Me zai faru idan Jonathan da Obi suka haɗe wuri guda?

Asalin hoton, Jonathan/Peter Obi/X
Yayin da ake ci gaba da tunkarar babban zaɓen 2027 a Najeriya, ƴansiyasa na ci gaba da lissafi da kitsa dabarun da za su kai su ga nasara.
Ƴansiyasa da dama na ci gaba da ƙoƙarin ƙulla ƙawance da zawarcin wasu, duk dai domin cimma babban burinsu na samun nasara a 2027.
A farkon makon nan aka samu wasu rahotanni da ke cewa ɓangaren tsohon shugaban ƙasa, GoodLuck Jonathan da ɓangaren Peter Obi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023 na tattaunawa a wani yunkuri na haɗuwa domin tunkarar zaɓen 2027.
A wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, a ƙarshen mako, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Dumebi Kachikwu ya yi iƙirarin cewa Jonathan ya yi wa Peter Obi tayin ba shi ministan kuɗi da tattalin arziki, idan ya jingine takara a zaɓe mai zuwa.
A baya-bayan nan ne dai wasu makusantan Jonathan suka bayyana cewa suna tattauna wa da shi domin shawo kansa ya amince da yi wa PDP takarar shugaban ƙasa a 2027.
Haka ma an jiyo tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido - wanda tsohon makusancin tsohon shugaban ƙasar ne - na cewa babu wanda ya dace da yi wa PDP takara a 2027 fiye da Jonathan.
Muna maraba da wannan haɗakar - PDP

Asalin hoton, PDP
To sai daI jam'iyyar PDP ta GoodLuck Jonathan ta ce ba ta san da wannan magana ba, amma kuma idan Obi zai koma cikinta za ta yi maraba da shi.
Kakakin Jam'iyyar na ƙasa Ibrahim Abdullahi ya shaida wa BBC cewa ai dama Peter Obi nata ne, don haka idan zai dawo jam'iyyar za ta so hakan.
''Ai dama Peter Obi namu ne, matsala aka samu ya fita a kakar zaɓen da ta gabata, to yanzu idan ya dawo ba abin mamaki ba ne'', in ji shi.
Ibarhim Abdullahi ya ce PDP za ta yi maraba da haɗakar, tunda yanzu makomar ƙasar za a duba ba ra'ayin ɗantakara ba.
''Idan kuma da gaske suke yi to za su yi abin da ya kamata zai zama masalaha ga al'umma da ƙasar baki ɗaya'', in ji kakakin na PDP.
'Sai dai idan Jonathan zai mara wa Obi baya'

Asalin hoton, Peter Obi/X
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
To sai ɗan ɓangaren na Peter Obi ya ce waɗanda ke wannan ƙulle-ƙulle na da wata manufa ne a zaɓen 2031.
Ibrahim Hussain Abdulkarim makusancin Peter Obi ne ya kuma shaida wa BBC cewa abin da kawai suka sani shi ne akwai kyakkayawar alaƙa tsakanin mutanen biyu.
''Duk wanda ya san mutanen biyu a lokacin gwamnatin Jonathan ya san irin muhimmanci Obi da irin rawar da ya taka a gwamnatin'', in ji Ibrahim Abdulkarim.
To sai dai ya ce a matakin da Peter Obi ya kai yanzu ba zai iya karɓar muƙamin minista ba.
''A halin da muke ciki yanzu ba magana ba ce ta dawowa, magana ce da ta yin gaba, mun riga mun taɓa gwamnatin Joanathan yanzu gaba muke hari'', in ji shi.
Ibrahim Hussain Abdulkarim ya ce Idan ma za a ƙulla ƙawancen to sai dai Jonathan ɗin ya mara wa Obi baya.
''Mu fatanmu koda za a tattauna to shi Jonathan ya zo ya mara wa Peter Obi baya , saboda a samu nasarar kawo sauyin da ake buƙata'', in ji shi.
To sai dai kakakin jam'iyyar ta PDP, Ibrahim Abdullahi ya ce a shirye jam'iyyar take ta bai wa kowa dama tsayawa takara, kuma duk wanda kuma ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani to sai ta goya masa baya.
Me zai faru idan aka cimma ƙawancen?

Asalin hoton, Peter Obi/X
Farfesa Abubakar Kari ya ce inda ƴansiyasar za su amince su ƙulla wannan ƙawance abu ne da zai taimake su dukkansu.
''Kowanne a cikin su biyu zai iya kasancewa ƙaɗangaren bakin tulu ga ɗayan, saboda inda suke tsammanin za su samu matuƙar karɓuwa idan sun tsaya takara, shi ne yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudanci''.
''Don haka idan duka suka yi takara za su janyo wa juna cikas'', in ji shi masanin siyasar.
Farfesa Kari ya ce duk da cewa haɗuwar tasu a ƙarƙashin inuwa guda abu ne da kamar wuya, amma kuma ya ce a siyasa ba abin da ba zai yiwa ba.
Masanin siyasar ya ce makusantan Peter Obi za su iya zuga shi kada ya yarda, amma kuma ya ce abin da ya kamata ya yi kenan.
''Kullum yana nuna cewa shi masanin tattalin arziki ne, mafi yawan maganganunsa yakan yi su ne kan tattalin arziki, don haka ni ina ganin idan aka ba shi ministan tattalin arziki ai zai dace da shi''.
Farfesa Kari ya ce yana ganin idan har duka mutunen biyu suka tsaya takara, to babu shakka za su yi wa juna asarar ƙuri'un yankunansu.
Yayain da ake ci gaba da yin dabdala a fagen siyasar Najeriya, wani abu da bakunan masu hamayya suka zo ɗaya a kansa shi ne akwai buƙatar yin taron dangi domin kawar da gwamnatin APC da Bola Tinubu a 2027.
To sai dai yadda alƙaluman siyasar ƙasar ke ci gaba da sauyawa masana na ganin akwai sauran lokaci a iya hasashen abin da zai faru.











