Me ya sa Iran ta kai hare-hare kan ƙawayenta?

Asalin hoton, Getty Images
Iran ta kai hare-hare kan ƙasashe uku da take ƙawance da su - Syria da Iraƙi da kuma Pakista - cikin kwana biyu. Cikin gaggawa Pakistan ta mayar da martani ta hanyar kai harin makami mai linzami kan iyakar Iran. Me ya sa Iran ta kai harin, kuma mene ne ke faruwa yanzu?
Duka waɗannan alamu ne na matsin lambar da dakarun sojin juyin juya hali na Iran ke ciki na su ɗauki mataki kan masu kaifin kishin Islama na cikin ƙasar.
Masu kaifin kishin Islamar na ci gaba da nuna damuwa game da yadda Iran ta zuba idanu Isra'ila take kashe mutane masu yawa a Gaza.
Kuma ga damuwar da suke nunawa ta gaza yin komai da Iran ɗin ta yi na yadda abokiyar gabarta Isra'ila take kashe manyan kwamandojin dakarun juyin juya halinta a Syria - kuma da kalmomin baki kawai suka nuna goyon bayansu ga Houthi lokacin da Amurka da Burtaniya suka kai musu hare-hare.
Akwai kuma harin bam da ƙungiyar IS ta yi ikirarin kai wa a birnin Kerman na Iran makonni biyu da suka gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 84.
Dakarun rundunar na jin cewa suna da haƙƙin yin wani abu game da wannan lamari ko ta halin ƙaƙa. Ba tare da wani matsin lamba ga Amurka ko Isra'ila ba, Iran na yin takatsantsan wajen shiga cikin wannan yaki da ake yi tsakanin Gaza da Isra'ila, ko da yake ta yi tayin taimakon soji ga Hamas da Houthi da kuma Hezboullah.
Amma a harin da ta kai a Syria da Iraƙi da kuma Pakistan, ana ganin ba ta yi nasara ba kamar yadda ta yi tsammani.
Iran ta ce harin makami mai linzami da na jirgi maras mauƙi da takai Pakistan ta hari mayaƙan ƙungiyar Jais al Adli - wadda ta kira "ƙungiyar 'yan ta'adda ta Iran". Amma Pakistan ta ce ta kashe yara biyu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Pakistan da ke da makamin nukiliya na jin cewa ya kamata ta mayar da martani kan wannan hari - wanda ya take haƙƙin Pakistan na zama ƙasa mai cikakken 'yanci a zahiri. Wanda kuma ya nuna raini ga mallakar makamin nukiliya da Pakistan ta mallaka.
Kuma ta kai hare-hare a raɗin kanta kan abin da takira maboyar "yan ta'addan" Pakistan da ke Iran - Ƙungiyoyin Balochistan Liberation Army da Balochistan Liberation Front. Iran ta ce an kashe mata uku da maza biyu da kuma yara hudu.
Iran da Pkistan suna da iyaka ta kimanin kilomita 900 kwatan kwacin mil 560, yadda za a kare iyakar ya zama abu mai wuya tsakanin ƙasashen biyu.
Pakistan dai ƙawa ce mai daraja a kawance duniya, kuma ko da yaushe tana goyon bayan Tehran a lamura daban-daban.
Harin da aka kai Syria kuma wata ramuwa ce kan kisan da aka yi a Kerman. Amma ko a can babu rahoton harin ya yi wa IS ɓanna ko ƙungiyar Sunni kamar yadda Iran ta yi iƙirari.
Amma a ɓangaren Iraƙi - Iran ita ce makwabciyarta ta kusa - Gwamnati ta fusata da hare-haren makamai masu linzami 11 da aka harba Irbil, ya yankin Iraƙi Kurdistan.
Gwamnatin Iraƙi ta yi wa kwamitin sulhu na MDD ƙorafi, wanda ta so a zauna a tattauna kan waɗannan hare-hare.
Dakarun juyin juya halin Iran sun yanke shawarar kai hare-haren ne kan ƙasashen uku bayan tuntubar da suka yi wa shugaban jagoran addini na Iran. Akwai alamun ba a tuntuɓi ministan harkokin wajen ƙasar ba gabanin kai wadannan hare-hare.











