FBI ta kama sojan da ke neman aikin ina-da-kisa a intanet

Parody internet site

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI, ta kama wani sojan sama na ko-ta-kwana bayan an zarge shi da neman zama ɗan ina-da-kisa a wani shafin intanet na barkwanci mai suna "Rent-a-Hitman".

Matashin Josiah Ernesto Garcia, ɗan shekara 21, ya ce yana buƙatar kuɗi ne don ɗaukar ɗawainiyar iyalinsa kamar yadda takardun kotu suka nuna.

Tun ainihi, an buɗe shafin ne don tallata wani kamfani mai harkar fasahohin tsaro na zamani a 2005.

Da ya durƙushe ne kuma, sai aka mayar da shi zuwa shafin barkwanci da zaɓin neman mutane su shiga don yin aiki a matsayin 'yan ina-da-kisa.

Hukumar binciken manyan laifuka ta yi zargin cewa a tsakiyar watan Fabrairu ne, Mista Garcia ya aika da takardun karatunsa - da ke nuna "gogewarsa a fagen aikin soja da ƙwarewarsa ta sarrafa bindiga".

Takardun karatun nasa sun kuma nuna cewa ana yi wa Mista Garcia laƙabi da "Reaper" wani suna da ake samu saboda bajinta da gogewa kan aikin soja da ƙwarewa wajen iya saiti da bindiga, in ji wata sanarwa daga FBI.

Tashar talbijin ta CBS News, mai ƙawancen aiki da BBC a Amurka, ta tabbatar cewa Josiah Garcia ya shiga aikin sojan tsaron sararin saman Amurka na ƙasa a watan Yulin 2021.

Da ya ji ba a waiwaye shi ba, bayan ya aika takardun neman aiki, an yi zargin Garcia ya sake bibiyar shafin na intanet ɗin, waɗanda suka yi masa kwatance zuwa wani ofishin hukumar FBI.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ba tare da ɓata lokaci ne ba kuma, sai wani jami'in hukumar FBI da ya ɓad-da-kama, ya fara tattaunawa da Garcia.

Hukumar ta yi iƙirarin cewa sojan ya yarda a ba shi aikin kashe wani mutum a kan kuɗi dala dubu biyar.

An kuma yi zargin Josiah Garcia ya faɗa wa FBI cewa ya "daɗe yana zuba ido don irin wannan dama" ta yadda zai samu "maƙudan kuɗin" da zai ɗauki ɗawainiyar ɗan da za a haifa masa.

Jami'in FBI da ya ɓad-da-kama ya gamu da mutumin a wani dandalin shaƙatawa inda ya ba wa soja bayanai kan sunan ƙarya na wanda yake so a kashe cikin bayanan har da hotuna da sauran bayanai da kuma kafin alƙalamin $2,500.

Bayan ya yarda da sharuɗɗan aikin ne, sai Josiah Garcia ya tambayi ko sai ya kawo shaidar hoton gawar mutumin, in ji wata sanarwa da ofishin babban lauyan gwamnatin Amurka na lardin Tennessee.

Daga nan sai jami'an tsaro suka kama Mista Garcia kuma suka gudaar da bincike a gidansa inda sua gano wata bindiga ƙirar AR.

Idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar ɗaurin sama da shekara goma a gidan yari.