Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Tinubu ya sauke rabin alƙawarin da ya ɗauka bayan shekara biyu?
Najeriyar yanzu, babu ko shakka ta sha bamban da Najeriyar da aka sani shekara biyu da suka gabata, lokacin da Bola Tinubu ya karbi mulkin ƙasar.
Abubuwa da dama sun sauya tun daga lokacin da aka rantsar da sabon shugaban ƙasar, inda nan take ya furta ɗaya daga cikin manyan manufofin da suka sauya lamurran ƙasar tun bayan samun ƴanci - cire tallafin man fetur.
Wannan ɗaya ne daga cikin alƙawurran da Tinubu ya ɗauka tun a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Shi ya sa ma wasu ke ganin cewa mulkin Tinubu akasi ne na mulkin magabacinsa Muhammadu Buhari, kasancewar "an san abin da Tinubu ya ƙuduri aniyar yi, kuma su yake yi" ba kamar gwamnatin magabacin nasa ba, wadda al'ummar ƙasar da dama ke ganin cewa ta gaza cimma hasashensu.
A yanzu Tinubu ya cika shekara biyu cif da hawa mulki, wato rabin wa'adin shugabancinsa na shekara huɗu ke nan. Ko ya cika rabin alƙawurran da ya ɗauka?
Murtala Mohammed Adogi, wanda masani ne kan manufofi da ƙudurorin gwamnati ya ce bisa nazarinsu, Bola Tinubu bai cika rabin alƙawurran da ya ɗauka ba.
BBC ta duba muhimman alƙawurran da shugaban ƙasar ya ɗauka da kuma rawar da ya taka:
1- Daidaita darajar naira
A jawabinsa na kama mulki, Tinubu ya ce: "Tsare-tsaren kuɗi abu ne da ke buƙatar kyakkyawan tunani. Wajibi ne CBN ya samar da farashin canji bai ɗaya. Hakan zai sa a daina saye da sayar da kadarori cikin sauri kuma a koma zuba jari da samar da ayyukan da za su taimaka wa tattalin arziki a aikace."
Jim kaɗan bayan kama mulki sai Tinubu ya ɗauki wasu tsauraran matakai a yunƙurinsa na daidata darajar naira.
Ya dakatar da shugaban Babban Bankin ƙasar, Godwin Emefiele sannan ya sanar da matakin sakar wa naira mara ta tantance darajarta a kasuwa.
Za a iya cewa Tinubu ya cika wannan alƙawari baki ɗaya, ba ma rabinsa kawai ba. to amma ko hakan ya magance zubewar darajar naira?
A'a.
A watan Mayun 2023 lokacin da Muhammadu Buhari ya miƙa mulki ga Bola Tinubu, ana canza dalar Amurka ɗaya kan naira 464.51 a hukumance, yayin da ake sayen dalar kan naira 762 a kasuwar bayan fage.
Matakin da Tinubun ya ɗauka a watan Yunin 2023 ya tura farashin nairar zuwa 664.04 a hukumance.
Daga lokacin kuma darajar nairar ta ci gaba da zubewa har zuwa yau, inda yanzu aka canza dala ɗaya kan kimanin naira 1,600.
Dakta Mohammed Adogi ya ce za a iya cewa Tinubu ya cika alƙawari wajen rage tangal-tangal ɗin darajar naira amma kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.
"To amma idan an samu daidaituwar darajar naira rayuwar mutane fa, ta inganta? Hanyoyin samun abinci sun inganta? Akwai abin da ya canza?" in ji Adogi.
2 - Tallafin man fetur
"Tallafin man fetur ya tafi," in ji Tinubu a ranar da aka rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya.
Shugaban ya samu yabo daga waɗanda ke ganin cewa Najeriya ta daɗe tana ɓarnatar da kuɗaɗe wurin rage farashin fetur ga al'ummar ƙasar, yayin da wasu kuma suka soki shugaban kasancewar matakin ya zamo asasi na tashin farashin komai a Najeriya.
A lokacin da Muhammadu Buhari ya bar mulki ana sayar da litar man fetur ɗaya ne kan kimanin naira 180, amma ya zuwa watan Yulin 2023 farashin litar man fetur ɗaya a Najeriya ya nunka fiya da sau uku, zuwa kimanin naira 600 a wasu sassan.
