Madatsun ruwa shida da suka fi janyo ambaliyar ruwa a Najeriya

Madatsar ruwan Vaal Dam da ke ƙasar Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 7

A daidai lokacin da damuna ta yi nisa, hankalin mutane musamman waɗanda suke zauna a yankunan da ake hasashen samun ambaliyar ruwa sun fara shiga damuwa saboda fargabar halin da za su iya shiga.

A Najeriya, duk shekara, ambaliyar ruwa daga manyan madatsun ruwa daga cikin ƙasar da ma maƙwabta na haifar da asarar rayuka, lalata amfanin gona da kuma ruguza gidaje a ƙasar.

A shekarar da ta gabata, ambaliya ta ɗaiɗaita birnin Maiduguri, lamarin ya jawo asarar rayuwa da asarar ɗimbin arziki, wanda har yanzu waɗanda abin ya shafa ba su gama warwarewa ba.

Haka kuma a bana an yi ambaliyar ruwa a garin Mokwa da ke jihar Neja, wadda ta jefa mutanen yankin cikin tashin hankali.

Sai dai kamar abin da masu iya magana ke cewa, an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa, haka wasu ke cewa game da ambaliyar ruwa a Najeriya, kasancewa lamarin ya yawan maimaituwa, duk da matakan da gwamnatoci a matakai daban-daban suke cewa suna ɗauka.

Mun duba wasu daga cikin madatsun ruwa mafiya hatsari da kan haifar da ambaliyar ruwa a kai a kai a Najeriya:

Madatsar ruwa ta Lagdo - Kamaru

Dam

Asalin hoton, Getty Images

Kowace shekara miliyoyin al'umma a Najeriya na shiga cikin fargaba a duk lokacin da aka saki ruwa daga dam ɗin Lagdo da ke ƙasar Kamaru. Ruwan na ratsawa ta jihohi 10 na Najeriya.

Ɗaruruwan rayuka ne suka salwanta a shekarun da suka gabata sanadiyyar ambaliyar ruwa bayan sakin ruwa daga madatsar, haka nan ambaliyar ta raba dubban mutane da muhalli da kuma sana'o'insu.

Jihohin da kan shiga cikin haɗarin ambaliyar ruwa daga madatsar Lagdo su ne Adamawa, da Taraba da Kogi, da Nasarawa da Benue Anambra da Bayelsa da Cross River da Delta da Edo da da kuma Rivers.

An kammala gina madatsar ruwa ta Lagdo ne a shekara ta 1982 domin samar da wutan lantarki ga arewacin ƙasar Kamru da kuma aikin noman ban-ruwa.

To sai dai idan ruwa ya yi ruwa madatsar kan cika ta tumbatsa, lamarin da kan sanya hukumomi su saki ruwa daga madatsar.

Asali ya kamata Najeriya ta gina wata madatsar ruwa da za ta iya ɗauke ruwan da ake saki daga Lagdo, to amma har yanzu ba a kammala aikin madatsar ta Dasin Hausa dam ba.

Madatsar ruwa ta Kainji - Jihar Neja

Madatsar ruwa ta Kainji da ke Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Madatsar ruwa ta Kainji da ke Najeriya

Kainji dam ne madatsar ruwa mafi girma a kan Kogin Kwara, wato River Niger, wanda shi ne rafi na uku mafi tsawo a nahiyar Afirka.

Madatsar wadda aka yi aikin samar da ita daga 1964 zuwa 1968 na daga cikin manyan cibiyoyin samar da lantarki na Najeriya, haka nan ana amfani da shi wajen ayyukan noman ban-ruwa da kamun kifi da kuma sufuri.

A shekarar 2020 jihar Neja ta fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni a cikin shekaru, wanda aka ɗora laifin kan buɗe ruwa da aka yi daga madatsar ta Kainji da ruwan da ya kufto daga madatsun ruwa na Shiroro da kuma Jebba.

Ambaliyar ta kashe mutane da dama, ta mamaye ƙauyuka 150 tare da haifar da gagarumar asarar kayan amfanin gona.

Madatsar ruwa ta Jebba - Jihar Neja

Jebba dam madatsar ruwa ce da ke kan Kogin Kwara a kusa da garin Jebba na jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar ƙasar.

Kamar sauran madatsun ruwa da aka ambata a sama, Jebba an tsara ta ne domin aikin samar da lantarki. Sai dai madatsar wadda aka ƙaddamar a shekarar 1985 na taimaka wa al'umma wajen ayyuka na tattalin arziƙi.

A farkon shekarar 2025 rahotanni sun bayyana yadda sakin ruwa daga madatsar Jebba da Kainji ya haifar da asarar kimanin eka 5000 na gonakin shinkafa da aka yi ƙiyasin za su kai kuɗi naira biliyan 11.5.

Ambaliyar ta shafi ƙananan hukumomin Moro da Patigi da kuma Edu duk a jihar Kwara.

Madatsar ruwa ta Shiroro - Jihar Neja

Dam ɗin Shiroro madatsar ruwa ce da aka gina kan rafin River Kaduna a cikin ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Madatsar ta fara aiki ne a shekara ta 1990 inda take da ƙarfin samar da lantarkin da ta kai ƙarfin megawatts 600.

Bayanai sun nuna cewa yankunan da ke maƙwaftaka da madatsar Shiroro kan fuskanci ambaliyar ruwa lokaci zuwa lokaci, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da ta dukiya.

Madatsar ruwa ta Alau - Jihar Borno

Mazauna Maiduguri da Jere kan samu ruwan sha daga madatsar ruwa ta Alau

Asalin hoton, Borno State Government

Bayanan hoto, Mazauna Maiduguri da Jere kan samu ruwan sha daga madatsar ruwa ta Alau

An gina madatsar ruwa ta Alau a yankin ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno da ke da nisan kilomita 36 daga Maiduguri a shekarar 1986.

