Jihohin Najeriya da ambaliyar ruwa ta fi kashe mutane a 2025

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta ce aƙalla mutane 232 ne suka mutu sanadin ambaliyar ruwa daga watan Janairu zuwa Satumban shekarar 2025 a fadin ƙasar.

NEMA ta kuma ce mutane sama da dubu 121 ne suka rasa matsugunansu a irin wannan iftila'i.

Wani rahoto da hukumar ta fitar, ya kuma ce ambaliyar ruwa ta shafi sama da mutum dubu 339 tare da lalata gidaje fiye da dubu 42.

Hukumar ta kuma ce ambaliyar ta lalata gonaki a faɗin Najeriya da girmansu ya kai hekta dubu 48, inda kuma mutane 115 suka yi ɓatan dabo da har yanzu ba a gan su.

Yadda ambaliyar ta shafi jihohi 24

..

Asalin hoton, Getty Images

  • Abia: Ambaliyar ta shafi mutum 11,907, inda ta tilasta mutum 4,896 barin matsugunansu.
  • Adamawa: Jihar Adamawa ta rasa mutum 59 sannan ta shafi mutum 57,890 inda mutum 23,077 suka bar gidajensu sannan mutum 438 sun samu raunuka.
  • Abuja: Ambaliyar a babban birnin tarayyar Najeriya ta shafi mutum 1,025 sai dai babu wanda ya rasa ransa a ibtila'in.
  • Akwa Ibom: Ita kuwa jihar ta Akwa Ibom tana da mutum 46,233 da al'amarin ya shafa sannan kuma ta tilasta mutum 40,140 barin gidajensu.
  • Anambra: A jihar Anambra, al'amarin ya shafi mutum 925 inda 816 suka bar matsugunansu.
  • Bayelsa: Mutum 5,868 ne al'amarin ya shafa a jihar ta Bayelsa.
  • Borno: Mutum 1 ne ya rasu a jihar Borno, bayan da ibtila'in ya shafi mutum 8,164 inda 2,436 suka bar muhallinsu.
  • Cross River: Mutum 5,646 ne ambaliyar ta shafa inda 5,518 suka bar gidajensu.
  • Delta: Mutum 14,057 ne abin ya shafa kuma 3,325 suka fice daga gidajensu.
  • Edo: A jihar Edo kuwa mutum 10,608 ne abin ya shafa sannan 2,439 ne suka bar gidajensu.
  • Gombe; Mutum 4,098 ne abin ya shafa sannan 865 suka bar gidajensu sai kuma mutum 12 da suka samu rauni sakamakon ibtila'in.
  • Imo: Mutum 29,242 ne ambaliyar ta shafa sannan 15,607 suka gudu suka bar muhallinsu.
  • Jigawa: Mutum 1 ne ya rasu sakamakon ibtila'in ruwan a jihar Jigawa daga cikin mutum 3,650 da ta shafa sannan 293 suka tsere daga muhallinsu.
  • Kaduna: Mutum 7,334 ambaliyar ta shafa sannan ta tilasta 662 barin gidajensu.
  • Kano: A jihar Kano mai yawan al'umma, ambaliyar ta shafi mutum 1,446 amma ba bu rasa rai ko kuma barin muhalli.
  • Kogi: A jihar Kogi, ambaliyar ta shafi mutum 2,825 da gidaje 892.
  • Kwara: Ambaliyar ta shafi mutane 2,663 a jihar da ke tsakiyar Najeriya.
  • Lagos: Jihar Lagos mai yawan jama'a ta zamo a gaba-gaba inda al'amarin ya shafi mutum 57,951 tare da ɗaiɗaita mutum 3,680 bayan lalata gidaje 3,244.
  • Nassarawa: Al'amarin ya shafi mutum 749 tare da lalata gidaje 27.
  • Neja: A jihar Neja kuwa, ambaliyar ta shafi mutum 6,041 sannan ta ɗaiɗaita 1,660 inda kuma mutum 163 suka rasa rai.
  • Ondo: Mutum 3,735 ne abin ya shafa sannan ta ɗaiɗaita mutum 363 tare da lalata gidaje 407.
  • Rivers: Mutum 22,722 ibtila'in ya shafa a jihar River da ke bakin ruwa inda 9,645 suka ɗaiɗaita, 88 suka samu raunuka sannan gidaje 121 suka lalace.
  • Sokoto: Jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya ta samu mutum 4,278 da abin ya shafa sannan 1,287 suka ɗaiɗaita sai kuma gidajen 175 sun lalace.
  • Taraba: Mutum 26,722 ne abin ya shafa sannan 3,080 sun bar gidajensu sai kuma 88 da suka samu rauni inda kuma biyar suka mutu sannan gidaje 5,150 suka lalace.
  • Yobe: Mutum 4,256 ne abin ya shafa sannan 486 sun ɗaiɗaita, 3 sun samu rauni, 2 sun mutu sannan gidaje 572 sun lalace.

Madatsun ruwa shida da suka fi janyo ambaliyar ruwa a Najeriya

  • Madatsar ruwa ta Lagdo - Kamaru
  • Madatsar ruwa ta Kainji - Jihar Neja
  • Madatsar ruwa ta Jebba - Jihar Neja
  • Madatsar ruwa ta Shiroro - Jihar Neja
  • Madatsar ruwa ta Alau - Jihar Borno
  • Madatsar Kashinmbila – Taraba

Abubuwan da ke haifar da ambaliya

Wani masani kan matakan kariya a sashen lura da muhalli na Jami'ar Bayero da ke Kano, Dakta Yusuf Idris ya shaida wa BBC cewa akwai abubuwa da dama da ke haddasa ambaliyar ruwa a Najeriya. Manya daga cikinsu su ne:

  • Sauyin yanayi
  • Rashin kula da madatsun ruwa
  • Rashin magudanan ruwa
  • Rashin tsara hanyoyin zubar da shara

Dr Garba ya ce rashin nazari kan yanayin muhalli na daga cikin abin da ke haifar da cika da tumbatsar rafuka har ta kai ga samun ambaliya.

Ya bayyana cewa idan aka yi la'akari da mummunar ambaliyar da aka samu a jihar Borno a shekarar 2024 "ɗabi'ar rashin kula da bin shawarwarin wadanda suka gina madatsar ne sila."

Haka nan ya yi bayani kan yadda samun ruwa mai ƙarfi ba tare da tsammani sanadiyyar sauyin yanayi ke haifar da matsaloli.

"Sanadiyyar abubuwan da suke faruwa a muhalli, kamar sauyin yanayi, ba a iya hasashen yawan ruwan sama da za a samu sanadiyyar rashin tabbas na yanayi.

"Wani lokaci za ka ga ana samun ruwan sama mai yawa a lokaci ƙankani, wanda hakan ke iya haifar da ambaliyar ruwa, musamman a yankunan da babu magudanan ruwa."