Abin da ya sa jakin dawa da wasu dabbobi ke da zanen fari da baƙi

Akwia dabbobi da yawa masu zanen fari da baƙi - amma masana kimiyya na ganin akwai dalilai da dama da suka jawo samunsu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai dabbobi da yawa masu zanen fari da baƙi - amma masana kimiyya na ganin akwai dalilai da dama game da hakan
Lokacin karatu: Minti 4

Daga tsuntsu aku zuwa ɗawisu, da kwaɗi, da kifi mai raoɗi-roɗi - duniyar dabbobi cike take da launuka iri-iri.

Amma wasu dabbobin sun zarta wasu shahara saboda wasu dalilai - rashin launi gaba ɗaya a jikinsu.

Akan samu dabbobi masu launin fari da baƙi a faɗin duniya, daga dazukan China zuwa Afirka.

Sai dai yayin da launukansu ka iya shan bamban, akwai dalilai masu yawa da suka jawo hakan.

Maganin ƙwari

Launin baƙi da fari zai iya hana ƙwari cizon jakin dawa, a cewar rahoton wani bincike da Jami'ar Bristol ta yi a Ingila.

Wasu jakunan dawa biyu suna tsaye a fili

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Launin fari da baƙi kan taimaka wajen hana ƙwari cizon jakunan dawa

"Babu wani takamaiman dalili da za a ce shi ne ya sa suke da launukan baƙi da fari," a cewar Dr Martin How, mai shirin zama farfesa a fannin launuka kuma ƙwararre kan ganin dabbobi, wanda kuma ya rubuta rahoton.

Ƙudaje jinsin mata kan ciji dabbobi domin shan jininsu. Masu bincike kan ce wannan zai iya zama dalilin da ya sa jakin dawa ke da zane-zanen baƙi da fari a jikinsa.

"Ƙwari ne marasa imani ko da a ce ba su ɗauke da cuta, amma idan suna ɗauke da cuta kuma suka ciji mutum a nahiyar Afirka, lamarin zai iya zama na rayuwa ko mutuwa," in ji Dr How.

"Sauraye sun fi yin amfani da ƙanshi fiye da ganinsu wajen neman abin da za su ciza...amma ƙudaje sun fi amfani da ganinsu."

Masu bincike na ganin zane-zanen baƙi da fari kan hana ƙwari cizon jakin dawa.

Yayin binciken, sun diddigin ƙwarin da ke hawa jikin dokunan da ke sanye da mayafi mai launin ruwan toka, sai suka kwatanta su da waɗanda ke hawa kan masu mayafi mai zane-zanen baƙi da fari.

Ɗaya daga cikin ƙwarin da ke cizon dabbobi da mutane, waɗanda ka iya saka musu cuta.

Asalin hoton, Gamma-Rapho via Getty Images

Bayanan hoto, Ƙwarin da ke cizon dabbobi kan saka musu cuta

Dr How ya ce ƙwarin sun sauka a mayafi mai launin toka, amma da aka sauya mayafin zuwa mai zane-zanen fari da baƙi kamar na jakin dawa, sai suka daina sauka a kan su gaba ɗaya.

"Za ku iya gane yadda suke yanke shawara, idan suka zo za su ce: 'Tsaya, ba wannan muke nema ba', sai su wuce gaba," in ji Dr How.

"Duka salon zanen da muka sauya, indai na fari da baƙi ne yana hana ƙwarin hawa jikin mayafin."

Dr How ya ce ƙwari "na da matsala wajen gani", wanda ka iya zama dalili na ruɗewarsu.

"Idan suka taho abin da suke gani daga nesa kawia shi ne dusu-dusu, idan kuma suka matso kusa da kamar mita biyu sai su fara ganin fari da baƙin," a cewarsa.

"Sukan sauya daga ganin dusu-dusu zuwa ganin wani abu mai zane-zane, kuma ina ganin wannan ne ke janye hankalin ƙwarin daga kan dabbobin."

Sajewa

Duk da cewa ana ganin launin baƙi da fari ba zai taimaka wa jaikn dawa wajen ɓatar da kamarsa ba, ana ganin zai taimaka wa sauran dabbobi kamar panda, wadda zane-zanenta ke taimakawa wajen kare ta daga muggan namun daji kamar damisa.

"A dazukan yammacin China, akwai dusar ƙanƙara da duwatsu masu baƙi da fari, da kuma manyan bishiyoyi a wasu lokutan na shekara," kamar yadda Farfesa Tim Caro, ƙwararre kan launuka a Jami'ar Bristol, ya bayyana.

"Idan aka hangi wata dabba maras tafiya da sauri kamar panda daga nisan mita 50 ko 100, da wuya a iya tantance ta a cikin ƙanƙara, ko duwatsun da aka hange ta."

Launin dabbar panda kan taimaka mata sajewa da wurin da take a ciki ƙanƙara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Launin dabbar panda kan taimaka mata sajewa da wurin da take a ciki ƙanƙara

Ankararwa

Samun launin baƙi da fari zai iya zama wata hanya ta ankarar da sauran dabbobi, da haɗin kansu, a cewar Farfesa Caro - misali a jelarsu mai kama da zobe.

Dabbar lemur

Asalin hoton, Getty Images

Dabbobin kansu masu haske ne, amma suna da layuka a jelarsu masu baƙi da fari da suke ɗagawa sama idan suna tafiya.

"Abin da muke tunani shi ne, saboda suna ɗaga jelar idan suna tafiya a cikin rukuni, muna ganin alama ce da ke cewa: 'Ga ni nan, ku biyo ni'," in ji shi.

Akwai irn wannan misalin a ɓangaren damisa, saboda ɓalli-ɓallin fari a bayan kunnuwan damisa.

Ba abu ne a fili ba

Dabbobin pengiun biyu na'uin gentoo suna tsaye

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Babu wata tabbatacciyar amsa

Akwai wasu tunanin game da layukan fari da baƙi.

A jikin dabbar pengiun nau'in gentoo, baya ga sajewa, baƙin gashin da ke jikin fukafukinsu na ɗauke da launin da ake kira melanin, wanda ke ba su kariya, a cewar Dr Rowland.

Launukan daban-daban kan taimaka musu wajen daidaita zafin jikinsu.

"Wurare masu duhu kan taimaka wajen zuƙe zafi da sauri fiye da fararen wurare," in ji ta.

"Dabbobin Pengin na yawan juya bayansu ga rana, ko kuma su juya cikinsu ga haske idan gari ya yi zafi."

Amma dai ba mu da tabbas gaskiya.

"Wani zubin abubuwan kan hadu wuri guda," in ji Dr Rowland.

"Kimiyya ba ta taɓa fito da wata takamaimiyar amsa ba."