Shi ma a wannan alƙawari za a ce Tinubu ya cika amma lamarin ya haifar da tashin farashin kayan masarufi ta yadda al'umma ƙasar suka faɗa cikin mawuyacin hali, kasancewar gamwantin ta gaza cika alƙawarin samar da tallafin da zai sauƙaƙa rayuwa.
3 - Tsaro
A shekarar 2023 lokacin da Tinubu ya karɓi mulkin Najeriya tsaro na daga ckin manyan abubuwan da suka addabi Najeriya.
Matsalar ƴan fashin daji ta yi ƙamari, garkuwa da mutane ta zama ruwan dare a jihohin arewa maso yammacin Najeriya, duk da an samu sassauci daga hare-haren Boko Haram a arewa maso gabas, inda har gwamnatin shugaba Buhari ta yi iƙirarin cin galaba kan ƙungiyar.
Bayan zuwan Tinubu an samu ɗorewar tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadda a baya ta yi ƙaurin suna wajen satra mutane, amma aka samu sauƙi a ƙarshen mulkin nasa.
Sai dai matsalar garkuwa da mutane ta ci gaba da addabar mutane a arewa maso yamma, inda ƴan fashin daji suka ci gaba da addabar mazauna ƙauyukan jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da Sokoto da kuma Neja.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce an kashe aƙalla mutum 10,217 da tarwatsa ƙauyuka sama da 672 tun bayan kama mulkin Tinubu.
Rikici da hare-hare ya ƙara ƙazancewa a jihohin Filato da Benue sannan hare-haren Boko Haram sun ƙara ƙamari daga ƙarshen shekarar 2024 har zuwa tsakiyar 2025 lokacin da Tinubun ke cika shekara biyu a kan mulki.
Dakta Adogi ya ce nasarar da aka samu wajen tabbatar da tsaro a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kano abin a yaba ne, amma an gaza magance tushen matsalar tsaro a ƙasar.
"An yi ƙoƙari wajen magance abubuwa na gaggawa kamar tallafa wa mutanen da rikici ya tarwatsa da samar da gine-gine amma ba a magance abubuwan da suka haifar da matsalar ba, kamar rashin aikin yi da talauci," in ji Adogi.
Ya kammala da cewa "kamar an kashe maciji ne ba a cire kai ba."
4 - Ƴancin faɗin albarkacin baki
Haka nan a lokacin rantsar da shi shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa za ta zamo "mai tuntuɓa da neman shawarwari, ba wadda za ta dinga ƙaƙaba wa mutane abin da ba sa so ba".
Ya ce "Gwamnatinmu za ta yi jagoranci ba mulaka'u ba. Za mu yi tuntuɓa da tattaunawa, ba za mu yi ƙarfa-ƙarfa ba."
"Za mu nemi gudummawar kowa, amma ba za mu ware wani ba kawai saboda ra'ayinsa ya saɓa da namu ba."
Bayan shekara biyu, Mohammed Adogi na ganin cewa gwamnatin Tinubu ta yi ƙoƙari wajen kawar da ido daga masu sukar ta.
"Ya zuwa yanzu ba mu ga an yawaita kama masu adawa da gwamnatin ana tsare su ba, saboda haka nan ya bai wa mutane damar faɗar albarkatun bakinsu."
Sai dai Adogi ya ce gwamnatin ba ta cika sauraron shawarwariin da al'ummar ke ba ta ba.
"Ko ni na yi rubutu da dama, na bayar da shawara kan abubuwa da suka kamata a yi, amma suna jin shawara ne? Ban ga alamun suna ɗaukar shawara yadda ya kamata ba."
Sai dai duk da haka wasu matakan da hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa ta ɗauka na kama tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasar Farfesa Yusuf Usman da kuma sanannen mai amfamni da shafukan sada zumunta Martins Vincent wanda aka fi sani da Verydarkblackman sun tayar da ƙura.
EFCC ta ce ta kama Farfesa Usman ne bisa zargin badaƙala ta naira miliyan 90 sai dai wasu na zargin cewa an kama shi bisa zafafawar da yake yi wajen adawa da manufofin gwamnatin shugaba Tinubu.