FBI ta kai samame gidan tsohon shugaban Amurka Donald Trump na Mar-a-Lago

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon shugaan Amurka Donald Trump ya sanar cewa jami'an hukumar FBI mai binciken manyan laifuka sun kai wani samame gidansa da ke Jihar Florida, kuma sun balla wani akwatin ajiyar kaya da kudade da ke cikin gidan nasa.
Daga baya wani dan tsohon shugaban, Eric Trump ya shaida wa tashar talabijin ta Fox News cewa binciken da aka gudanar a gidan mahaifin nasa da ke Mar-a-Lago na da alaka da wasu takardu da ofishin adana takardun tarihi na Amurka ke nema ne.
Har zuwa wannan lokacin, hukumar ta FBI da ma'aikatar Shari'a ta Amurka ba su ce uffan ba.
CIKIN WATA SANARWA, Donald Trump - wanda na Jihar New York yayin da aka kai samamen - ya ce an yi wa "gidana na Florida kofar rago" - saboda samamen da wasu jami'an FBI msu yawa suka kai.
Ya kuma ce ya dade yana ba jami'an gwamantin tarayya da wasu hukumominta hadin kai , kuma bai ga dalilin kai samamen ba cikin sirri kamar yadda aka yi.

Asalin hoton, Getty Images
'Babu dalilin raba takardun sirri da mazauninsu'
David Tafuri, wani tsohon jami'in ma'aikatar harkkin waje ta Amurka ne, kuma babban lauya, ya ce da alama Mista Trump ya kwashi wasu takardun sirri da ba mallakinsa ba ne yayin da ya bar Washington DC:
"Babu dalilin da zai sa a raba wasu takardun sirri daga mazauninsu, ko ma a ciro su daga cikin wani akwatin ajiyarsu na sirri. Tilas ne a bar irin wadannan takardun a wuraren da gwamnati ta tanadar. Shi yasa da zarar shugabn kasa ya sauka daga mukamin, daga wannan lokacin ba shi da damar daukar dukkan abubuwan da suka kasance na sirri ne."
Mista Trump ya ce an daukin wannan matakin ne domin a tozarta shi kuma domin a hana shi sake tsayawa takara a zaben 2024.
A nata bangaren Fadar White House ta ce ba a sanar da ita za a kai samamen ba sai bayan ya auku.