Kogin na ɗaya daga cikin kogunan da ke kwaranyewa cikin Tafkin Chadi bayan Ngadda da kuma Yedzeram, wanda shi ne mafi girma.

Babbar manufar gina Alau ita ce samar wa manoman rani ruwa, da kuma rage haɗarin ambaliyar ta hanyar tara ruwan da ya kai yawan cubic meter miliyan 112 (lita biliyan 112).

Ambaliyar ta mamaye kimanin kashi 40% na birnin Maiduguri, ta haifar da sarar rayuka aƙalla 40 da tarwatsa mutum kimanin 500,000, lamarin da ya kai ga tserewar dabbobi daga gidan ajiye namun daji na Maiduguri.

Madatsar Kashinmbila – Taraba

Kashimbila madatsar ruwa ce da aka gina a kan rafin Katsina-Ala River kusa da garin Kashimbila da ke ƙaramar hukumar Takuma ajihar Taraba, arewa maso gabashin Najeriya.

An tsara gudanar da aikin madatsar ne tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015 domin kawar da matsalar ambaliyar ruwar da kan shafin jihohin Benue da kogi da Cross River da kuma Delta.

Haka nan an tsara cewa madatsar za ta samar da ruwan sha ga al'umma da kuma samar da lantarki da kuma ruwan yin noma ga al'umma a jihar Taraba.

A cikin watan Mayun 2023 ne gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da madatsar da kuma cibiyar samar da lantarkin mai ƙarfin megawatt 40.

Sai dai rashin kammala aikin madatsar baki ɗaya ya sanya har yanzu al'umma a wasu jihohin Najeriya na kasancewa cikin hatsarin ambaliya da zarar aka saki ruwa daga madatsar Lagdo da ke Kamaru.

Me ke faruwa ?

Mahaɗar kogin Kwara da na Benue a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mahaɗar kogin Kwara da na Benue a Najeriya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Idan aka sako ruwa daga Lagbo, yana jawo ambaliya mai zafi a jihohin da suke maƙwabtaka da tekun Benue, musamman Adamawa da Taraba da Benue da Filato.

A shekarun baya, musamman a shekarun 2022 da 2023 an samu ambaliya a jihohin Najeriya da dama da aka alaƙanta da sakin ruwa daga dam ɗin na Lagbo.

A game da abin da ke faruwa daga madatsun ruwan har a samu ambaliya, BBC ta tuntuɓi Umar Ibrahim Muhammad, darakta-janar na hukumar kula da harkokin ruwa ta Najeriya wato Nigerian Hydrological Services Agency (NIHSA), wanda ya ce yawanci madatsun ruwan Najeriya suna haifar da ambaliya idan idan sun cika, sun tumbatsa, har suka fitar da ruwa.

Ya ce, "abin da ke faruwa shi ne ba a so waɗannan madatsun ruwan su cika, har ya zama an saki ruwan zuwa koguna. Akwai abin da ake kira "dam management", akwai wani mataki da ba a ruwn ya wuce. Don haka idan ba a kula da waɗannan matakan, sai ruwan ya tumbatsa, da dole a sake shi ba tare da shiri ba."

Sai dai ya ce a kan samu matsala,"kamar irin ta bara a Maiduguri wanda masu kamun kifi suka buɗe wani waje a dam ɗim domin su yi kamun kifi. Wannan ɗan ɓulin ne da ruwan ya yi yawa, har ya rinjaye shi ya ɓalle ya yi ambaliya."

Matakan kariya

Ambaliyar ruwa a jihar Kogi da ke Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ambaliyar ruwa a jihar Kogi da ke Najeriya

Shugaban hukumar ya ce akwai matakan da suke ɗauka tare da ɓangaren kula da madatsun ruwa domin kiyaye aukuwar ambaliyar.

"Muna magana da su ne domin sanin matakin da ruwan ke ciki a madatsun ruwa, mu kuma muna faɗa musu matakin da kogunanmu suke ciki. Hakan zai sa a san yaushe ya kamata a sako ruwa da kuma lokacin da bai kamata ba. Hakan ya sa ake samun sauƙin sako ruwan domin ana yi a hankali."

Ya ce fitar da ruwan a hankali ne ke sa kogunan suke iya kwashewa suna tafiya da su cikin sauƙi ba tare da madatsun sun cika maƙil ba, ballantana ma su fi ƙarfin madatsun, har su yi ambaliya.

"Yanzu haka mun ce a riƙa sako ruwan kaɗan-kaɗan saboda kogunanmu ba su cika ba, kuma madatsun ruwan ma ba su cika ba. Ka ga tun yanzu ya kamata su riƙa sako mana ruwan a hankali suna tafiya ta kogunan."

Umar ya ce ko a bar ambaliyar da aka samu ba daga madatsun ruwa aka samu matsalar ba, domin a cewarsa, "madatsun ba su yi cikar da gagara ba har su sako ruwan."

A ƙarshe ya ce duk matakan da ya kamata su ɗauka, sun ɗauka, "kamar wayar da kan al'umma a kan nisantar wuraren da aka hasashen ambaliya. Ka san duk matakan da aka ɗauka, dole a yi nisa saboda yanayin sauyin yanayi ya sa ba za mu iya cewa tabbas ba za a yi ambaliyar ba."

Sai dai ya ce ana aikin gina wasu madatsun ruwa da za su taimaka wajen tare ruwa daga manyan madatsun da suke jawo a ambaliyar a ƙasar.

"Akwai madatsun ruwan biyu a Benue da ɗaya a Adamawa sai wani a Kebbi, waɗanda aka tanada domin tare ruwa idan an sako su daga madatsun."