Dalilai uku da ke haifar da ƙaruwar hare-haren ƴanbindiga a Kano

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf zaune a kan kujera

Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/Facebook

Bayanan hoto, A baya-bayan nan jihar Kano ta riƙa fuskantar hare-haren ƴanbindiga
Lokacin karatu: Minti 5

A farkon makon nan ne wasu ƴanbingida suka far wa ƙauyen Faruruwa da ke yankin ƙaramar hukumar Shanono a jihar Kano, inda suka yi garkuwa da wasu mata biyar ciki har da masu shayarwa.

Bayanai daga yankin sun ce ƴanbindigar ɗauke da miyagun makamai sun auka ƙauyen ne da tsakar dare, inda suka riƙa bi gida-gida kafin daga bisani su yi awon gaba da matan.

Ko a makon da ya gabata ma sai da jami'an tsaro suka samu nasarar hallaka wasu ƴanbindiga da suka kai hari ƙaramar hukumar Shanono.

Jihar Kano - wadda ta fi kowacce jiha yawan al'umma a Najeriya - na daga cikin johohin arewacin ƙasar da ba a sani da matsalar ƴanbindiga masu garkuwa da mutane ba.

To amma a baya-baya jihar ta riƙa fuskantar hare-hare musamman a yankunan jihar da suka yi iyaka da jihar Katsina mai fama da matsalar tsaro.

Wasu mazauna yankunan sun yi zargin cewa ƴanbindigar daga jihar Katsina kan tsallako jihar sakamakon sulhun da wasu al'umomin Katsina suka yi da su.

Girman matslar tsaro a Kano

Dakta Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Security mai nazarin tsaro a ƙasashen yankin Sahel ya ce matsalar tsaro a jihar Kano ta fara girman da ya kamata gwamnati ta mayar da hankali domin magance ta.

Masanin tsaron ya ce duka ƙauyukan da ke da iyaka da jihohin Katsina da Kaduna na cikin barazanar hare-haren ƴanbindiga.

''Haka ma ƙauyukan da suka yi iyaka da dazukan Falgore da sauran dazukan da suka ratsa Kano da Katsina na cikin barazanar''.

Masanin tsaron ya ce kodayake kawo yanzu kamfaninsa ba shi da ƙididdigar adadin hare-haren da aka kai Kano, amma dai ya tabbatar da samun ƙaruwar hare-haren a baya-bayan nan.

Me ya janyo matsalar tsaro a Kano?

Wasu ƴanbindiga riƙe da muggan makamai

Asalin hoton, Daily Trust

Bayanan hoto, Wasu na ganin yin sulhu da ƴanbindiga a Katsina na daga cikin abubuwan da suka haifar da matsalar
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dokta Kabiru Adamu ya ce akwai abubuwa kamar guda uku da suka haddasa samun matsalar ɓullar ƴanbindiga a jihar Kano.

  • Matsin lambar Jami'an tsaro a makwabtan jihohi

Masanin tsaron ya ce ɗaya daga cikin matsalolin da suka haifar da matsalar tsaro a jihar Kano shi ne yadda jami'an tsaro suka matsa wa ƴanbindigar da hare-hare musamman a jihar Katsina mai makwabtaka.

''Akwai matakan tsaro masu yawa da jami'an tsaro ke ɗauka a jihar Katsina, wanda kuma babu irin hakan a jihar Kano, saboda ƙarancin matsalar a jihar, wannan ya sa ƴanbindigar suka karkata zuwa Kano, inda babu irin waɗancan matakan sosai'', in ji shi.

  • Sulhu da ƴanbindiga a Katsina

Wani abu da ya ƙara janyo samun hare-haren ƴanbindiga a jihar Kano shi ne yadda wasu al'umomin Katsina mai makwabtaka ke yin sulhu da ƴanbindigar domin samun zaman lafiya, a cewar Shugaban Kamfanin na Beacon Security.

Al'umomi a ƙananan jhukumomi da dama a jihar Katsina sun yi sulhu da ƴanbindiga, lamarin da ya sa ƴanbindigar suka dakatar da hare-hare a yankunan da aka yi sulhun.

"A iya ƙididdigar da muka yi akwai ƙananan hukumomi 17 a jihar Katsina da suka yi sulhu da ƴanbindiga da ke addabarsu da hare-hare'', in ji Kabiru Adamu.

''To ka ga kenan wuraren da suka kai wa hare-hare sun ragu matuƙa, kuma tun da suna riƙe da makamai, dole su nemi wasu wurare da za su riƙa kai hare-hare, tun da sulhun bai tanadi karɓe makamansu ko sauya musu tunani ba'', in ji shi.

