Idan Jonathan ya tsaya takara a 2027 mutuncinsa zai zube - Shehu Sani

Asalin hoton, OTHERS
Tsohon ɗan majalisar dattijan Najeriya, Sanata Shehu Sani ya ce rikicin da babbar jam'iyyar hamayya ta kasar, PDP ke fama da shi da ficewar wasu daga cikin 'yan majalisa da gwamnonin jam'iyyar zuwa APC, na daga cikin dalilan da suka sa, yake shawartar tsohon shugaban kasar Goodluck Ebele Jonatahan da kar ya tsaya takara a zaɓen 2027.
Shehu Sani ya sheda wa BBC cewa shigar Jonatahn takarar na iya shafar mutunci da girmamawar da ya samu a ciki da wajen Najeriya.
''Na farko dai a shekarun baya kamar zaben 2019 da 2023 an yi irin wadannan kiraye-kiraye na jawo Jonathan ya sigo filin takara amma ya ja da baya, saboda ya hanga ya ga hadarin da ke tattare da hakan ta fuskar kare kimarsa,'' in ji Sani.
Tsohon Sanatan na mazabar Kaduna ta tsakiya ya kara bayani da cewa Jonathan ya yi hakan ne saboda a matsayinsa na shugaba da ake ganinshi da kima da girma, ya kamata ya rike girmansa kar ya sake fadawa fagen siyasa a halin yanzu.
Ya ce jam'iyyar da ta dora shi a kan mulki wato PDP ba irin wadda ya sani ba ce a da, saboda yanzu akwai rikice-rikice a cikinta.
Ya bayar da misalin yadda ya ce wani bangare na jam'iyyar da ya fito daga kudu maso yammacin Najeriya ya amince da Shugaba Tinubu ya ci gaba duk da cewa Tinubun dan APC ne.
''Da yawa 'yan majalisunsu da kuma gwamnoninsu sun koma jam'iyyar APC. To ganin haka nake ganin a halin yanzu ya hakura ya rike girmansa, kamar yanda ake girmama shi a Najeriya da Afirka da sauran kasashen duniya. Ya ci gaba da zama a matsayinsa na shugaba kuma uban kasa.'' A cewar Shehu Sanin.
Dangane da yadda wasu ke kallon cewa kimar tsohon shugaban kasar ce ta sa PDP ke son ya yi mata takara domin ya dinke barakar cikinta ya sake dunkule ta waje daya, sai Kwamared sani ya ce : ''Ai yanzu kusan babu mutum daya da zai iya tsawatarwa don magance rikice-rikicen da jam'iyyar ke fama da su.''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya kara da cewa: '' ba ta yadda za a yi wani ya fito ya ce zai yi takara a PDP a ce ministan Abuja Nyesom Wike, wanda dan PDP ne bai yi amfani da kudi da kuma mulki ba ya kai dan takarar kasa.''
Game da yadda wasu ke ganin ko Shehu Sanin na fargabar ko Jonathan zai kayar da Tinubu ne idan ya shiga takarar ta 2027, sai ya gaya wa BBC cewa, shi ba ya zaton ko ya fito takara zai iya kayar da shugaban.
''A halin gaskiya gani nake nashi lokacin ya yi kuma ya yi kokari duk da yake sai daga baya mutane suka gane adalcinsa da gaskiyarsa,'' in ji shi.
Ya kara dacewa, ''ni kawai saboda girmamawar ne nake ganin bai kamata ya shiga wannan takara ba.''
Tsohon Sanatan ya jadda matsayar tasa a kan shawartar tsohon shugaban na Najeriya da kada ya yarda ya yi takarar a 2027, yana mai nuni da cewa: ''Ina ganin ba shi da jam'iyyar da za ta taimaka masa har ya hau kan mulki. Maimakon ya hau ya kunyata kansa ina ganin kwanda ya rike girmansa.
A makonnin da suka gabata ne wannan magana ta dauki hankali a Najeriya, inda wasu jiga-jigan jam'iyyar ta PDP kamar tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido suka nuna cewa tsohon shugaban na Najeriya ya fi dacewa da yi wa jam'iyyar takara a 2027.
Shi dai Goodluck Ebele Jonathan ya ja baya a harkokin siyasa tun da ya fadi zabe a 2015.
Jam'iyyar PDP dai ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da shi domin ya yi mata takarar shugaban ƙasa don kalubalanar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓe mai zuwa.










