Mene ne bambancin kawar da al'umma da kisan-kiyashi?

 Shugaba Trump na tarbar Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a White House, ranar 04 ga watan Fabarairu na 2025

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Trump ya rubuta a shafinsa na sada zumunta da muhawara cewa Isra'ila za ta ba wa Amurka Gaza bayan yaƙi
    • Marubuci, Tom Santorelli
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Maganar da Donald Trump ya yi cewa Amurka za ta karɓi iko da Gaza ta sake tsugunar da al'ummar Zirin a wasu ƙasashe ta janyo zargin cewa yana neman share al'ummar, kuma hakan ya janyo suka daga Majalisar Ɗinkin Duniya, da ƙasashen Larabawa da sauran shugabannin duniya da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'Adam

Trump ya yi kalamana ne a fadar gwamnatin Amurka a lokacin wani taron manema labarai a ranar Talata, lokaci da yake tare da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.

Yayin da Netanyahu ya ce tunanin abin da ya dace a duba ne shi kuwa mataimakin babban sakataren ƙungiyar ƙasashen Larabawa, Hossam Zaki, ya gaya wa BBC cewa raba mutum miliyan biyu da muhallinsu laifi ne na cin zarafin al'umma.

"Wannan tunani ne da ke neman tabbatar da share al'umma - tilasta fitar da mutane farar hula daga ƙasarsu. Dukkanin waɗannan Falasɗinawan da ke cike da alfahari da ƙwarin guiwa da aka ga suna tururuwa suna komawa kofayin da a da ke zaman gidajensu, bayan cimma yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta. Ta yaya za ka ma iya tunanin cewa za su yadda a fitar da su daga ƙasarsu?'' Ya ce.

To amma wannan shawara ta shirin da Trump ya ambata da yake nuni da cewa za a sauya wa mutanen wani muhalli da yake nesa da inda suke amma cikin zaman lafiya da kuma kyakkyawan muhalli fiye da wanda aka raba su da shi, zai iya kasancewa share al'umma? Kuma ta yaya share al'umma ya bambanta da kisan kiyashi?

Falasɗinawa da aka raba da gidajensu na komawa arewacin Gaza

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Falasɗinawa da aka raba da gidajensu na komawa arewacin Gaza

Me kawar da al'umma ke nufi?

A taƙaice share al'umma na nufin korar wata al'umma daga wani waje.

Wannan zai iya kasancewa ta fitar da su daga ƙasa ko tilasta sauya musu matsuguni da nufin ganin wata al'umma ko ƙabila ɗaya ce kawai a wajen da aka tashi mutanen.

Farfesa George Andreopoulos, darektan farko na Cibiyar Kare Haƙƙin Ɗan'Adam a Kwalejin John Jay da ke New York, ya ce abin ya wuce maganar sauya wa wata ƙabila muhalli - akwai magar kawar da duk wasu abubuwa nasu masu muhimmanci kama daga lalata gineginensu na tarihi da maƙabartu da wuraren ibada".

Kalmar ta fara fice ne ta yi suna a shekarun 1990 lokacin da rikicin ƙabilanci ya ɓarke a lokacin rugujewar Jamhuriyar Tarayyar Yugoslavia.

A wannan lokaci 'yansiyasa da kafafen yaɗa labarai sun riƙa amfani da kalmar wajen bayyana irin aƙubar da aka riƙa gana wa al'ummar Musulmi a Bosnia da Herzegovina, da Serbiyawa a yankin Krajina na Kuroshiya, da Albaniyawa da kuma Serbiyawa a Kosovo.

Haka kuma tsohon shugaban hukumar kare haƙƙin ɗan'Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya Zeid Raad Al Hussein ya yi amfani da kalmar a 2017, inda ya bayyana matakin da gwamnatin jihar Rakhine ta Myanmar ke ɗauka na korar Musulmai 'yan ƙabilar Rohingya a matsayin babban misali na share ko kawar da al'umma.

