Michelle O'Neill ta kafa tarihin zama shugabar Northern Ireland ta farko

Michelle O'Neill

Asalin hoton, GETTY/CHARLES MCQUILLAN

Tsibirin Northern Ireland ya samu shugaba ta farko a tarihi.

Da take karbar mukamin, Michelle O'Neill ta shaidawa ’yan majalisa cewa iyayenta za su yi mamaki mace mai irin aƙidun ta ce za ta rike wannan muƙami.

Sabuwar shugabar ta buƙaci ƴan siyasa su jingine banbancin da ke tsakanin su domin aiki tare wajen kawo ci gaba.

Ta zamo ƴar asalin Northern Ireland ta farko da ta riƙe wannan matsayi tun bayan kafa tsibirin fiye da ƙarni guda da ya gabata.

Da ta ke jawabi a zauren majalisar dokoki, Ms O’Neill ta ce za ta mutumta duk wani ɗan ƙasa, ba tare da nuna wariya ko babanci ba.

Ta ce "A yau an buɗe sabon babi na tabbatar da makomar mu nan gaba. Ina alfahari da tsayuwa nan a matsayin shugabar ku. Muna murnar tabbatar wani yanayi na bayar da ƴanci da adalci ga kowa, domin aiki tare domin bunƙasa tare. Iana da yaƙinin cewa duk da abubuwan da suka faru a baya, a tare, za mu iya gyara makomar mu."

Ta ce yanzu dai abin da jama’a ke buƙata shi ne haɗin kan ƴan siyasa wajen aiki tare da kawo ci gaba.

Jam’iyyar Ms O’Neill tana fatan haɗe tsibirin da jamhuriyar Ireland a nan gaba.

Za ta yi aiki tare da masu fafutukar ganin tsibirin Northern Ireland ya ci gaba da zama a cikin Birtaniya.

Jam’iyyarta ta DUP ta ƙauracewa gwamnati shekara biyu baya, lokacin dambarwar da ta biyo bayan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, lamarin da ya shafi safarar kayayyaki a tsakanin ƙasashen yankin.

Amma jam’iyyar ta sake dawowa bayan ƙulla wata yarjejeniya da gwamnatin, wadda ta ƙumshi tafiyar da mulkin haɗin gwiwa da rabon muƙamai a tsakanin jam’iyyu.

A bisa sabuwar yarjejeniyar dai, dole ne gwamnati ta shigar da kowanne ɓangare a cikin tsare-tsaren tafiyar da mulki.