Yadda ƴansanda suka kama wasu da suke zargin ƴanbindiga ne a Kano

Kwamishinan yansandan Kano CP Ibrahim Adamu Bakori

Asalin hoton, @KanoPoliceNG

Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar yansandan jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta yi nasarar kama wasu da take zargin yanbindiga ne masu satar mutane domin kudin fansa.

Rundunar yansandan ta ce ta kama mutum biyu a ranar Asabar a yankin Shanono bayan samun bayanan sirri.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa Jami'in hulda da jama'a na rundunar yansandan jihar Kano ya shaida wa BBC cewa yanbindigar sun shigo ne daga jihar Katsina da ke makwabtaka da Kano.

Wannan na zuwa bayan mazauna yankin ƙaramar hukumar Shanono a jihar Kano sun koka game da yadda 'yanbindiga masu satar mutane suka fara addabarsu suna satar mutane da kuma dabbobi.

SP Kiyawa ya tabbatar da cewa an samu kutsen wasu da ake zargin ƴanbindiga ne a yankin ƙaramar hukumar Shanono kuma suna satar mutane da dabbobinsu.

"Bayan samun labarin kwamishinan ƴansanda na jihar Kano ya tura jami'ai a yankin da suka yi aiki a ƙarƙashin ƙasa inda aka ci gaba da bibiya wanda ya kai ga nasarar kama mutum biyu," in ji shi.

Ya ƙara da cewa mutanen biyu suna hannun rundunar ƴansandan jihar Kano kuma ana faɗaɗa bincike.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ƴansandan Kano ta ƙara baza jami'an tsaro domin daƙile matsalar ƴanbindigar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

SP Kiyawa ya ce an girke jami'an tsaro a dajin Ɗansoshiya kan iyakar Kano da jihar Katsina da ke makwabtaka da ƙananan hukumomin Rogo da kuma Shanono.

An kuma girke jami'an tsaro a kan iyakar Kano da Kaduna musamman a dajin Falgore, a cewar kakakin rundunar ƴansandan na jihar Kano.

Ya kuma ce suna aiki da al'umomin yankin domin taimaka masu da bayanan sirri domin maganin matsalar.

Hare-haren ƴanbindiga masu fashin daji a Kano wani sabon al'amari ne. Galibi sun fi addabar jihohin Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da hare-haren.

Ƴanbindigar suna da sansanoni a dazukan Zamfara da Katsina da Kaduna da Sokoto da Neja da kuma Kebbi inda suke ƙaddamar da hare-hare kan al'umma.

Wasu na ganin sulhun da aka yi da wasu ƴanbindigar a Katsina ne ya sa suka fara tsallakowa zuwa Kano cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya.

Rahotanni sun ce ƴanbindiga yanzu sun koma kai hari kan masu haƙo ma'adinin zinari maimakon kai wa manoma hari da satar mutane sakamakon sulhun da suka yi wanda ya rage masu hanyoyin samun kuɗi.

Kodayake, ƴanbindiga ba su da wata aƙida illa fashin daji da satar mutane domin kuɗin fansa, amma masana na bayyana damuwa kan alaƙar wasunsu da ƴanbindiga masu da'awar jihadi musamman Iswap da Boko Haram da Ansaru da kuma Lakurawa.