Ƴanbindiga sun kai hari yankin Birnin Gwari duk da an yi sulhu

Yankin Birnin Gwari

Asalin hoton, Bashir Kutemeshi

Lokacin karatu: Minti 2

Wasu ƴanbindiga sun kai wani sabon hari a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna a arewacin Najeriya duk da sulhun da aka yi a yankin.

Ƴanbindigar sun ƙaddamar da harin ne a garin Kuyallo da ke yankin Birnin Gwari jihar Kaduna, wanda ya yi sanadin asarar rayuka.

Mazauna yankin sun ce mutum tara aka kashe a harin, wasu kuma suka tsira da munanan raunuka.

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta tabbatar da harin amma ta ce mutum bakwai aka kashe, mutum biyar kuma suka ji rauni, kamar yadda DSP Mansir Hassan, jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Kaduna ya shaida wa BBC.

Kusan shekara guda kenan da aka yi sulhu tsakanin jama'ar yankin Birnin Gwari da 'yanbindiga, al'amarin da ake ganin ya kai ga samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Kwatsam sai ga labari, cewa an kai wani hari a garin Kuyello, abin da Dayyabu Haruna Baban Abba, mai bincike da tattara bayanai kan harkar 'yanfashin daji a yankin Birnin Gwari da wasu garuruwa makwabta, ya ce ya samo asali ne daga wani sabani tsakanin Fulani makiyaya da kuma masu haƙar zinari a dajin da ke yankin.

"Wani ɗanbindiga ne ya addabi masu haƙar zinari a kan hanya yana tare su yana masu fashi, har ta kai ga faɗan da ya yi ajalinsa."

"Wannan ne kuma ya harzuka wasu 'yan'uwan marigayin, har suka kai farmaki garin Kuyello," a cewar Dayyabu Haruna.

Ya ce mutum tara aka kashe da kuma jikkata wasu mutum tara a harin da ƴanbindigar suka kawo.

Sai dai ya ce waɗanda suka kawo harin an tabbatar da ba waɗanda aka yi sulhu da su ba ne, wasu ne daga jihar Katsina suka tsallako yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna.

DSP Mansir Hassan ya ce jami'an ƴansanda sun yi artabu da maharan bayan samun labarin harin tare da cewa an tura ƙarin jami'an tsaro a yankin.

Yanzu haka dai ana nan cike da fatan matakan da ake dauka za su ci gaba da samar da kandagarki, don magance sake aukuwar irin harin da aka kai garin Kuyello.