Donald Trump: Yadda ƴan majalisar wakilai suka tsige shugaban Amurka 'kan tunzura mabiyansa' su hambare gwamnati

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Majalisar Wakilan Amurka ta tsige Shugaba Donald Trump saboda laifin "tunzura mutane su hambarar da gwamnati" da wasu mabiyansa suka yi a ginin majalisar kasar a makon jiya.

Shi ne shugaban kasar na farko a tarihin Amurka da aka taba tsige wa daga mukamin shugaban ƙasa har sau biyu - wanda kuma majalisar za ta yi wa shari'a a karo na biyu.

Mista Trump dan jam'iyyar Republican zai fuskanci wata shari'a a majalisar dattawan ƙasar, wanda idan ta same shi da laifi zai iya rasa damar sake neman ko wane mukami na tsawon rayuwarsa.

Yawancin 'yan majalisar wakilan sun bi sahun jam'iyyarsu ne wajen kada ƙuri'ar tsige shugaba, inda aka tsige shi da ƙuri'u 232, su kuma waɗanda su ka ki goyon bayan a tsige shi aka sami ƙuri'u 197.

Ranar 20 ga watan Janairun nan Mista Trump zai bar ofis bayan da ya sha kaye a hannun Joe Biden a zaben watan Nuwamba.

An dai shafe sa'o'i ana tafka muhawara kafin 'yan majalisar su ka ƙada kuri'ar tsige shugaban.

'Yan majalisa 10 daga jam'iyyar Republican mai mulkin kasar sun goyi bayan takwarorinsu na Democrat wajen kaɗa ƙuri'ar tsige Mista Trump.

Sai dai da wuya a dauki mataki kan Mista Trump gabanin saukarsa daga mulki nan da mako guda saboda Majalisar Dattawa na hutu kuma ba a sa ran za ta dawo domin duba batun.

A makon jiya 'yan majalisa daga jam'iyyar Republican su 139 su ka kaɗa kuri'ar amincewa da sakamakon zaben shugaban ƙasa na 2020 da kuma shan kayen da Mista Trump ya yi.

2px presentational grey line

Mene ne zai faru nan gaba?

Nancy Pelosi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nancy Pelosi ta bayyana Trump a matsayin shugaban da ba shi da kunya

Za a aike da takardar tsige shugaban kasar zuwa majalisar dattawa, wadda za ta gudanar da zama domin yanke hukunci kan ko shugaban yana da laifi. Ana bukatar kashi biyu cikin uku na 'yan majalisar dattawa su amince da batun kafin a hukunta Mr Trump, ma'ana dole akalla 'yan Republicans 17 su bi sahun dukkan 'yan Democrats a majalisar.

Ranar Talata jaridar New York Times ta rawaito cewa 'yan majalisar dattawa 20 na jam'iyyar Republicans sun amince su hukunta shugaban kasar.

Idan majalisar dattawa ta samu Mr Trump da laifi, mai yiwuwa 'yan majalisar su sake kada kuri'a da za ta hana shi sake tsayawa takara - duk da yake ya nuna alamar yin hakan a 2024.

Sai dai ba za a yi wannan hukunci a wa'adin da ya ragewa Mr Trump na mako daya a kan mulki ba.

Shugaban masu rinjaye na jam'iyyar Republican a majalisar dattawa Mitch McConnell ya fitar da wata sanara da ke cewa: "Idan aka yi la'akari da dokoki da tsare-tsare da kuma abubuwan da suka faru a majalisar dattawa a baya game da batun tsige shugaban kasa, babu wata dama da ta nuna cewa za a kammala yanke hukunci cikin adalci ko kuma bisa muhimmanci tkafin zababben shugaban kasa Bidenya sha rantsuwar kama aiki a mako gobe."

Ya kara da cewa babban abin da majalisun dokoki suka kamata su yi shi ne su mayar da hankali wurin ganin an mika mulki cikin kwanciyar hankali ga gwamnatin Mr Biden. inauguration.

Babu shugaban kasar Amurkan da aka taba cirewa daga mulki ta hanyar tsigewa. Majalisar wakilai ta tsige Mr Trump a 2019 bisa alakarsa da Ukraine, amma majalisar dattawa ta wanke shi. Haka ma abin yake ga tsofaffin shugabanni Bill Clinton a 1998 da Andrew Johnson a 1868.