'Ni ba mazambaci ba ne', in ji D'banj bayan ICPC ta sake shi

Asalin hoton, Getty Images
Shahararren mawaƙi ɗan Najeriya D'banj ya ce ba shi da wata "alaƙa da zamba" bayan lauyansa ya ce hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC ta sako shi daga tsarewar da ta yi masa.
An kama shi a farkon makon nan kan zargin zambar miliyoyin kuɗin da aka ware don tallafa wa matasan Najeriya ta cikin shirin N-Power.
"Na taimaka wa hukumar da dukkan abin da na sani," a cewar D'Banj cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram.
"Na tabbatar za su iya gano gaskiya," kamar yadda ya bayyana.
D'banj ya ƙara da cewa an sake shi ne saboda "ɗaukakarsa", abin da ke nufin ba sai ya cika ƙa'idojin beli ba kafin a sake shi.
A gefe guda kuma, wani jami'in ICPC ya faɗa wa BBC cewa ana ci gaba da bincike.
A ranar Laraba ne ICPC ta ce kuɗaɗen da suka ɓata sun kai biliyoyin naira, kuma babban sakatare a Ma'aikatar Jin-Ƙai Dr. Nasiru Gwarzo ya faɗa wa BBC Hausa cewa su ne suka yi wa ICPC ƙorafi.
Mawaƙin - wanda sunansa ne gaskiya shi ne Oladapo Daniel Oyebanjo - ya yi iƙirarin cewa shi jakada ne na shirin na N-Power da aka ƙirƙira don matasa marasa aikin yi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram
Sai dai kuma, Ma'aikatar Jin-Ƙai wadda ke kula da shirin ta ce babu wata alaƙar aiki tsakaninta da mawaƙin kuma iƙirarinsa ba gaskiya ba ne.
A shekarar 2016 Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da shirin N-Power. Sai dai da yawa daga cikin matasan da suka ci gajiyar shirin sun yi ƙorafin zama tsawon watanni ba tare da albashi ba.
Kazalika, an kama wasu mutum 10 da ake ci gaba da bincikar su tare da D'banj.
Kundin waƙar da D'banj ya saki a 2012 mai suna Oliver Twist ya jawo masa masoya a ciki da wajen Najeriya.
Shekara biyu da suka wuce ɗansa ya nitse a ruwan ninƙaya da ke cikin gidansa a Legas.
____________
Wane ne D'banj?
- Shekararsa 42, ɗan kasuwa kuma mai shiri a talabijin
- Ya lashe kambin African Act a bikin ba da kyautuka na MTV Europe Music Awards 2007
- Ya ci kyautar mawaƙi mafi shahara a Afirka na 2014 a bikin World Music Awards
- Waƙarsa ta Oliver Twist ta jawo masa ɗaukaka a Najeriya duniya baki ɗaya











