Sabon jagoran Syria ya ce dole ne a cire wa ƙasar takunkumi

Ahmed al-Sharaa

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban kungiyar 'yan tawayen da ta hambarar da gwamnatin Basahr al-Assad na Syria, HTS, Ahmed al-Sharaa ya gaya wa wakiliyar musamman ta Birtaniya da ta ziyarci kasar cewa dole ne a cire wa Syria takunkuman da aka Sanya mata na duniya.

Birtaniya ta kasance daya daga cikin kasashe kadan da suka tura wakilansu babban birnin na Syria, Damascus, tun bayan da 'yan tawayen suka kawar da gwamnatin Assad sama da mako daya da ya wuce.

Ahmed al-Sharaa ya gaya wa jakadiyar ta musamman ta Birtaniya, Ann Snow, cewa abu ne da yake da muhimmancin sosai a kawo karshen takunkuman da aka sanya wa kasar a lokacin mulkin Bashar al- Assad, domin ta hakan ne 'yan kasar ta Syria da suka tsere za su iya komawa gida.

Miliyoyin 'yan gudun hijira na Syria na warwatse a fadin yankin Gabas ta Tsakiya da Turai da kuma sauran sassan duniya sakamakon mummunan yakin basasar kasar na sama da shekara goma.

Birtaniya ta haramta kungiyar 'yan tawayen da ta yi nasara a kasar ta Syria ta Hayat Tahrir al-Sham, a matsayin kungiyar 'yan tadda, to amma jagoran nata, al-Sharaa na kokarin nesanta ta daga asalinta na kungiyar masu ikirarin jihadi.

To amma a ranar Lahadi Birtaniyar ta sanar da bayar da kunshin taimako daya kai na fan miliyan 50 – kwatankwacin dala miliyan 63, domin taimaka wa 'yan Syria masu Rauni da ke cikin bukata.

Daga cikin kudin za a yi amfani da fam miliyan 30 wajen samar da taimako na kai tsaye ga mutane sama da miliyan daya – inda za a sama musu abubuwan da suka hada da abinci da matsuguni, da kula da lafiya da kuma tabbatar musu da kariya.

Za kuma a yi amfani da kudin taimakon wanda galibi ake bayar da shi ta hanyar hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, wajen samar da muhimman abubuwa na bukata – kamar ruwa da asibitoci da makarantu.

Miliyoyin 'yan Syria ne dai ke bukatar taimako, bayan yakin basasar na sama da shekara goma wanda ya daidaita yawancin kayan jin dadin rayuwa, tare da sa al'ummar kasar da dama tserewa

Tuni wasu daga cikin wadanda suka bar kasar suka fara komawa daga makwabtan kasashe bayan hambarar da gwamnatin ta Assad.

Jagoran kungiyar da ke shugabantar Syriar a yanzu tun da farko ma ya sanar da cewa za a ruguza bangarorin kungiyoyin 'yan tawaye na kasar sannan a sanya mayakansu cikin ainahin rundunar sojin Syriar.