Wata uwa 'yar ƙabilar Rohingya ɗauke da jaririyarta a sansanin gudun hijira na Kutubpalang, Ukhiya Cox a gunmdumar Bazar a Bangladesh, ranar 24 ga Agustan 2022.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A watan Agusta na 2017, wani gagarumin tashin hankali ya tilasta wa sama da Musulmi ƙabilar Rohingya 742,000 tserewa daga gidajensu zuwa maƙwabciyar ƙasar Bangladesh

Shin kawar da al'umma laifin yaƙi ne?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kalmar ta yaɗu saboda yanayin rikice-rikicen da ake yi da makamai a wannan zamanin.

Ƙwararrun hukumar sun ce akwai matakai na gallazawa da tilastawa da za a iya amfani da su wajen shawo kan al'umma su tashi wanda hakan zai sa sojin ƙasa su gaggauta miƙa wuya.

Waɗannan matakai sun haɗa da azabtarwa, da kame ko tsarewa da fyaɗe da cin zarafi ta lalata da ɓarnata ko lalata gida ko dukiya da fashi da kuma kai hare-hare kan wuraren kula da lafiya.

Wasu daga cikin waɗannan abubuwa laifuka na yaƙi a zahiri, amma kuma wannan mataki na kawar da al'umma ba a ayyana shi kuma ba a bayyana shi a matsayin laifin yaƙi a ƙarƙashin dokokin duniya ba in ji Majalisar Ɗinkin Duniya.

Jami'ar bincke kan kare haƙƙin ɗan'Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya a yankunan Falasɗinawa da Isra'ila ta mamaye, Francesca Albanese, ta ce Isra'ila ta daɗe tsawon shekara da shekaru tana ƙoƙarin kawar da tarin Falasɗinawa da sunan yaƙi.

"Akwai babban haɗarin da muke gani yanzu na yuwuwar ganin maimaicin mamaya da korar Falasɗinawa da mamaye yankinsu da Isra'ila ta yi a 1948, jami'ar ta ce, inda take nuni da matakin da aka yi amfani da shi a 1947-1949 lokacin da Isra'ila ta kori Falasɗinawa sama da 75,000 daga gidajensu da filayensu a rikicin da ya kai ga kafa ƙasar Isra'ila.

Mene ne bambancin kawar da al'umma da kuma kisan-kiyashi?

Yayin da zuwa yanzu ba a ayyana kawar da al'umma a matsayin laifi mai zaman kansa ba a ƙarƙashin dokokin duniya, kisan kiyashi kuwa laifi ne.

A shekara ta 1946, babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya ya ayyana shi a matsayin laifi, sakamakon manufofin Nazi na kisan Yahudawa.

An fassara shi a matsayin duk wani abu da aka yi na niyyar lalata wani bangare ko gaba ɗaya wata tarayya ko haɗaka ta ƙasa ko ta ƙabila ko kuma ta addini.

Waɗannan abubuwa sun haɗa da kisa ko haddasa mummunan rauni ko cutarwa ga wasu mutane, wanda hakan zai iya kawo ƙarshen mutanen, da hana sabuwar haihuwa a cikin wata al'umma ko kuma a ƙwace wasu yara daga ƙabilar a kai su wajen wata ƙabilar ko al'umma.

Tsohon Firaministan Rwanda Jean Kambanda a lokacin shari'arsa a kotun duniya a Hague

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya a kan Rwanda ita ce ta farko da ta yi hukunci a kan laifin kisan-kiyashi

Tsohon Firaministan Rwanda Jean Kambanda, ya kasance wani shugaban gwamnati na farko da aka yanke wa hukunci kan laifin kisan-kiyashi da kotun duniya ta yi a 1998 a kan rawar da ya taka a kisan 'yan Tutsi miliyan ɗaya da kuma 'yan Hutu masu matsakaicin ra'ayi shekara hudu kafin nan.

Maganar aikata laifin da niyya

To amma kuma fassarar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta kuma ƙunshi abin da ta kira niyyar lalata haɗakar ko al'ummar ta ƙasa ko ƙabila ko kuma mabiya wani addini.

Wannan niyya ko ƙuduri shi ne babban banbancin da ke tsakanin kawar da al'umma da kuma kisan-kiyashi.

Yayin da lalata ko ganin bayan wata al'umma ko ƙabila ko mabiya addini shi ne ainahin ƙudurin kisan-kiyashi, babban dalilin kawar da al'umma kuwa shi ne korarsu da kuma niyyar wata ƙasa mai ƙabila ko al'umma ɗaya.