Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wa Tinubu ya bar wa riƙon Najeriya bayan tafiya hutu?
- Marubuci, Awwal Ahmad Janyau
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC Abuja
- Lokacin karatu: Minti 3
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai shafe tsawon mako biyu yana hutu a Ingila, amma tambayar da wasu ke yi ita ce, wa shugaban ya bar wa riƙon ƙwarya?
A ranar Laraba 2 ga watan Oktoba shugaban na Najeriya ya soma hutun mako biyu, kamar yadda fadarsa ta sanar.
“Shugaban yana da yanci ya tafi hutu - kuma ya ɗauki mako biyu daga cikin mako huɗu na hutunsa,” kamar yadda Abdul’aziz Abdul’aziz ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban ya shaida wa BBC.
Wannan ne karon farko da shugaban ya tafi hutu tun zama shugaban Najeriya a watan Mayun 2023, kodayake ya sha yin balaguro a ƙasashen waje.
Sai dai babu tabbaci ko shugaban ya sanar da majalisa buƙatarsa ta soma hutu kamar yadda sashe na 145 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadi.
Sashen ya kuma yi tanadin miƙa ragamar tafiyar da mulki ga mataimakin shugaban ƙasa a matsayin shugaban riƙo idan har shugaban ba zai iya sauke nauyin haƙƙin ofishinsa ba.
Fadar shugaban Najeriyar ta tabbatar da cewa “shugaban ya ɗauki hutun ne domin ya je ya ɗan huta ya kuma sarara don samun damar nazarin tafiyar da shugabancin Najeriya,” kamar yadda Abdul’aziz Abdul’aziz ya shaida wa BBC.
Ya kuma ce, akwai ƙa’idar miƙa mulki, kuma ba a wannan yanayin ba ne ake miƙa mulkin riƙon ƙwarya.
“Mika mulki sai idan lokacin ya zama mai tsanani ne wato idan zai shafe dogon lokaci”
“Ba wai zama zai yi a can na rashin aiki ba, zai ci gaba da yin aiki daga inda yake,” In ji shi.
Ya ƙara da cewa idan har akwai buƙata, “akwai manyan jami’an gwamnati kamar mataimakin shugaban kasa da za su ci gaba da sa ido daga dukkanin abubuwan da ke faruwa a cikin Najeriya.”
Tinubu ya yi tafiye-tafiye, inda a watan Agusta ya tafi China inda ya yada zango a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Daga nan kuma ya zarce zuwa Birtaniya kafin ya dawo Abuja.
Saɓanin wanda ya gada, tsohon shugaba Muhammadu Buhari, Shugaba Tinubu bai taɓa miƙa ragamar tafiyar da mulkin riƙon ƙwarya ga mataimakinsa ba Kashim Shettima.
Kusan sau uku Buhari yana mika ragamar mulkin rikon ƙwarya ga mataimakinsa Farfesa Osinbajo, tun bayan da suka sha rantsuwar mulki a watan Mayun 2015.
Kuma kafin miƙa mulkin riƙon ƙwarya, Buhari yakan rubuta wasiƙa ga shugabannin majalisa domin sanar da su buƙatarsa ta soma hutu, kamar yadda kundin tsarin mulki ya yi tanadi.
Osibanjo ya taɓa shafe kwana 51 a matsayin shugaban riƙo musamman a lokacin da aka shiga rashin tabbas kan lafiyar tsohon shugaba Buhari.
Amma masu sharhi na ganin Buhari bai sake ba mataimakinsa ɗana mulkin riƙon ƙwarya ba har suka gama mulki, saboda wasu matakai da ya ɗauka da suka ƙunshi sauye-sauyen muƙami na wasu jami’an gwamnati.
Masharhanta na ganin yanzu ya rage a jira a gani idan har shugaban zai dawo a wa’adin da ya ɗauka na mako biyu, idan kuma ya tsawaita hutun, tirka-tirka na iya bijirowa musamman la’akari da sashe na 145 da ya ba majalisa damar yin umarni ga mataimakin shugaban ƙasa ya gudanar da aikin ofishin shugaban ƙasa a matsayin shugaban riƙon ƙwarya har sai shugaban ya rubuto wa majalisun tarayya cewa yana nan domin ci gaba da aikinsa na shugaban ƙasa.