 'Cabal' ba?

Lokacin Olusegun Obasanjo - 1999 - 2007

Dakta Abubakar Kari ya ƙara da cewa "babu yadda za a yi mutum ya yi mulki a duniya babu "Cabal". Kuma lamarunsu a Najeriya ya fi ƙarfafa ne a jamhuriya ta huɗu wato daga 1999 zuwa yanzu".

Ya ƙara da cewa "lokacin Shuagaba Obasanjo akwai "Cabal" kashi biyu. Kashi na farko su ne waɗanda suke cikin fadar gwamnati sai kuma kashi na biyu da ke cikin jami'an gwamnati.

A lokacin Obasanjo mutane irin su Manjo Janar Abdullahi Muhammed mai ritaya wanda a buɗe take ya sha gaban kowa. Akwai irinsu Nasiru Ahmed El Rufa'i da su Ngozi Okonjo-Iweala da ma wasu da dama" in ji Dakta Kari.

Lokacin Umaru Musa Ƴar Adua - 2007 - 2009

Dakta Abubakar Kari ya ce a "wannan lokacin magana kake irin ta su Marigayi Abba Sayyadi Ruma wanda ya rike ma'aikatar noma da albarkatun ruwa.

Tanimu Yakubu Kurfi mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudi shi ma na cikinsu.

Sai kuma Abdurrahama Bello Dambazau babban hafsan sojojin ƙasa na wancan lokacin".

Lokacin Goodluck Jonathan - 2009 - 2015

A lokacin mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan, dakta Kari ya ce "A wannan lokacin akwai irin su tsohon sakataren gwamnatin kuma tsohon shugaban majalisar Dattijai Sanata Anyim Pius Anyim wanda ya yi sakataren gwamnati.

Akwai irinsu tsohon shugaban yankin Naija Dalta Edwin Clark da dai sauransu.

Reno Omokri da Reuben Abati dukkansu ana musu kallon sun taka rawa irin ta Cabal a wancan lokacin".

Lokacin Muhammadu Buhari - 2015 - 2023

"Shi ma Buhari ai ba a bar shi a baya ba, kuma kan mutane ya sake wayewa game da waɗannan mutane da ake kira "Cabal".

Akwai irin su Babban jami'in tsaro na farin kaya Lawal Daura. Akwai su marigayi Isma'il Musa Funtua da kuma marigayi Abba Kyari.

A gefe guda kuma irin su Sani Zangon Daura da kuma ɗan uwan shugaba Buhari Mamman Daura da kuma jikansa Sabi'u Tunde wanda aka zura wa ido sosai a lokacin mulkin Buharin."

Lokacin Bola Ahmed Tinubu - 2023

"Kamar yadda muka faɗa tun da fari babu shugaban da zai yi jagoranci ba tare da "Cabal" ba, ko shi Shugaba Tinubu da ya yi wannan iƙirarin akwai waɗanda muke wa kallon su ne "Cabal" ɗinsa, in ji Dakta Kari.

Ana yi wa matarsa Remi Tinubu da ɗansa Sheyi kallon suna da ƙarfi kwarai da gaske a wannan tafiya.

Akwai shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa tsohon kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila. Sai shugaban kwamitin amintattu na kamfanin mai na NNPCL Pius Akinyelure."