Dama dai masana tsaro sun sha yin gargaɗi game da illolin yin sulhu da ƴanbindiga ba tare da karbe makaman da suke amfani da su ba.

  • Sauƙin kai hari

Kabiru Adamu ya ce a ilimin kimiyyar tsaro, akwai abubuwa guda uku da ke sa ƴanbindiga su ƙaddamar da hare-hare a wuri, na farko shi ne mai aikata laifin yana kan bakarsa na ci gaba da aikatawa, na biyu zai duba ribarsa idan ya kai, sai kuma sauƙin ƙaddamar da harin.

''To idan ka duba duka waɗannan abubuwa sun haɗe a Kano, ga ƙauyuka nan babu jami'an tsaro, sannan ga shi kuma za su samu riba idan suka kai'', in ji matsanin tsaron.

Me ya kamata hukumomi su yi?

Wasu jami'an tsaro

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban kamfanin mai nazarin tsaro ya ce galibi jihohin Najeriya suna da sakaci wajen ɗaukar ingantattun matakan tsaro na zamani.

''Yana da kyau gwamnati ta ɓullo da wasu hanyoyi da mazauna ƙauyuka za su samu damar sanar da jami'an tsaro idan suna cikin barazana, su kuma jami'an tsaro su gaggauta kai ɗauki'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa yana da kyau gwamnatin jihar Kano ta tashi tsaye wajen inganta harkokin tsaron jihar, ta hanyoyin zamani.

''Kano na da ƙananan hukukomi 44 da dubban ƙauyuka, to ya kamata gwamnatin jihar ta samu wani ƙauye mai nisa ta yi gwajin hanyoyin zamani na isar da saƙo, a kuma ga minti nawa zai ɗauki jami'an tsaro kafin su kai ga ƙauyen domin bayar da agaji,'' in ji shi.

Me ya kamata mazauna yankunan su yi?

Matsalar tsaro matsala ce da ta shafi kowa da kowa, haka kuma masana na ganin dole sai kowa ya bayar da gudunmawa domin magance ta.

Kan haka ne Dokta Kabiru Adamu ya ce su ma mazauna waɗannan ƙauyuka akwai irin rawar da za su taka domin daƙile matsalar.

Ya kuma zayyana wasu matakai uku da ya ce ya kamata su ɗauka domin taimakawa:

  • Tsananta kiraye-kiraye ga wakilansu a siyasa

Babban matakin da ya kamata mazauna yankunan su ɗauka shi ne tsananta kiraye-kiraye ga jagororinsu na siyasa.

''Su yawaita kiran kai musu ɗauki daga jagororin siyasar yankin, hakan zai sa su tuna da haƙkin da ke kansu domin su gaggauta yin gyara'', in ji shi.

  • Fallasa ƴanbindigar

Wani mataki da ya kamata mazauna yankin su ɗauka shi ne su riƙa fallasa irin waɗannan ƴanbindigar, a cewar Dokta Kabiru Adamu.

''Su ma waɗannan ƴanbindigar galibi ana zaune da su ne a wuri guda, don haka yana da kyau su ɗauki matakin bayar da bayanan da za su taimaka wajen kama su'', in ji shi.

  • Tsananta sanya idanu

Dokta Kabiru Adamu ya ce akwai kuma buƙatar mazauna waɗannan wurare su tsananta sanya idanu domin lura da yankunansu.

''Hausawa na cewa idan kiɗa ya canja to dole rawa ma ta canja, don haka idan a baya mutane sun sake, suna gudanar da al'amuransu cikin kwanciyar hankali, to ya kamata yanzu su kula da kyau su ƙara lura'', in ji shi.

  • Kafa ƙungiyoyin ƴan sa kai

Shugaban Kamfanin na Beacon Security ya kuma ce yana da kyau mutanen waɗannan yankuna su riƙa kafa ƙungiyoyin ƴan sa kai, da za su riƙa taimakawa wajen kare al'umomi.

Sai dai ya ce ire-iren waɗannan ƙungiyoyi suna buƙatar tallafi da taimakon jami'an tsaro domin gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa.

''Galibi za ka ga waɗannan ƴan sa kan ba ma wasu makaman kirki suke riƙewa ba, da za su iya tunkakar ƴanbindigar, amma dai gwargwado san idanunsu na taimaka wa jami'an tsaro'', in ji shi.