Barcelona na nazari kan Rashford, Nunez na son komawa Napoli

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona na tunanin ɗaukar aron ɗan wasan gaban Manchester United ɗan ƙasar Ingila Marcus Rashford mai shekara 27. (Guardian)
Ɗan wasan Liverpool da Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 25, ya fi bayar da fifiko kan komawa Napoli idan har ya bar Anfield a bazarar nan. ( Football Italia)
Nottingham Forest ta yi watsi da tayin da Newcastle ta yi mata na kusan fam miliyan 45 kan ɗan wasan Sweden Anthony Elanga, mai shekara 23, wanda ta ƙaƙaba masa farashin Fam miliyan 60. (Sky Sports)
Chelsea na fatan gaggauta kammala cinikin ɗan wasan gaban Borussia Dortmund ɗan ƙasar Ingila Jamie Gittens, yayin da Bayern Munich ma ke zawarcin ɗan wasan mai shekara 20. (The Athletic)
Newcastle na da niyyar mayar da ɗan wasan gaban Sweden Alexander Isak mai shekara 25 ya zama ɗan wasan da ya fi samun albashi mafi tsoka a tarihin kulob ɗin don kawar da zawarcinda Liverpool da Barcelona da kuma Arsenal. (Times)
Fenerbahce na zawarcin ɗan wasan gaban Manchester United Jadon Sancho, mai shekara 25, wanda farashinsa ya kai Fam miliyan 25. (Talksport)
Sunderland ta tuntuɓi Sassuolo game da yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Faransa Armand Lauriente mai shekara 26. (ESPN)
Everton da Manchester United na zawarcin ɗan wasan Leicester ɗan Najeriya Wilfred Ndidi, mai shekara 28, wanda zai iya barin ƙungiyar a kan farashin fam miliyan 9. (Talksport)
Har yanzu Leeds ba ta samu tayi kan golan Faransa mai shekara 25 Illan Meslier ba duk da rahotannin da ke cewa yana shirin zuwa gwada lafiyarsa a Fenerbahce. (Sky Sports)
Ana sa ran golan Chelsea ɗan kasar Sifaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 30, zai kammala komawa Arsenal a kan cinikin fam miliyan 5 a wannan makon. (Sky Sports)
Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Athletic Bilbao ɗan ƙasar Sifaniya Nico Williams, mai shekara 22, wanda ke da farashin fam miliyan 50 a kwantiraginsa, ya shaidawa ƙungiyar cewa yana da sha'awar komawa Barcelona. (Athletic)
Burnley na shirin gabatar da tayinfam miliyan 12 kan ɗan wasan Lazio ɗan kasar Faransa Loum Tchaouna, mai shekara 21. (Football Italia)











