Fashewar gas a Nairobi ta kashe mutum uku da jikkata kusan 300
Mutum uku aka tabbatar da mutuwarsu yayin da sama da 300 suka jikkata sakamakon wata mummunar fashewar gas ɗin girki a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya.
Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ya ce wata babbar mota ce ɗauke da tukwanen gas ta fashe a unguwar Embakasi a daren jiya, lamarin da ya haddasa tashin gobara a yankin.
Hotunan bidiyon a kafafen sada zumunta sun nuna yadda wuta da hayaƙi suka turnuƙe saman rukunin benaye yayin da mutane suka shiga firgici da ruɗani domin neman tsira.
Gidaje da kasuwanni, da shaguna da motoci dama ne suka ƙone sakamakon tashin gobarar.
Tun da farko, gwamnatin ƙasar ta ce fashewar ta auku ne a cibiyar sayar da gas ɗin, sai dai kawo yanzu ba a san abin da haddasa fashewar ba.
Mazauna yankin Embakasi da ke kudu maso gabashin Nairobi sun ce sun ji kamar girgiza kafin ganin haske a sama a tsakar dare.
Wani mazauni yankin wanda ya ce a gabansa fashewar ta auku Boniface Sifuna ya ce ta ƙyar ya tsira duk da ya samu ƙuna a jikinsa.
Haka kuma wani ƙarin shaidar ya ce mutane sun razana tare da kaɗuwa sakamakon aukuwar fashewar.
Da yawa daga cikin waɗanda suka jikkata an ce sun shaƙi hayaƙi ne, ciki har da ƙananan yara 25, kamar tadda wata kafar yaɗa labarai a ƙasar ta ruwaito.
Shugaban 'yan sandan yankin Embakasi, Wesley Kimeto ya ce daga cikin waɗanda suka mutu har da wani ƙaramin yaro, yana mai gargaɗin cewa adadin waɗanda suka mutun ka iya ƙaruwa.
Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta ce ta kai mutum 271 da suka samu munanan raunuka zuwa babban asibitin ƙasar da ke Nairobi.

Asalin hoton, Reuters
Wani ɗan jarida da ke zaune a yankin ya ce mutanen yankin sun fice daga gidajensu bayan fashewar.
Ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta wallafa a shafinta na sada zumunta cewa jami'anta na wurin da abin ya faru, inda suke aiki ba dare ba rana domin taimakawa wajen kashe wutar.

Asalin hoton, AFP
Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar Mista Mwaura ya ce jami'ai sun killace wurin da abin ya faru domin tabbatar da aikin ceto.
Ya kuma yi kira ga mutane da su guje wa zuwa wurin, domin samun sauƙin gudanar da aikin ceton cikin nasara, ba tare da tangarɗa ba.













