Sojan Amurka ya amsa laifi kan yunƙurin taimakawa 'ƙungiyar 'yan ta'adda'

US soldiers

Asalin hoton, Reuters

Wani sojan ƙasa na Amurka ya amsa laifin cewa ya yi yunƙurin taimakawa ƙungiyar IS wajen kai hari da hallaka wasu takwarorin aikinsa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ma'aikatar shari'a ta kuma ce sojan ya amsa laifi kan yunƙurin ba da tallafin kayan aiki ga ƙungiyar da aka ayyana a matsayin ta masu ta'addanci.

Cole Bridges, wanda aka fi sani da Cole Gonzales, ya miƙa bayanai ga wani jami'in leƙen asiri, a cewar ma'aikatar shari'ar.

Yana iya fuskantar ɗaurin sama da shekara 40 a gidan yari.

Mista Bridges ya shiga Rundunar Sojin Amurka a cikin watan Satumban 2019 inda aka tura shi sansanin sojoji na Fort Stewart da ke jihar Georgia.

Jim kaɗan kuma sai ya fara "bincike da karanta farfagandar intanet da ke kambama ayyukan masu iƙirarin jihadi da aƙidunsu na tashe-tashen hankula," a cewar wata sanarwar Ofishin Babban Lauyan Amurka

Sai dai Bridges ya fara musayar bayanai da wani ma'aikacin Hukumar Leƙen Asirin Amurka ta FBI a watan Oktoban 2020 wanda ya ɓad da kama a matsayin wani mai goyon bayan ƙungiyar IS da ke tuntuɓar mambobinta a Gabas ta Tsakiya.

Mista Bridges ya ba shi labarai game da takaicinsa a kan rundunar sojan Amurka kuma ya nuna sha'awarsa ta taimaka wa ƙungiyar IS - wadda kuma ake kira da ISIS - ga jami'in leƙen asirin na FBI.

Sanarwar ta ce daga nan sai ya fara bayar da "horo da jagoranci ga mayaƙan da ya ɗauka 'yan ISIS ne da ke shirin kai hare-hare, ciki har da ba su shawara a kan wuraren da za su iya kai wa hari a Birnin New York".

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An kuma ce ya aika wa jami'in leƙen asirin "wani ɓangare na kundin ba da horon rundunar sojojin Amurka da harkokin jagoranci a kan dabarun yaƙin sojoji".

Daga watan Disamban 2020 kuma, Mista Bridges ya fara bayar da umarni ga mayaƙan IS kan yadda za su kai wa sojojin Amurka hari a Gabas ta Tsakiya.

Ya ma aika masa wani zane na taƙamaiman dabarun yaƙin sojoji don ƙara yawan dakarun Amurka da za a hallaka.

Ya kuma samar da wani bidiyo da ya ɗauki kansa sanye da rigar sulke ta sojojin Amurka yana tsaye a gaban tutar ƙasar inda yake nuna alama da hannu ta nuna goyon baya ga ƙungiyar masu iƙirarin jihadi.

Mako ɗaya bayan nan ya sake aika wani bidiyo, inda ya yi amfani da manhajar jirkita murya, yana zayyana wani jawabin farfaganda don nuna goyon baya ga wani harin kwanton ɓauna da mayaƙan IS za su kai wa dakarun sojin Amurka.

"Kamar yadda ya amsa da bakinsa a kotu yau, Cole Bridges ya yi yunƙurin shirya wani mummunan harin kwanton ɓauna ga takwarorinsa sojoji da sunan yi wa ISIS aiki da miyagun aƙidojinta," cewar Damian Williams, Babban Lauyan Amurka na Lardin Kudancin New York.

"Halayyar Bridges ta cin amana, juya baya ne ga abokan aiki da ƙasarsa gaba ɗaya ne."

Sai ranar 2 ga watan Nuwamba, za a yanke masa hukunci.