Yadda 'yanbindiga daga Katsina ke tsallakawa suna kai hare-hare a Kano

Wani mutum riƙe da bindiga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Katsina mai maƙwabtaka da jihar Kano na fuskantar hare-haren 'yanbindiga kusan kullum
Lokacin karatu: Minti 3

Mazauna yankin ƙaramar hukumar Shanono da ke jihar Kano sun koka game da yadda 'yanbindiga ke kai musu hare-hare tare da sace mutane da dabbobinsu.

A ranar Alhamis ne wata ƙungiyar mazauna ta yi taron manema labarai domin shaida wa duniya yadda suka ce 'yanbindigar na tsallakawa daga Katsina domin kai musu hare-hare.

Yayin taron manema labaran a ranar Alhamis, shugaban al'ummar Farin-Ruwa Alhaji Yahaya Bagobiri ya nemi gwamnatin taayya da ta jihar su kawo musu ɗauki.

"Muna neman Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf su kawo mana ɗauki saboda tuni wasu mazauna yankin suka fara barin gidajensu zuwa birnin Kano da maƙwabtan garuruwa," in ji shi.

Bagobiri ya ce wasu hare-hare da 'yanfashin suka kai musu ranar Talata da Laraba sun yi sanadiyyar raunata mutane da kuma sace shanu da dama.

Shanono da ke arewa maso yammacin jihar, na da nisan kilomita 85 daga ƙwaryar birnin Kano, kuma ta yi maƙwabtaka da ƙananan hukumomin Kankiya da Musawa da Danja na jihar Katsina waɗanda ke fama da hare-haren 'yanfashin dajin.

Ba a fiya samun rahotonnin hare-haren 'yanfashin daji a Kano ba. Sai dai jihohin Kaduna da Katsina masu maƙwabtaka na fama da hare-haren.

Garuruwan da 'yanfashin suka addaba

Yahaya Bagobiri ya ce garuruwan da 'yanfashin suka fi kai wa hari sun haɗa da Farin-Ruwa, da Kuraku, da Gorantuse, da Saure, da kuma Shadu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Hatta a jiya da shekaran jiya [Talata da Laraba], 'yanfashi sun sake kawo hari inda suka raunata mutane kuma suka sace shanu fiye da 40, ban da sauran dabbobi da dukiyoyi," a cewarsa.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya faɗa wa BBC cewa an shafe kusan wata biyu zuwa uku suna fuskantar irin waɗannan hare-hare.

"Zuwa yanzu sun kawo hare-hare kusan sau bakwai ko takwas," a cewarsa. "Ba zan iya lissafa irin asarar dukiyar da muka yi ba zuwa yanzu."

Ya ƙara da cewa duk lokacin da suka kai hari sai sun tafi da dabbobi.

"Ko a harin kwana biyun nan sun sace garke-garke na shanu. Ana ƙiyasta shanun da suka sace za su kai 800 zuwa 1,000.

"Wannan karon da suka zo ba su ɗauki mutane ba, amma sun harbi wasu. A baya kuma, sun sha harbin mutane a kasuwar garinmu ta Farin-Ruwa."

Mutumin ya ce har yanzu ba su san dalilin da ya sa 'yanfashin ke kai musu hare-hare ba, amma suna hasashe.

"Muna tunanin kawai saboda arzikin dabbobi da muke da shi ne ya sa suka addabe mu. A da sai dai kawai mu ji labarai," kamar yadda ya bayyana.