Mene ne ke haddasa yawaitar ambaliyar ruwa a Najeriya?

Rescuers dey carry pipo comot from di flood

Asalin hoton, Governor Fintiri/Facebook

    • Marubuci, Abubakar Maccido
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC, Kano
  • Lokacin karatu: Minti 5

Hukumar lura da yanayi ta Najeriya ta ce za a ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa a ƙasar sanadiyyar mamakon ruwan da za a riƙa tafkawa a wannan yanayi na damina.

Ambaliyar ruwa da aka samu a Adamawa cikin ƙarshen mako ta haifar da asarar rayuka aƙalla 15 a ƙananan hukumomin Yola North da Yola South, baya ga asarar ɗimbin dukiya.

Ambaliyar ta faru ne bayan marka-markar ruwan sama da aka wayi gari da shi ranar Lahadi a sassan jihar.

Duk da ƙoƙarin da hukumomi suka ce sun yi wajen kai ɗauki, mutane da dama su soki lamarin gwamnati kan cewa ta yi sakaci.

Lamarin da ya kai ga cewa gwamnan jihar Umau Fintiri ya fitar da sanarwa yana ƙoƙarin kare gwamnatinsa.

"Mun je wurin, mataimakiyata Farfesa Kaleptapwa Farauta da sauran mutane sun je inda abin ya faru saboda mun yi amanna da ɗaukar mataki," kamar yadda sanarwar da gwamnan ya fitar ta bayyana.

Ambaliyar ruwa ba sabon abu ba ne a Najeriya, musamman a jihohin da manyan rafukannan biyu - Kwara da Benue - suka ratsa ta cikinsu.

A duk shekara irin wannan ambaliya na haifar da asarar ɗimbin rayuka.

Hasashen ambaliyar ruwa na shekarar 2025, wanda hukumar kula da rafuka ta Najeriya ta fitar ya nuna cewa wurare 1,249 a ƙananan hukumomi 176 na jihohi 30 na Najeriya na cikin babbar barazanar fuskantar ambaliyar ruwa a wannan shekara ta 2025.

Haka nan kuma wurare 2,187 a ƙananan hukumomi 293 a jihohi 36 da babban birnin tarayyar ƙasar na fuskantar barazanar ambaliya.

Mummunar ambaliya a baya-bayan nan

Rescuers dey carry pipo comot from di flood

Asalin hoton, Governor Fintiri/Facebook

MAYU 2025 - Ambaliya ta baya-bayan nan da ta lakume rayukan mutane da dama ita ce wadda ta faru a ƙaramar hukumar Mokwa da ke jihar Neja a arewacin Najeriya.

Hukumomi sun ce sama da mutum 200 ne suka mutu yayin da fiye da 300 suka ɓata sanadiyyar ambaliyar ruwar wadda ta faru a ranar 29 ga watan Mayun 2025.

Ambaliyar ta tarwatsa fiye da mutum 3,000 baya ga gidaje masu yawa da ta lalata.

SATUMBA 2024 - A shekarar da ta gabata, jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar ta fuskanci ɗaya daga cikin ambaliyar ruwa mafi muni a cikin shekara 30 a Najeriya.

Ambaliyar ta Borno ta kashe sama da mutum 100 tare da tarwatsa sama da mutum miliyan ɗaya daga muhallansu, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Clothes scata round, mattresses dey soaked wit water and different crushed metal roofing sheets show wia some of di dozens of houses bin dey bifor, for Tiffin Maza Community for Mokwa town, Niger state.
Bayanan hoto, Hoton ambaliya da aka samu a Mokwa

Masana da dama da kuma hukumomi a Najeriya na ganin cewa sauyin yanayi da ke sahafar ɗaukacin duniya ne ke haifar da ambaliya a Najeriya.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja na daga cikin wadanda suka yi yaƙinin hakan, inda hukumar ta ce sare dazuka da sauyin yanayi ne ke haddasa ambaliyar.

A wata hira da kafar talabijin ta Channels, shugaban hukumar Ibrahim Hussaini ya ce duk da an yi hasashen cewa za a samu ambaliyar ruwa a Mokwa, amma ba a yi tsammanin zai shafi cikin garin Mokwa ba saboda ba ya kan hanyar ruwa.

"Ina so na shaida muku cewa sauyin yanayi ne, sauye-sauyen da ake gani a yanayi, da yadda mutane ke sare dazuka ba ji ba gani, yanzu ana samun ambaliya har a inda ba a taɓa samu ba a baya," in ji Hussaini.

"Shi ya sa ambaliyar da aka samu wannan karo, babu wanda ya yi tunanin za a same ta kumaba abu ne mai sauki ba a iya hasashen samun ta."

Abubuwan da ke haifar da ambaliya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani masani kan matakan kariya a sashen lura da muhalli na Jami'ar Bayero da ke Kano, Dakta Yusuf Idris ya shaida wa BBC cewa akwai abubuwa da dama da ke haddasa ambaliyar ruwa a Najeriya.

Manya daga cikinsu su ne:

  • Sauyin yanayi
  • Rashin kula da madatsun ruwa
  • Rashin magudanan ruwa
  • Rashin tsara hanyoyin zubar da shara

Dr Garba ya ce rashin nazari kan yanayin muhalli na daga cikin abin da ke haifar da cika da tumbatsar rafuka har ta kai ga samun ambaliya.

Ya bayyana cewa idan aka yi la'akari da mummunar ambaliyar da aka samu a jihar Borno a shekarar 2024 "ɗabi'ar rashin kula da bin shawarwarin wadanda suka gina madatsar ne sila."

Haka nan ya yi bayani kan yadda samun ruwa mai ƙarfi ba tare da tsammani sanadiyyar sauyin yanayi ke haifar da matsaloli.

"Sanadiyyar abubuwan da suke faruwa a muhalli, kamar sauyin yanayi, ba a iya hasashen yawan ruwan sama da za a samu sanadiyyar rashin tabbas na yanayi.

"Wani lokaci za ka ga ana samun ruwan sama mai yawa a lokaci ƙankani, wanda hakan ke iya haifar da ambaliyar ruwa, musamman a yankunan da babu magudanan ruwa."

Ta yaya za a shawo kan matsalar?

Dr Garba ya zayyana wasu abubuwa da ya ce idan gwamnati da kuma al'umma suka yi za su iya kawo sauƙi a matsalar ambaliyar ruwa.

"Ya kamata gwamnati nemi shawarar ƙwararru wadanda ke da masaniya kan lura da muhalli, wadanda za su riƙa kula da madatsun ruwa a faɗin ƙasar.

"Wani abin kuma shi ne ya zama wajibi mutane su daina zubar da shara barkatai, musamman daina zubawa a cikin magudanar ruwa, abin da ke datse hanyoyin ruwan kuma ya haifar da ambaliya," in ji Dr Garba.

Ya kuma kuma nuna buƙatar ganin al'umma sun daina gina gidaje a kan hanyar ruwa.