An rage tsawon hukuncin ɗauri da aka yanke wa tsohon firaministan Malaysia

Tsohon Firaministan Malaysia Najib Razak

Asalin hoton, REUTERS

Bayanan hoto, Tsohon Firaministan Malaysia Najib Razak

An rage tsawon lokacin da Mr Najib Razaq zai shafe a gidan yari daga shekara 12 zuwa shekara shida.

Sannan an rage yawan tarar da aka ci shi, daga dala miliyan 40 zuwa dala miliyan 10.

Hukumar yi wa jama’a afuwa karkashin jagorancin Sarkin Malaysia ce ta yi masa wannan sassaucin.

Koda yake hukumar ba ta yi ƙarin bayani kan abin da ya sa ta dauki wannan matakin ba, amma dai Mr Najib da sauran abokan tafiyarsa na siyasa sun daɗe suna kamun kafa kan a sako shi daga gidan yari.

Shari’ar da aka yi wa tsohon firaiministan na da nasaba da sace dala biliyan hudu daga wani asusun gwamnati da ya kafa lokacin yana kan Mulki.

Diyar Najib, watau Nooryana Najwa Najib ta ce iyalansa sun ji dadin rage tsawon shekarun da zai shafe a kurkuku amma kuma sun ji takaicin cewa ba afuwa ba ce gaba ɗaya da za ta sa ya samu walwalar ƴanci.

Rage yawan shekarun da Mr Najib zai yi a gidan yari na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin Firaiminista na yanzu Anwar Ibrahim da lashe amansa kan batun yaki da rashawa tun bayan da aka soma yin afuwa ga ƴan jam’iyyarsu da ake zargi da cin hanci da rashawa.

Anwar Ibrahim ya dade yana kurarin yaƙi da rashawa amma tun bayan da ya hada hannu da jam’iyyarsu Najib Ibrahim domin kafa gwamnatin hadin kai a watan Nuwamban 2022 maganar ta soma bin shanun sarki.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kawo yanzu ofishin firaiministan bai mayar da martini ba.

A yanzu dole ne Mista Najib ya biya sabon tarar kafin a sake shi cikin watan Agustan 2028.

Idan kuwa ya kasa biyan tarar, za a tsawaita wa'adin zaman nasa a gidan yarin zuwa 2029.

A shekarar 2020 ne kotu ta same shi da laifi, bayan ya shafe kusan shekara biyu yana ɗaukaka ƙara don guje wa samunsa da laifi.

Rage adadin shekarun da tsohon firaministan zai yi, alama ce da ke nuna cewa shugabanni a yankin kudu maso gabashin Asiya na da wata alfarma har bayan kammala mulkinsu, kamar yadda Farfsea James Chin na jami'ar Tasmania ya bayyana.

"Hakan na nufin idan ka kai wani matsayi, babu abin da zai faru da kai,'' in ji Farfesa Chin.

Jam'iyyar UMNO ta mista Najib - wadda a baya ta jagoranci gwamnatin haɗin kan Malaysia - ta yi ta kiraye-kirayen neman afuwar sarkin ƙasar, bayan duka hanyoyin ɗaukaka ƙara sun ƙure masa.

Ko a makonni biyu da suka gabata ma dai jami'an kula da gidajen yarin ƙasar sun yi wa mista Najib rakiya zuwa wata kotu a Kuala Lumpur babban birnin ƙasar inda aka saurari ƙarar da ya ɗaukaka.

Haka kuma Najib tare da matarsa Rosmah Mansor, na fuskantar wasu ƙararraki a kotu, kan wasu zarge-zargen daban da ake yi musu.